SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Cikin wannan galabaitar ta kalleshi tana kuka tace “Ka kaini wajen Abhi na, bana so na mutu ban ganshi ba, je vous en prie.”
K’anwarshi dake bi wa Iffa mai sunan Bilkissu amma suna kiranta da Mamuh dan sunan mahaifiyar babansu ne hannu tasa ta gyara mata gashinta a cikin harshen french tace “Kwantar da hankalinki, zai kaiki kinji, kiyi hak’uri.”
Kallon mama yayi yace “Mama ku saka mata kaya zanje na taho da likita saiya dubata.”
“To.” Ta fad’a ta kalli Mamuh tace “D’auko mata rigarki ta saka.”
Mik’ewa tayi ita ma taje ta d’auko doguwar riga, mama ce ta karb’i rigar ta zura mata wuya, atshawar da tayi ta tilasta fitowar majina a hancinta, kafin ta goge tuni mama ta jawo hab’ar zaninta ta goge mata kamar yarinya k’arama. Da kallo ta bi mama, take taji k’aunar matar ta shiga ranta, k’azantar jikinta ta goge da kayan jikinta? Uwa ce kawai zata iya maka haka ko wani shak’ik’i, a gaskiya ta siye zuciyarya da wannan abun d’aya data mata, tana wannan tunanin mama ta kama hannayenta ta zura mata hannayen rigar, mik’ewa tayi tsaye tare da kamata ta tashi ita ma, zip d’in rigar ta zuge mata inda Salah dake tsaye ya bita da kallo, dama Mamuh siririya ce ita ma, rigar ta d’auki jikinta sai dai tsayin bai saukar mata ba saboda ta fita tsayi.
Har zai fita Farha ta shigo tace “Na gyara shinfid’ar.”
A kasalance yace “Ki bar maganar shinfid’ar nan, zanje tahowa da likita ne ya duba yarinyar nan.”
A wani yamutse ta kalli Sarah da mama da Mamuh ke ta wani shafarta suna gyara mata gashin kanta, a gaskiya har ranta taji bata sonta saboda dalillai dayawa, haka kawai zata takura mata ta kuma hanata rawar gaban hantsi da mijinta, ita har yanzu bata samu dalilin daya sa shi tahowa da ita ba. Ganinshi kawai tayi ya wuce zai fita ta bishi da kallo.
A tsiyace yasa guard corp d’inshi su bincike mishi kaf masaukin Salahadeen duk k’ank’antar shaida ko hujja da zata kaisu gareshi yana sonta, cikin akasi sunyi shigar dare gidan sai suka samu Richard, tsareshi sukayi suka kira Shakoor suka fad’a masa, nan yace su taho mishi dashi zasu samu bayanai a wurinshi, haka kuwa ta kasance bayan sun kawo shi, lambar Salahadeen kawai da yake aiki da ita acan suka samu a wayarshi, lambar suka d’auka suka korashi ya tafiyarshi.
Duk da ya sauka k’asar Niger ya kuma ganshi cikin garin maradi bai sa shi samun nutsuwa ba, saida yayi anfani da tablet d’inshi wajen bin dindigin layin Salahadeen, sauk’i kamar shan ruwa sai ga signal dashi ya musu jagora har zuwa k’ofar gidan.
Salahadeen na fitowa ya ci karo dasu suna kallon gida da kyau, Shakoor na shirin shiga ya fito hakan yasa shi tsayawa, kallon kallo aka shiga yi babu wanda yayi gaggawar magana, k’arasa fita yayi ya tunkaresu inda guard corp d’in sukayi kan Salahadeen, da sauri ya dakatar dasu ta hanyar d’aga musu hannu, tsayawa sukayi sai shi ya shiga tahowa rai a b’ace.
Yana zuwa ya shak’i wuyan rigarshi cikin d’aga murya yace “Me yasa Salahadeen? Me yasa zaka min haka? Ina ‘yata take?”
Ba alamar tsoro ko razani ya kalli tsakiyar idonshi yace “Tana ciki.”
Sakinshi yayi ya ture shi zai shiga ciki, tsayawa yayi ya juyo ya kalleshi yace “Me yasa ka tahoda ita?”
Juyowa yayi shima yace “Ka sa na sace ta dan ka cutar da ita?”
Dda mamaki a fuskarshi yace “Waya fad’a maka haka?”
Cikin rashin damuwa yace “Ni da kaina na sani.”
Wani murmushi yayi shi kuma ya shiga ciki, saida yayi tsaye tsakiyar gidan ya k’are mushi kallo tas kafin ya iya k’ak’aro sunan ‘yarsa yace “Sarah.”
Sarah da caraf ta cafke muryar mahaifinta da sauri ta mik’e tana sakin gyalen mama k’asa ta fita, tana tozali dashi ta daka a guje ta rumgumeshi, shi kanshi yayi farin cikin ganinta hakan yasa shi d’aukarta yana juyawa da ita, su mama ne suka fito suna kallon ikon Allah, tunda suke a rayuwa su kam inba a tv ba shi ma ba kullum ba.
Sauketa yayi kan k’afafunta yana kallon fuskarta, mamaki ya bayyana ganin fuskarta duk tayi ja musamman hancinta alamar mura, idonta duk sun kod’e kamar ba ita ba, hannaye yasa kan damatsenta da nufin jawota ya tambayeta, sai kuma yaji zafi rau a jikinta, cikin firgici ya kalleta yace “Princess me ya same ki? Baki da lafiya ne?”
Kallon Salahadeen tayi daya shigo yanzu tace “Eh Abhi.”
Juyawa yayi ya kalli inda ta kalla yana ganinshi ya k’ara shak’o rigarshi yana fad’in “Dubi yarinyata, dubi halin da take ciki, Salahadeen me yasa zaka min haka? Yarinyar nan bata tab’a shigowa k’asar nan ba, ko zaka shigo da ita yana da kasa a mata rigafin wannan cututtukan, haka kawai ka d’auko min ‘ya, to ka sani saina mik’a ka hannun jami’ai.”
Cikin jin haushi ya bige hannunshi daga rigarshi yana fad’in “Sai me? Ka mik’ani nima kuma zan fad’i wanda ya saka ni kidnapping d’inta, zan fad’i dalilina na tahowa da ita idan ya so duk a d’auremu tare.”
Kallon rashin fahimta ta musu ta rik’e hannun Shakoor tace “Abhi, what its going on?”
Kallonta yayi cikin rashin gaskiya yace “Nothing princess.”
Da k’arfi Salahadeen yace “Ka fad’a mata gaskiya, ni dama ko baka zo ba zan mayar maka da ‘yarka idan kana so ka dafata bai dame ni ba.”
Saida ya matso kusa da shi ya nuna fuskarshi da yatsa yace “Amma ka san wani abu d’aya, ‘yarka na matuk’ar sonka kuma kai kad’ai ta sani a rayuwarta, banda sunan Abhi bata san sunan kowa ba, cutar da ita cin amanarta ne da kuma yaudarar zuciyarta.”
Rik’e hannunshi yayi sosai ya jashi da k’arfi suka fitar k’ofar gidan, sororo suka barta tsaye da tunanin kalaman Salahadeen. Suna fita ya sake shi cikin d’aga murya yace “Me kake so Salahadeen? So kake ka shiga tsakanina da ‘yata?”
Girgiza kai yayi yace “A’a, amma da ace idan na fad’a mata wanda yasa a saceta zata yarda dani dana fad’a mata.”
Da mamaki ya sake kallonshi yace “Me yasa kake so ka kasheta?”
Da tsoro ya kalleshi yace “Ni d’in? Ba kasheta nake so nayi ba?”
Murmushi ya masa yace “Me yasa ka sani na saceta to?”
Cikin rashin gaskiya yace “Saboda ina so na kareta ne daga masu son kasheta.”
Murmushi ya sake yi yace “Amma dai kasan waye Salahadeen ko? Kuma kasan ba yaro bane ni.”
Da sauri yace “Salahadeen ka fahimce ni, bana da niyyar cutar da ita ko kad’an, yanzu ka fad’a min ka samu kud’in dana turo maka?”
Girgiza kai yayi yace “Na gansu, kud’in daka tura min ta account d’in da kai kad’ai ka san shi, sannan daga baya ka bi duk ka goge wata hujjar da zata nuna ka bani kud’i.”
Wani kallo ya masa wanda yasa Salahadeen yin murmushi yace “Duk na sani na kuma yi tunani akan lamarin, ka bani motarka ka umarceni na zo har compagninka na sace ‘yarka, ka ce na kaita wajen hutawarka na bakin ruwa wanda kayi register wurin da wani suna na daban, inda a k’arshe duk kai kawon police zai dawo kaina ne, inda zaka nuna musu ni amintaccenka ne da yasan shigeda ficen gidanka da kuma yarka, bayan ka kashe ‘yarka kuma saika fito da gawarta inda zan fito a makashinta tsundum, watak’ila ma zaka kirani da wanda yayi kidnapping d’inta ne kuma ya kasheta bayan ya samu kud’in.”
Matsowa yayi kusanshi sosai yana wani shak’iyin murmushi yace “Hakane? Haka shirin naka yake?”
Ganin sai rarraba ido yake da tsantsar mamaki da firgici yanda yasan shirinshi kamar a gabanshi ya tsara, tabbas hakane abinda ya shirya bayan an kasheta zai goga mishi matsalar, dan Salahadeen yasan sirri dayawa a game dashi, shiyasa yake so da ya zaja mishi matsalar da za’a kashe shi ko kuma a d’aureshi d’aurin rai da rai.