NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Mama ce ta matso ta kalleshi tace “Salahadeen kukan me takeyi wai? Me yasa ya mareta?”

Kallonta kawai yayi bai ce komai ba ya shiga jawo Sarah a bayanshi, yanda ta rik’e rigarshi sosai da yanda ya fizgota da k’arfi yasa botir d’in rigarshi guda ya cire, mik’a mishi hannunta yayi ya rik’e ya jata zasu wuce.

Duk da safiya ce har mutane sun d’an fara tsayawa wurin ganin mutane kala biyu ana ta wata show, zubewa tayi k’asa tana kuka sosai tana rik’e k’afarshi tana cewa “Abhi ka barni na tafi bana son tafiya, Abhi, Abhi ka barni zan zauna anan.”

Da k’arfi ya juyo rai b’ace ya kalleta yace “Ke mahaukaciyar ina ce? Ba zaki iya zama anan ba.”

Cikin shahsekar kuka tace “Abhi zan iya, zan iya na rantse maka.”

Cike da damuwa yace “Idan ma kin iya Sarah zaki wahala, sannan su ma ba zasu barki ki zauna musu a gari ba, kwanakin daya d’ebo muku k’alilan ne, dole za’a mayar dake k’asarki.”

Cikin muryar da tasha kuka ta sake cewa “Zan iya Abhi, ina so na zauna nan.”

D’aya hannun yasa yana gyara mata gashin kanta yana fad’in “Kamar yanda na fad’a miki ba zai yiwu ba, baki da dalilin zama a k’asar nan, ke ba aure ba kuma ba wani aiki ba, dole dai zamu koma tare.”

Kallon tsakiyar idonshi tayi da kyau, kamar an tsikareta sai kawai ta fizge hannunta da k’arfi saboda a lokacin ya sassauta rik’on daya yi mata, da gudu ta tashi ta zo gaban Salahadeen ta durk’usa gwiwarta d’aya, wani tamfatsetsen zoben diamond dake hannunta na dama ta ciro ta mik’a mishi tana fad’in “Will u marry me?”

Wani irin mamaki ne ya bayyana a fuskarshi ya kafeta da ido, Allah sarki marin daya mata ashe haka ya lalata mata fuska, idonta yayi jawur jini ya kwanta, ga shatin yatsun da suka fito rau da su kamar an zana, ga jinin dake barazanar lek’owa ta bakinta, saida ya lumshe ido tuna da yayi wannan Sarah ce fa yar k’wallisa. Shi kanshi Shakoor daya taho tsayawa yayi kallonta, su mama duk suna kallo suma suna fahimtar wani abun, a lokacin k’annan Salahadeen maza wanda daga masallaci suka wuce wajen gudu ne suka dawo, nan suka shiga kallon me ke faruwa suna tambayan yan uwansu.

Sarah data kafeshi da ido ita ma shima kuma yana kallonta yana tunanin yaren da zai fad’a mata dashi cewa ba zai iya ba, cikin sanyin muryar tausayi tace “Just for save my life, please marry me.”

Mama ce tayi saurin kallonshi tace “Wai ba zaka fad’a min meke faruwa ba?”

Jiki a matuk’ar sanyaye ya kalleta yace “Mama yana so ya koma da ita, ita kuma bata son tafiya dashi saboda taji shine ya kashe mahaifiyarta, shine take neman na aureta dan ta ci gaba da zama anan, dan na ceci rayuwarta.”

D’an dukanshi tayi a damtse tana fad’in “Shine sai ka tsaya dogon tunani, Salahadeen ka taimaketa daga sharrin bijimin can mana, lallai bashi da imani ko tausayi.”

Da mamaki ya kalleta yace “Kin amince mama?”

Ba alamar damuwa tare da ita tace “Na amince mana, ka sani dalilin haka ma ta musulunta.”

D’an juyawa yayi ya kalli Farha a hankali ya kalli mama yace “Mama Farhana fa?”

Dafa kafad’arshi tayi tace “Karka damu zan mata bayani da kaina.”

Juyowa yayi ya kalli Sarah, da sauri Shakoor ya taho ya zura hannu ta baya zai kamo gashinta shi kuma yayi saurin mik’ar da ita tsaye yace “Zan aureki, saboda na ceci rayuwarki kawai, bayan komai ya daidaita zaki koma k’asarki ta haihuwa, kin amince?”

Jinjina kai tayi tana murmushi, zai k’ara jawo hannunta mama tayi sauri hararanshi ta jawo Sarah tasa bakin gyalenta tana share mata fuska, juyawa tayi da ita zuwa cikin gidan tana fad’in “Uban banza uban wofi, yo me ake da uba irinka a duniya.”

Shakoor na kallonsu ya kasa katab’us dan yaga in yace zai takura shine zai kwana a ciki, sai dai kuma dalilin Sarah ba zai yarda a tsiyatashi ba k’arshe a kashe shi a wulak’ance ba. Saida suka kai k’ofar gidan ta juyo ta kalleshi tace “Ka manta ka tab’a haihuwar Saratu a duniya, ka d’auka baka tab’a haihuwar ‘yar daka bata sunan mahaifiyarka ba, na tsaneka Abhi bana son sake ganinka a rayuwata.”

Suna shigewa ciki ya kalli Salahadeen yace “Happy? Thank u.”

Saida ya matso daf dashi yace “Amma ka sani ba zan barta ba, Sarah ba zata sake kwana anan ba, ko da k’arfin tsafi saina mayar da ita gidana.”

Wani murmushi yayi yace “Karka d’auka waccen tantirin Salahadeen daka sani shine yanzu ma, wannan Salahadeen d’in mai bautar Allah da kuma kiyaye ibadarsa, ko a can ma ba yarwa nayi ba kai ne dai baka kula da haka ba.”

Juyawa yayi shima ya bi bayansu suka shige ciki, cikin jin haushi ya juya kamar zai tashi sama, masu tsaronshi ya bud’e mishi mota ya shiga, saida suka d’auki hanya sunyi nisa yace su tsaya, tsayawa sukayi yace su bashi wuri zaiyi waya, a k’arshe dai dole Kabeer ya kira dan samun shawarar da zaiyi anfani da ita.

Saida ya fad’a masa komai daya faru kafin Alhaji Kabeer yace “Shakoor ina hankalinka yake da har ka kasa tafiyar da al’amarin nan cikin sauk’i?”

Jin yayi shiru yasa yace “Har yanzu shirinka na kan daidai, Salahadeen zai zama makashinta ba shi kad’ai ba har da ma yan gidan nasu.”

Da sauri yace “Ban gane me kake nufi ba?”

Murmushi ya masa yace “Kayi gaggawar komawa gidan ka same su, ka basu hak’uri tare da nuna komai ya wuce, sannan karka yarda ka bar gidan saika d’aura mishi aure da ita.”

“What!? Ya fad’a da k’arfi tare da d’orawa da “Ba zai yiwu ba gaskiya, Sarah ta auri yaro na kuma mafi k’ask’anci ma a cikin yaran.”

Dariya yayi yace “Shakoor, to wa yasan data aure shi ma? Ko kwana ba zasuyi ma a matsayin ma’aurata zamu sa shugaba ya tsotse mana jininta, me kake ganin zai faru idan aka wayi gari babu Sarah? Karfa ka manta har yanzu case d’in b’atanta yana hannun yan sandan Tha茂lande, kuma kai kan ka suna zarginka lokacin da ka ce zaka zo ka tafi da ita.”

Jim yayi kafin daga bisani yace “Kayi gaskiya, amma ya zanyi na cire kaina?”

Wata dariya yayi yace “Wannan mai sauk’i ne, karka manta akwai blackmail sannan akwai tirsasawa, ka fara d’aura musu auren idan ka dawo nan mayi magana kan mataki na gaba.”

Murmushin jin dad’i yayi yace “Ok, merci.”

Da sauri yace su ja mota suka sake komawa inda suka baro.

Tunda suka shiga ciki ta zaunar da ita kan katifa ta sake rufeta saboda jikinta ya k’ara zafi, Salahadeen na shigowa ta kalleshi tace “Mr. ina so nasha coffee, kaina ya fara ciwo.”

Wani kallo ya mata yana tambayar kanshi ina zai same shi to, cikin tausar kanshi yace “Zaki sha lipton?”

Jim tayi tana kallonshi kafin tace “Bani guda biyu, banda sugar.”

Fita yayi daga d’akin rai a b’ace shi fa ba zai iya jarabar yarinyar nan ba, baida hak’urin lallab’a yaro ma bare mace k’atuwa, Zeid ne ya kalli mama yace “Wai mama da ita yah Salah ya taho ne?”

“Um.” Kawai ta fad’a tana d’an tausa mata kusan idonta daya kumbura, da mamaki yace “To me ya had’ashi da ita?”

Ba tare data kalleshi ba tace “Aurenta zaiyi.”

Da k’arfi dukansu suka ce “Aure?”

Al’ameen ne ya k’ara da “Aurenta mama? Zaiyi?”

Da kallo suka bi Farha data mik’e da sauri ta fita a d’akin, sai lokacin mama ta tuna ashe fa Farha na d’akin, kallon Mamuh tayi tace “Kula da ita, idan ya kawo ku bata tasha ina zuwa.”

Da sauri Mamuh ta matso kusanta hakan ne yasa Iffa zabga mata harara tana fad’in “To jarababbiya uwar naci, daga zuwanta sai wani lik’e mata kike kamar k’anwar uwarki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button