NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Murgud’a baki tayi tace “Eh d’in naji dai babu ruwanki dani.”

Tsaki tayi ta mik’e zata fita tana fad’in “Aikin banza, sai kace wata yar gwal sai wani nan da nan ake da ita, ni banga jarabar da tasa shi tahowa da ita ba ma wallahi, sai kace ‘yar aljanu.”

Zeid ne ya bita da kallo yana fad’in “Ki dai iya bakinki yarinya.”

Da kallo duka ta bisu kamar bata tab’a ganin hallitarsu ba. Ko da Iffa ta shiga ta samu Mama na rarrashin Farha, zaune tayi tana kallonta cikin jin haushi tace “Mama da gaskiyarta fa, ki bari ta koka ko taji dad’i a ranta, haba ta kwashe shekaru tana jiran mijinta sai kawai ya zo mata cikin dare da wata mai jan kunne ace wai zai aureta.”

Rai b’ace mama ta kalleta tace “Iffa, ni nake fad’a kina fad’a har kike d’aga min murya haka? To dake nake magana yanzu da kika saka min bakinki? To karna sake ji wallahi inba haka ba ranki zai b’ace.”

Kallon Farha tayi dake ta kuka ta ci gaba da cewa “Kamar yanda na fad’a miki karki d’auki al’amarin yarinyar nan kisa a ranki, ba aure ne na dindindin ba ko na soyayya, ita da kike gani mahaifinta mugu ne, so yake ya kasheta bayan shi ya kashe mahaifiyarta, ina jin ma d’an yankan kaine fa, shine yace zai koma da ita ta k’i yarda, kuma ba zata iya zama anan ba idan ba aure ne ya kawota ko wani aiki ba, to dan ya ceceta ne ya amince da aurenshi data nema, amma komai na daidaita zai rabu da ita ta koma garinta.”

Cikin kuka tace “Amma mama me yasa sai yah Salahadeen ne zai aureta? Ta auri wani mana.”

Cikin rarrashi tace “In banda abinki ba dalilinshi ne take garin nan ba, kawai ke dai ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru, ko d’aki d’aya fa bata da a cikin gidan nan, kuma ba shelanta auren za ayi ba, in tak’aice miki dai kamar ace auren viza.”

D’an sakin fuskarta tayi tace “Da gaske mama?”

Saida ta shafi kumatunta tace “Allah kuwa, ina wasa dake ne?”

Girgiza mata kai tayi hakan yasa mama mik’ewa tace “Yanzu ki tashi kiyi wanka ki cab’a ado dan mijinki, zan turo ya zo ya samu ya kwanta ya huta, ni zanji da bagwariyar yarinyar da bata gane yaren kowa sai nata.”

Fita tayi inda Iffa ta kalleta tace “Allah yarinyar bata min ba, haka kawai duk ta hargitsa mana gida daga zuwanta.”

Tab’e baki kawai Farha tayi ta fita dan yin wanka.

Ya kawo mata lipton d’in bata kai ga sha ba Shakoor ya shigo da sallama a bakinshi, ko da mama ta ga ya fita ta bi bayanshi dan mutumin tsoro yake bata, kallonsu yayi dukansu yace “Hak’uri na zo baka kan abinda ya faru, ka fini gaskiya Salahadeen, na gane kuskure ne kuma in Allah ya yarda ba zan kuma maimaita kamarsa ba.”

Hannu ya mik’a masa cikin harshen hausarshi daya fara barin bakinshi yake cewa “Mun zama surukai yanzu, zan bar k’asar nan da minti ashiri, sai dai bana so na tafi ba tare da nayi wakilci auren Sarah ba, dan Allah zan iya?”

Kallon juna sukayi shi da Mama da mamaki, sun d’an jima haka kafin mama ta kalleshi tace “Amma kasan ba auren dindindin bane zasuyi ko?”

Kallon Salahadeen yayi yace “Me yasa ba zaka aureta ba har abada?”

“Saboda ina da mata.” Ya fad’a kai tsaye, murmushi yayi yace “Shikenan ba komai, amma alfarmar da nake nema karka rabu da ita har sai ka samu mutumin kirkin da zaka had’ata dashi kamarka.”

Kallon da suka ma junansu yana da ma’anoni da dama, sai kawai mama ta katsesu da cewa “To dama ni bana so kowa yasan da maganar auren nan, dan zansha cacaka a wajen yan uwan mahaifinsu, amma tunda gashi ka dawo kawai ku zauna anan ka bashi aurenta ya karb’a shikenan a wuce wurin.”

Cikin jin dad’i ya kalli mama yace “Kinyi gaskiya Mama…”

Da sauri tace “A’a ni ba mamarka bace, ban ma isa haihuwarka ba.”

Juyawa tayi tana fad’in “Bari na kawo muku tabarma.”

Kallon juna suka dinga yi kamar su rufe juna da duka suke ji har mama ta shinfid’a tabarma suka zauna ita kuma tana tsaye kansu, hannu yasa aljihu yana fad’in “Zan biya sadakin da kaina.”

Dakatar dashi yayi da cewa “A’a ka barshi, ni zan biya daga abinda Allah ya hore min na halak, kuma mafi k’ank’atar sadaki domin wanzuwar alkairi.”

Wani kallo ya masa kawai inda ya fito da kud’i ya mik’a masa, saida ya k’idayasu yaga jaka arba’in cif sannan yace “Sarah Shakoor? Hummm.”

Mama na kallo ya bashi aurenta shi kuma ya karb’a kafin ya tashi sukayi sallama ko neman Sarah baiyi ba.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:02 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               1锔忊儯2锔忊儯

Mama na shirin tafiya makarantar da tana d’aya daga cikin malaman, Salahadeen ya shigo da sallama da kofin lipton d’in daya had’a ma Sarah dan baya so ta tashi ta nema, kasancewar sun gaisa da mama tun dawowarshi daga masallaci yasa ya kalli Sarah dake bacci yace “Wai bata tashi ba mama?”

Kyab’e baki tayi tace “Bata tashi ba.”

Aje lipton d’in yayi yana fad’in “Gashi to idan ta tashi, bana so ta hargitsa min lissafi akan neman cofee.”

Mik’ewa tayi tana gyara nik’ab d’inta tace “Nima dai tafiya zanyi yanzu, kasan yau asabar muna zuwa da wuri saboda sai mun fara karatu da malam, gashi kuma su Mamuh ma duk makarantar zasu tafi, daga ita dai sai Farha za’a bari a gidan.”

Yasan idan yace ya tasheta mama ba zata yarda ba, sai kawai yace “To mama, a dawo lafiya.”

Saida ta juya ta kalli Safar da har yanzu take rik’e da pillow gam kafin tace “Allah yasa.”

Har ta kai k’ofa zata fita kuma ta tsaya tace “Na manta ban fad’a maka ba, idan ta tashi dan Allah ga abun karinta nan ka bata ta ci.”

Da wani yanayi a fuskarshi yace “Ni kuma mama? Amma…”

Da sauri tace “Amma me? Inba kai ba wa zance to Salahadeen? Wai me yasa kake hakane? Matarka ce fa kuma wanda ya rabota da garinsu, kishiyarta kake so na ce ta zo ta mata hidimar?”

Cikin nutsuwa yace “Mama ba kishiyarta bace, ki ma daina had’asu ita matata ce ta har abada ita kuma ta wucen gadi ce.”

Kallon yaro yaro ne ta mishi tace “To naji, yanzu dai amana na baka kuma idan ka ci amana zata ci ka kaima.”

Kallon mama yayi da mamaki yace “Mama akan wannan d’in?”

Kallon mamaki ta masa tace “Ba wannan bace, hakk’inta zai iya jefa mu wuta dani da kai idan bamuyi da gaske ba, ka kula wallahi babu ruwa na.”

Sororo ya bi mama da kallo har ta fice, mayar da kallonshi yayi kan Sarah, saida yaji mama ta fita gaba d’aya ya taso ya durk’usa gabanta, hannunta ya shiga daddab’awa yana fad’in “Tashi ke gari ya waye tun tuni, ba kya sani wata wahalar ba wallahi, so take sai ya huce idan nace tasha ta min kuka kuma.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button