NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Da k’yar ya iya nasarar kallon fuskarta yace “Ke baki san da mutum bane?”

Cikin shagwab’a kamar za tayi kuka tace “Taya zan sani bayan baka fad’a min kana nan ba.”

Saida ya dire idonshi kan nonuwanta ya sake cewa “Amma ai ko k’amshin turare kinji ko?”

Turo baki tayi tana mishi wani mayen kallo daya shiga rugurguza mishi sassan jikinshi tace “Taya zan ji k’amshin turarenka bayan dama ban tab’a jin k’amshi ba.”

Cikin son rufe ido kamar wanda yasha wani abu yace “Kamar ya kenan Saaaraahhh?”

Kafe shi tayi da ido dan ita kanta gabanta ne ya fad’i kallon daya mata da kuma yanda ya kira sunanta, ganin ba tace komai ba yasa shi d’ago hanunshi dake rawa rawa ya jawo zanin rufar dake kan katifar ya d’orashi daidai k’irjinta yana fad’in “Ki…dinga kama…jikinki, baki san me zai…iya far..uwa dake ba.”

Da mamaki ta kalleshi tace “Kamar me fa?”

Saida ya sunkuyar da kanshi k’asa ya d’ago d’aya hannunshi yana ta rawa ya kaishi kan goshi ya shiga murzawa, ganin haka yasa ta kai hannunta da sauri ta tab’a goshinshi tana fad’in “Kana lafiya?”

Da sauri ta waro ido tace “Mr. zazzab’i kake?”

Kafin yace wani abu ta cire zanin daya rufa mata ta rufa mishi tana fad’in “Kwanta kafin mama ta dawo ta baka magani.”

Mik’ewa tayi tsaye da niyyar saka kaya, bata ankara ba bata tab’a tsammanin abinda zai faru ba kenan, kawai taji Salahadeen ya finciko hannunta da iya k’arfin daya rage masa a lokacin, laushi da sangarta yasa ta fad’awa kan jikinshi ragwaf da k’arfi.

A tare suka saki wata k’ara wanda dukansu na faruwar abu ne a bazata, kafin ta fahimci shine silar fad’uwarta yasa duka hannayenshi ya rik’o bayanta ya matseta da jikinshi.

Bud’a ido tayi ta sauke akan kyakyawar fuskarshi da bata d’auke da gashi, ganin idonshi a rufe suke sai k’ara matseta yake yasa ta daddab’ashi tace “Mr., me yake damunka ne?”

Ba tare daya bud’a ido ba cikin harhad’a kalmomi yace “Bbbabbban ssani ba…n..ima.”

K’ara matseta yayi hakan yasa tasa hannu ta fara ture shi tana fad’in “Mr. zaka ji min ciwo fa, ka barni na saka kayana.”

Ido rufe kamar mai bacci ya shiga shinshinar gashinta daya zubo kan fuskarshi acan kuma yana k’ara tausa k’ugunta da nashi yana gogawa, cikin wata irin murya yace “Sarah ke budurwa ce?”

Da mamaki ta kalli fuskarshi ta tsaya da son ture shi da take, me yake nufi da tambayarshi? Yana so ya sani ko ta tab’a iskanci kenan? Cikin jin haushi ta sake saka k’arfi zata ture shi tana fad’in “A’a, taya kake tunanin zan cuci rayuwata na k’i jin dad’i nima?”

A take ya bud’a ido ya zubasu kan fuskarta, shi kanshi baisan yanayin kallon daya mata ba? Sai dai kawai yasan bai ji dad’i ba da abinda ta fad’a, sai dai kuma abune da dama bai kamata ace yaji mamakinsa ba. A gurinta ita kam kallon tsana da jin haushi ne ya mata wanda bata san me hakan ke nufi ba.

Jin ya sassauta mata rik’on yasa tayi tunanin zai sake ta ne, amma sai taji ya birkita gaba d’ayanshi ya haye ruwan cikinta yana kallon k’wayar idonta. Da k’yar ta tattara wasu yawu ta had’e tana ci gaba da kallon fuskarshi.

Tafin hannunshi yasa ya shafo tun daga kan cikinta yana yin sama da hannun har yayi nasarar kaishi kan nononta, wanda da yake kallon idonta sai taga yayi ruf dasu ya lumshe, ba lumshewar kad’ai ba har da sakin wata marainiyar k’ara k’ara mai kama da kuka kuka…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:02 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               1锔忊儯1锔忊儯

Bayan sallah isha’i ya shigo d’auke da manyan ledoji har uku, a yanda mama ta koya mata yasa Farha tashi da sauri tana mishi sannu da zuwa, hannu tasa ta karb’i ledojin saiya sakar mata d’aya yana fad’in “Ba zaki iya duka ba, da nauyi sosai.”

Murmushi tayi ta bashi hanya ya wuce gaba har saida ta ga ya zauna kan tabarmar da mama take ita da Sarah tana ta datse mata akaifunta, ita dai ta buga tagumi tana kallonta kawai, cikin girmamawa yace “Mama sannu da gida.”

Ba tare data kalleshi ba ta amsa da “Sannu Salahadeen, har an dawo?”

“Na dawo mama.” Ya fad’a yana cire takalminshi k’afa ciki ya tank’washe k’afafu, kallon Sarah tayi cikin kwatanta mata tace “Ki gaishe shi.”

Jinjina kai tayi ta kalleshi tace “Bonsoir mr..”

Da kai kawai ya amsa mata, ledar ta aje gabanta ta juya cikin jin kunya ta shiga d’aki, jug ta d’auko da ruwa a ciki da bol d’inta ta kawo mishi, kallonta yayi yace “Nagode.”

Komawa tayi ta zauna sai mama data kalli Mamuh tace “Auta ki kawo mana tuwona ni da Saratu.”

Kallon mama yayi yace “Saratu kuma mama?”

Sai lokacin ta kalleshi tace “Saratu mana, baka ji ta fad’a ba d’azu sanda mugun ubanta ya zo.”

Satar kallonta yayi ya ga ta kuwa zubawa mama ido tana kallo, a hankali ya d’auke idonshi ya jawo ledojin gabanshi, ledar da tafi girma ya aje gaban mama yana fad’in “Mama wannan tsarabarku ce da ban samu lokaci na muku acan ba.”

Ledoji biyun ya aje gaban Sarah a harshen turanci yace “Wannan kayan da kika buk’ata ne, ba lallai su miki ba amma ki sani ba kowa bane mai kud’i irin mahaifinki.”

Turo baki tayi a harshen french tace “Amma ba ka ce zamu tafi tare ba.”

Saida ya d’auke idonshi daga kanta yace “Eh fasawa nayi.”

D’aukar ledar mama tayi da farin ciki tana fad’in “Ah Salahadeen ai da saika barshi ma, angode Allah ya saka da alkairi.”

Ciro kayan ciki ta dinga yi takalma ne da k’ananun poshet na hannu, duk wanda ta gani kuwa tasan da wacce ta dace, haka ta d’auki na ta ta mik’awa Iffa Farha da Mamuh, duka godiya suka mishi sai dai Farha ranta idan yayi dubu ya b’ace.

Akan me ya had’a tsarabarta data yan uwanshi? Me yasa zai ware ma Sarah ta ta kuma ya mata magana a harshen da basu fahimta? Me yasa zai bata wannan yar jakar da sunan tsarabar daya kawo mata ta tafiyar shekara uku?

Sarah data zazzage ta ta ledar duka kan tabarma ta shiga duba kayan, dogayen riguna ne har k’asa sai riga da wando suma, takalma sai kuma waya Samsung Galaxy J6, kallonshi tayi cikin wata tattausar murya tace “Mr. baka siyo min pant ko d’aya ba da bras, kuma wannan takalmin ma size d’inshi ya min yawa, sannan ina buk’atar pad saboda nan da kwana biyu zan fara p茅riod, kuma wannan wayar ma ni fa tawa dana baro acan Samsung Galaxy S20.”

Ya d’auka a ranshi yace “Tashin hankali.” Ashe a fili ne, kallonshi mama tayi tace “Meya faru na tashin hankali?”

Kallon mama yayi bai ce komai ba ya kalli Sarah yace “Wannan sise d’in ne ya miki yawa, 39 ne fa?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button