NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Cikin yatsina fuska tace “Eh mer., ni 38 nake sawa.”

A hankali ya kalli k’afar dake mik’e, a ido k’afar saika rantse zata ci lamba 40, amma kuma tace 39 sun mata yawa, wato munafukar k’afa gareta? Ganin yana kallon k’afar ta ta yasa tayi saurin saka takalmi d’aya tana mik’ewa tsaye da fad’in “Dubi ka gani to? Ka gani?”

Kallon k’afar ko ya shiga yi sai yaga yawan fa ba wani bane, sai dai daga sama ya d’an saketa hakan zaisa ba zata ji dad’in sakawa ba, saida ya d’an harareta ta wutsiyar ido yace “Cire kawo.”

Saida ta d’ora k’afar kan cinyarshi ta zage takalman ta barshi akan k’afarshi, baki bud’e ya kalleta suma duk haka, inda Farha kuma haushi ya gama kasheta ta tashi a hankali kamar za tayi wani abu ta shiga d’aki.

Kallonshi mama tayi tace “Ya zaka siyo mata wannan kayan da ba’a walalawa cikinsu? Ka mayar dasu suma ka siyo mata atamfa.”

Ido ya zaro yace “Mama atamfa? Wannan d’in zata saka atamfa?”

Kallon Sarah tayi da a lokacin ta d’auki wando tana duba lambarshi, kallonshi tayi nan ma tace “Mr. wannan wandon…”

Bai bari ta k’arasa ba yace “Ke idan ba zaki saka ba ki kawo, kina ji ma mama tace a siyo miki atamfa.”

Zaune tayi dab’as tana fad’in “Zan saka.”

Kallonshi tayi tace “To maganar bras da pant d’in fa?”

Banza ya mata kamar baisan tana yi ba, ganin ya shareta yasa ta kalli mama tace “Mamie ki fad’a masa ya siyo min, dubi fa idan ban saka ba basa yin girma.”

Duka tafukan hannayenta tasa ta dafe nonuwanta tana nuna wa mama girmansu, da sauri ya juyar da kansa mama kuma tayi saurin janye hannayenta tana satar kallon Salahadeen d’in, cikin murmushi tace “Zan fad’a mishi ya siyo miki to, amma banda abinki ma ai gabanki baya buk’atar ciko, kina da su daidai gwargwado kuma a kan k’afafunsu suke, miye na tushe tushen to?”

A hankali ya sulale ya mik’e ya nufi d’akinsu, wani dogon tsaki Iffa taja tana kallonta ta nuna ta da yatsa tace “Wai ke baki da kunya? Me yasa kike abu kamar wata mai tab’in k’wak’walwa? Komai ba tsari babu nutsuwa.”

Wani tsakin ta kuma ja ta mik’e ita ma ta shige d’akinsu, da kallo ta bi Iffa tana mamakin halin yarinyar da bata da fara’a, daddab’a mama tayi tana fad’in ‘Matso mu ci tuwo kinji, rabu da waccen haka take da bak’in hali.”

Har zata saka hannu mama tayi sauri rik’e hannun ta nuna mata buta tace “Wanke hannu kisa sabulu, yanzu aka yanke miki akaifa.”

Da sauri taje ta wanko ta dawo ta zauna, duk in tasa hannu zata d’ebo tuwan shinkafar saita sa mishi k’arfi, sai dai kuma tuwon ya mata dad’i sosai daya sha miyar kuka mama ta zuba musu d’an yaji a ciki da daskararren mai na suya (kitse). A haka mama ta dinga gatso mata tana aje mata gabanta tana d’auka tana kaiwa baki hankali kwance.

Yana shiga d’aki zaune ya ganta kan kujera sai had’e rai take, kamo hannunta yayi tayi tsaye yana kallonta yace “Ya dai? Miye na hushin?”

Cikin kumburo baki tace “Gaskiya yarinyar nan bata da kunya, ni kawai bana so tana shiga harkarka.”

Girgiza kai yayi yace “Da alama zaki saka matsalar yarinyar nan a ranki, ni kuma ba haka nake so ba saboda banga abun damuwa a ciki ba.”

Sakinta yayi yasa hannu aljihu ya fito da wani d’an k’aramin boite na yan kunnai ya bud’e ya mik’a mata, kallo tayi tare da kallonshi tana murmushi tace “Yaya Salahadeen nawa ne wannan?”

Ido ya lumshe mata alamar eh, cikin jin dad’i ta d’an rumgumeshi take kuma ta raba jikinsu tana fad’in “Nagode Allah ya saka da alkairi.”

Fitowa yayi daga d’akin ya zo ya d’auki takalmin dan canzo mata, kallonshi tayi tace “Mr. ka taho min da Bugger.”

Wani kallon jin haushi ya mata, duk da ta fahimci kallon amma saita basar tace “Ko na zo mu tafi tare?”

Kasa d’auke idonshi yayi daga kanta, turo baki tayi gaba tace “Please, ina so naga garin ne.”

K’wafa yayi ya juya ya fice, tab’e baki tayi ta kalli mama tace “Me yasa yake jin haushi na? Na masa laifi ne? Naga dai shi ya taho dani nan ba tare dana nema ba.”

Da yake mama taji farkon me tace sai tace mata “Ba haushinki yake ji ba, kinsan shi baya son yawan surutu ne kawai, baki ga d’aya matar tashi ba ita ma bata mishi magana sosai ba?”

Da mamaki ta kalli mama tace “Mamie ita matarshi ce, ni ma kuma mijina ne, to ya zaiyi damu kenan dukanmu? Ko dan ni auren bogi ne?”

Dariya mama tayi tace “To baki ga wasu ba ma matansu hud’u kuma duka sun san yanda sukeyi dasu ba.”

Saida ta nuna da duka yatsunta tace “Hud’u mamie? A gida d’aya kuma? Ya suke zaune to? Dama haka ake auren anan?”

Ita ma da mamaki ta kalleta tace “Ku a garinku mace d’aya ake aure?”

Jinjina mata kai tayi tace “Mamie idan har kinga mai mata biyu to sai dai yaudarar d’aya yayi amma dukansu basu san da juna ba.”

K’ura mata ido tayi tace “Shikenan mutum yayi ta zama da mace d’aya kenan uwa rai?”

Murmushi tayi tace “Eh mamie, amma fa mazan suna cin amanar matansu, wani yana da ‘yan mata a waje sunfi goma.”

Tintserewa sukayi da dariya inda mama ke fad’in “Dole mana, to kinga d’aya daga cikin dalilin da yasa ubangiji ya hallatawa maza auren mata hud’u kenan.”

Jinjina kai tayi tace “To amma mamie idan ya auri mace hud’u shikenan babu rabuwa kuma?”

Girgiza mata kai tayi tace “A’a ana rabuwa mana, idan d’aya daga cikinsu zaman babu dad’i da ita akan sallameta dan a samu nutsuwa.”

Da alamar tambaya a fuskarta tace “Kuma matan suna amincewa cikin sauk’i kafin su sa hannu a takardar sakin?”

Da mamaki tace “Takardar sakin? Wane sa hannu kuma?”

Da mamaki ita ma tace “Mamie bakuyi ne?”

Girgiza kai tayi tana fad’in “A’a bama yi.”

Hamma da tayi ta sanya mama mik’ewa tana fad’in “Bari na gyara miki shinfid’a ki kwanta.”

Kallonta tayi tace “Mamie babu tv ne? Ina so naga sabbin news.”

Sunkuyawa tayi ta rik’e hannunta tace “Babu anan gidan, amma a sabon gidan da Salahadeen ke gina mana yace duk ya saka mana.”

Da d’an mamaki tace “Gida?”

Da murmushi tace “Eh, ai tun yana can yake aiko da kud’i wani abokinshi ne ya tsaya kan aikin, yanzu haka an kusa kammala ginin ma.”

Cikin sanyin jiki tace “Kafin lokacin zan koma garina nima.”

Cikin tsokana mama tace “Me yasa ba zaki zauna tare damu ba? Ke ma fa gidan mijinki ne?”

Girgiza kai tayi tace “A’a Mamie, zan koma k’asarmu nima.”

Sakin hannunta tayi tana fad’in “Kina jin hausa kad’an kad’an mahaifinki ma naji yana hausa, shin asalinku dama yan nan k’asar ne?”

Saida tayi kamar zata yi kuka tace “Abhi ne ya fad’a min shi d’an Agadez ne, kuma yana da k’ani ma a garin Maradi, amma bai tab’a kawo ni ko ya nuna min ko da hotonsu ba.”

Fashewa tayi da kuka hakan yasa mama ma idonta suka cika da hawaye, share mata ta shiga yi tana fad’in “Daina kuka to kinji, insha Allahu wata rana zaki had’u dasu, kuma tunda yanzu kina garin Maradi ai zansa Salahadeen ya dinga bincika miki k’anin mahaifin naki.”

Da sauri ta kalli mama tace “Mamie nan ne maradi? Zan so na had’u dasu Mamie.”

Lallab’ata tayi tace “Karki damu insha Allah zaki had’u da yan uwan mahaifinki kema.”

A haka mama ta shiga d’aki ta gyara mata shinfid’a ta juya mata kan panka, Iffa ce tace “Mama mu a zafin zamu kwanta?”

Banza tayi da ita saida ta sake cewa “Tsakani da Allah mama akwai zafi a d’akin nan ba zamu iya bacci ba.”

Juyowa tayi tace “Saiki fita waje ki kwanta, kiyi tunani kanta mana ita da k’asarsu har k’ank’ara ke sauka, sannan a gidansu ac d’akinta ac motarta ma ac, ya kike tunanin zatayi bacci cikin salama a d’akin nan.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button