SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Turo baki tayi ta shiga gunguni mama dai bata sake kula ta ba, saida ta gama ta fito tace ta shiga ta kwanta, shiga tayi ta kwanta mama kuma ta tsaya hira dasu Zeid da suka shigo yanzu.
Sanda mama ta shigo har bacci ya fara d’aukarta saboda iskan panka dake kad’a mata, kwantawa mama tayi a bayanta saboda tana tashin dare, hannunta tayi pillow dashi dan Sarah ta d’auke pillown ta rumgume, a yanda ta saba a gida akan tamkad’ed’en gadonta mai matasai biyar baya ga irin k’anana na kwalliya.
A hankali bacci ya d’auki kowa, sanda Salahadeen ya shigo ya lek’o d’akin kowa yayi bacci, amma ita sai juyi take tana d’an tsaki kuma idonta a rufe alamar bacci take yi, saidai ya lura mama bata ji dad’in kwanciyar ba babu pillow, a hankali ya shiga takawa har yaje ya durk’usa gabanta, ledar hannunshi ya aje kusan kanta sannan yasa hannu biyu ya zare pillow daga k’irjinta data matse.
Kamar jaririn dake shan nono aka cire mishi bai gama sha ba, sai kuwa Sarah ta fashe da kuka ta tashi zaune tana kallonshi, murya k’asa k’asa ya shiga cewa “Ke ke shiru dan Allah, yi shiru pillow ne na karb’a.”
Da sauri mama ta mik’e zaune tana fad’in “Lafiya Sarah? Kai me ka mata tana bacci?”
Hannaye ya d’aga kamar wanda aka nuna da bakin bindiga yace “Babu abinda na mata mama, pillow ne na d’auka zan d’ora miki fa shine take wannan kukan.”
Saida ta gyara zama ta jawo Sarah ta d’ora kanta a k’irjinta tana shafa dogon gashinta tana fad’in “To ina ruwanka, nace maka ina so?”
Kallon Sarah yayi data yi shiru sai ajiyar zuciya take saukewa, kasa tashi yayi daga durk’ushen yana kallon yanda mama ke ta shafar kanta tana gyangyad’i ita ma daga zaunen, a hankali yaga ta gyara kwanciya tare da Sarah a k’irjinta, haka suka kwanta Sarah na k’irjin mama, mik’ewa yayi yana fad’in “Mama wankan jego ya rage miki tunda kinyi sabuwar jinjira.”
Tunda ya koma yake ji kamar ya kashe kanshi na juya masa baya da Sarah tayi, barasa ya dinga tittik’a yana sambatu yana fad’in duk abinda ya zo bakinshi, daga nan bacci ya d’aukeshi bai sake sanin me ke faruwa ba saida yaji kiran sunanshi a k’ungiya cikin wata murya mai ban tsoro.
Ko da ya bud’a ido a gaggauce ya samu kanshi a wuri yana rarraba ido, shugaban ne yace “Ya alk’awarinmu da kai Shakoor?”
Wani mammatsa idon daya fara yi ne yasa Kabeer kallon shugaban yace “Shugaba a gafarce ni, Sarah bata tare dashi, an ci amanarshi ne shima, amma za’a iya zuk’e jininta daga inda take, ya amince ya bayar da ita.”
Kamar ranar yanzu ma a allon bangon ya nuna musu ita, bacci take da pillow rugume k’am a k’irjinta, wata k’warya ya d’auka da babu komai a ciki ya rik’e a hannun hagu, d’aya hannun kuma ya bud’e duka yatsunshi yana nuna Sarah dake bacci, da sauri Shakoor ya d’an mik’e yana fad’in “Shugaba a mata hak’uri, na maka alk’awarin zan kawota da kaina, dan Allah karka tab’a min ‘ya.”
Ko kallonshi baiyi ba bare yasa ran zai saurare shi, rufe ido yayi dan baya son ganin Sarah a wani halin. Abun mamaki duk k’ok’arin shigaba na son jawo jininta ko kusa da ita ma shed’anun sun kasa zuwa bare suyi tasiri a jikinta, k’ara waro idonshi yayi yana k’ara bud’e hannunshi amma abun ya ci tura, juyowa yayi ya kalli Shakoor dake jin kamar ya fashe da kuka yace “Shakoor tseratar da ‘yarka kayi shine kake son raina mana hankali?”
Da sauri ya bud’a ido yana kallonshi yace “Kamar ‘ya?”
Juyowa yayi da kyau yana fuskantarshi yace “Me yasa ko kusa da ita shed’anun mu basa zuwa bare su kawo mana jininta?”
Cikin girgiza yace “Ban sani ba nima, amma bana tunanin abinda ka fad’a zai yiwu, tunda na haifi Sarah ban tab’a ganin ta d’ora goshinta a k’asa da sunan sallah ba, da sai nace ko daga nan ta samu kariyar.”
Cikin rashin tabbas yace “Sai dai kuma ko in…amma kuma Salahadeen, anya kuwa.”
Kallon shugaban yayi yace “A duba mana gidan da kyau, duk yanda akayi akwai wani abu.”
Da hannu ya d’anyi wata alama sai ga gaba d’aya d’akin ya bayyana, Mama ce zaune kan sallaya da Alqur’ani a hannu tana karatu, sai nesa da ita Iffa a tsaye tana sallah ita ma, sai Mamuh wacce ke cikin haila amma mama bata barta haka ba ita ma tana zaune tana tilawar karatu, wani wurin idan ta cije mama ke tashinta ta ci gaba da.
Wata jijjiga suka ga shugaban yayi tare da yin baya da k’arfi kamar zai fad’i, da sauri hoton ya b’ace hakan yasa ya juyo yana kallonsu a tsorace, cikin firgici da al’ajabi yace “Tunda muke haka bata tab’a faruwa ba, me ke shirin faruwa ne haka? Taya za ace jinin wani bil’adama ya gagari ikonmu? Ina! Ba zai yiwu ba.”
Da k’arfi ya kalli Shakoor ya nuna shi da hannu yace “K’arya kake Shakoor, duk siddabarunka munfi k’arfinka, ba zaka tab’a shan jinin yan uwan wasu kuma kai na ka ya gagaremu sha ba, dan haka duk k’ullin daka ma ‘yarka zamu warware shi kuma musha jininta, ka fahimta?”
Wani iska kawai ya furza dan shi kanshi al’amarin ya bashi tsoro, sai dai a matsayinsa na musulmi yasan dama babu abinda yafi k’arfin ubangiji, sallah da kuma karatun littafi mai tsarki kariya ne daga sharrin shed’anun mutane ma bare kuma aljanu.
Muryar shugaban ya tsinta yana fad’in “Daga yau kuma daga yanzu al’amarin ‘yarka Sarah ya dawo hannuna, da kaina zanyi aiki a kanta har sai hak’armu ta cimma ruwa.”
Cikin muryar dake isar masa da gargad’i ya sake nuna shi yace “Ka shirya tarwatsewar rayuwarka idan har jinin ‘yarka ya gagare mu.”
Ko da ya fad’a pat ya b’ace haka suma duk suka b’ace dan babu wata tattaunawa indai har ya bar wurin. Shakoor ma ko da ya samu kanshi a gida wani farin ciki ya ji wanda yake bawa kanshi tabbacin Sarah zata tsira daga gagarumin sharrinshi da kuma son zuciyarshi, ya fara ji a jikinshi zata gagari gaba d’aya k’ungiyar, duk da bai shirya ma talauci ba sai dai yasan zai riskeshi ba da jimawa ba, dan inhar basu samu Sarah ba shi zasu tagayyara a k’arshe su kashe shi.
Bai b’ata lokaci ba wajen tarkato duk wasu takardu da wata dukiya wacce yasan asalinta wacce ya mallaka ce a wajen mahaifiyar Sarah da kuma wacce Sarah ta gada a wurinta amma duk ya rik’e yana juyawa, saida ya kammalasu wuri d’aya ya shirya komai yanda zai risketa cikin sauk’i kafin ya d’auki biro da takarda yayi gajeran rubutu, had’ata yayi da sauran takardun kadarorin yasa a babbar farar enveloppe ya aje kan tuberin yana kallo yana busa sigari.
A daren Salahadeen ya cika cikakken miji mai iyali ta hanyar mayar da Farha cikakkiyar matar aure, dare ne daya shiga cikin tarihinsu dan dukansu sabbin shiga ne a fannin wannan rayuwar, sun dunk’ule sun zama d’aya inda kowa da sabon al’amarin daya ji a cikin zuciyarshi ruhi dama gangar jiki.
Washe gari…
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:03 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA GA
_DUK_
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
Talla
*Talla*
*Talla*
Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).