NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

BELC Babbar universit茅 ce dake cikin garin Tha茂lande anan motar ta shiga ta lula, inda mota bata shiga kad’ai aka tsaya, bud’e mata yayi ta fita sannan ta nufi ciki, ta d’anyi tafiya kafin ta isa class d’insu ba tare data kula kowa ba, yan mata ne su biyu suna ganinta suka washe baki da murna, tsaye suka mik’e dukansu suka d’an rumgume juna kafin su zauna, d’ayan ce ta d’an d’ago daga kujerarta a harshen turanci tace “Ya yau d’in? Zaki zo partyn makaranta?”

Ba tare data kalleta ba tace “Yes.”

Shigowar malamin ajin yasa kowa yayi shiru dan gabatar da abinda ya kawo su.

Bayan sun kamalla zana jarabawar kowa ya fito, ba’a wani tsaya b’ata lokaci na ban kwana ba saboda akwai shagalin da za ayi na ban kwana a daren yau. Daga nan Renaux motor’s suka wuce, abun birgewa daga yanda take tafiya da k’arfi a cikinta da kuma salo, bayan gaisuwa da take samu daga wajen ma’aikatan wasu daga ciki kuma na biyarta a baya, wani makeken office suka shiga inda ta wuce kai tsaye kan babbar kujera ta zauna, table d’in na gilas ne inda ta d’ora hannayenta tana kallonsu, suma zaune sukayi kan wasu manyan salon dake dake gefenta ta juyar kujerarta tana kallonsu, tattaunawa suka shiga yi na manyan motocin da take son ganin sun k’irk’iro, inda kowa ya nuna mata tunaninshi da zanen fasalin yanda komai zai kasance, a k’arshe zaman nasu ya tashi cikin farin ciki da k’ara bawa kowa k’arfin gwiwa.

Da dare ta shirya dan tafiya partyn tare da dreba, tayi mamaki sosai yanda mahaifinta ya barta babu tambaya ko jadadda mata ta kula, tana fitowa cikin jan doguwar rigar kanti ta had’u tayi kyau cikin gyaran gashi da dogayen takalma. Tana shiga suka d’auki hanyar makaranta inda za ayi partyn a cikin filin, kowa ya k’ure a daka yayi shiga ta kece raini, rawa ake da cakarewa ana korawa da nemu da ‘yar giya sama sama.

Tana gefe tsaye tana kallo daga nesa, wani matashin saurayi ne ya zo kusanta tare da cewa “Hi.”

Kallonshi tayi tace “Hello Amit.”

A harshen turanci yace “Ko zamu iya sha a tare?”

D’aga kafad’a tayi alamar ba komai, da sauri ya d’auki bol d’in lemu lokacin da wani water zai wuce, mik’a mata yayi ta amsa amma bata sha ba, yana d’an kurb’a yana kallonta sai kuma yace suyi rawa, bata mishi musu ba suka shiga filin suna d’an taka rawa, cikin matsatsin mutane daga baya aka d’an turo shi, hakan yasa shi d’an tab’a jikinta, ta kalleshi kafin tace wani abu taji an d’auke fuskarshi da mari.

Da sauri ta bishi da kallo inda ya fad’i k’asa tare da kallon wanda ya mare shi daga baya.

Da tsananin mamaki da firgici “Who are u? What are u doing?”

Da sauri ta durk’usa ta rik’e Amit d’in dan su tashi, wata fincikowa mutumin ya mata ya mik’ar da ita tsaye kamar yar tsana, fizge jikinta tayi da k’arfi tana kallon mutumin, ba wani mummuna bane, sanye da bak’ak’en kaya riga shemise da wandon jeans, fuskarshi d’auke take da bak’in gilashi da kuma kakkauran saje, za tayi magana cikin hushin ya nuna ta da yatsa yace “Stay away!”

Da mamaki ta kalleshi inda shi kuma ya kalli Amit yace “Last warning, kada ka sake bari jikinka ya tab’a na ta, ko da a mafarki ne.”

Jinjiga yatsarshi yayi alamar ka gane, da sauri ya d’aga kanshi alamar eh, ganin kowa yana kallonsu sai taji ya gama kunyata ta, cikin jin haushi ta tattare doguwar rigarta ta fita da sauri kamar zata fashe da kuka, to wanene ma? Wanene shi da zai mata haka? Bata san shi ba, bata tab’a ganinshi ba ma sai yau, har yake wani kashedi kar a sake tab’a ta.

Ko da ta fito ya ciro sigari a aljihunshi yasa mak’yasta ya kunna, ya zuk’a na d’aya zai sake kai wa baki ya tuna ta fita ita kad’ai fa, shi kuma tsaronta ne abu mai mahimmanci gare shi, ya kareta ko da zai rasa rayuwarshi, haka aka fad’a masa, dan haka yayi cilli da sigarin ya fita da wani matashin gudu zuwa waje. Waige waige ya shiga yi amma bai hange ta ba, da sauri ya kaiwa iska naushi yana fad’in “Ohhh shittt!”

Da gudu ya nufi inda motarshi take, Honda ce ash colour ya birka a hankali yana dubata, saida yaji wani dad’i daya hangeta tana tafiya ita kad’ai da sauri sai yarfa hannaye take, birki ya ci a gabanta ya sauke gilashi cikin dakakkiyar muryar bayar da umarni yace “Shigo ciki.”

Cikin fad’a ta kalleshi tace “Hey leave me alone, ho are u?”

Giftawa tayi ta wuce shi hakan yasa shi fita daga motar, da tako biyu ya rik’o hannunta wanda ya haddasa mishi jin wani fad’uwar gaba tare da jin kamar wutar lantarki ta kama shi, ita kanta saida ta d’an zabura dan ji tayi kamar wuta ta ja ta, k’ok’arin k’wace hannun ta shiga yi tana fad’in “How dare u tauch me? Leave me.”

Jawota yayi ya nufi motar da ita tana ta masifa “Hey u, u hunt me! Leave my hand..”

Saida ya wurgata cikin motar ya rufe kafin ya zagaya ya shiga shi ma, bala’i ta shiga surfa mishi amma ko a kanshi baya jinta sai sigari da yake ta sharb’ar kayanshi, tunani tayi to ko baya jin yaranta, a hankali cikin son kama abinda mahaifinta ya koya mata tace “Kai baka jina ne?”

Da sauri ya kalleta sai kuma ya kalli gabanshi, bai tab’a sanin ta iya hausa ba bare taji, kenan abinda ya fad’a ma yaron can taji me yace? Karta fahimce shi ba daidai ba fa, ci gaba yayi da tuk’inshi bai tanka mata ba har saida ya tsaya k’ofar gidansu, mamakinta ya akayi yasan gidansu? Da sauri ta fita ko rufe mishi k’ofar ba tayi ba tana fad’in “Yau na farko a rayuwata zan sa Abhi ya kashe min mutum.”

Da kallo ya bita har mai gadin dake tsaye ya sara mata tare da bud’e mata k’ofar tamgamemen gidan mai kama da masaukin bak’i ta shige. A hankali ya tsinci kanshi da murmusawa, jawo k’ofar yayi ya wuce yana jefar da sigarin a waje.

Shekarunta goma sha takwas, doguwa ce sosai mai k’irar turawa, bata da wani girman nonuwa sai dai a tsaye suke, yanda cikinta ke shafe haka mazaunanta ma suke babu tudu, fara ce tas mai sirkin masara a cikin farin, idonta bak’ak’e masu had’e da lainin k’asa k’asa, haka gashin kanta ma bak’i ne amma akwai ratsin kalar k’asa k’asa, mahaifiyarta Samanta yar asalin k’asar England ce, yar shahararren mai kud’i ce sosai, mahaifinta bahaushe ne haifaffen Niger, sai dai ita an haifeta England ta girma a Tha茂lande a haka kuma kullum cikin yawon k’asashe ake ita da mahaifinta, ya tara mahaukatan kud’ad’e da suka sa har iyayenshi suka koma ga Allah basu tab’a cin k’wandalarshi ba tunfa suka fahimta, a gari da yan uwa ana ta tsegumin kud’inshi bana halak bane, dan abun ya k’amzace, hakan kawai ya sa shi zamanshi a Tha茂lande tare da ‘yarshi bai damu da had’ata da danginta ba na uwarta ko na shi, kuma a hakan ma wai iya abinda yake iya d’auka ne idan zai tafi suka gani, basu ga inda yake zaune ba da harkokin da yake juyawa, su kansu k’asar wajen dan kar a saka shi gaba da wasu cibiyar bincike da waye waye yasa shi kullum cikin bud’a masana’antu yake, campanie na kaya na mota madara kayan cimaka da masarufi, har an kai k’adamin da saida ya mallaki manya manyan jiragen ruwa dake d’aukar mutum da kayanshi da kuma conteneurs dubunai, cikin garin Tha茂lande da da k’etare har har zuwa fad’in nahiyar an sanda waye Elhaj Shakoor Aghali.

Ko da ta shiga kai tsaye wani babban falo mai zaman kansa ta wuce, tsaruwarsa ma ba zai misaltu ba sai dai kawai ka k’iyasta, wani siririn jan haske ne kawai ya gauraye d’akin, yana tsaye yana d’an safa da marwa da alamar damuwa a fuskarshi, yana ganinta ya taho da sauri tare da rumgume ta yana fad’in “Ina kika shiga? Ya kika dawo ba tare da kin jira dreba ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button