NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Da sauri ta janye hannun Mama tana wani marayan kuka tana neman yin kwance, ciwo ne da babu dad’i ko kad’an dan bata tab’a jin irinshi ba, wata irin k’ara ce cikin yayi irin rugugugu d’in nan.

A tare suka kalli juna Mama ta d’ora da “Kaji ko, yunwa ce wallahi.”

Tsaki tayi ta mik’e ta shiga uwar d’aki, madarar da take anfani da ita saboda ulcer d’inta ta samu kofi babba ta zuna ta fito ta saka mata ruwan d’umi, shigowa tayi da niyyar bata saita samu Salahadeen ya zage sai shafa gashin kanta yake ya d’an hura mata iskan bakinshi a goshinta da yaga har wata zufa zufa ke tsatsafo mata, da sauri ta zauna ta shiga k’ok’arin tallabota.

Da sauri ya tallabota a hankali tare da rumguma bayanta a k’irjinshi, karb’an kofin yayi ya kai bakinta tasa ta kurb’a a hankali, yana bata tana kurb’a sannu sannu Farha ta shigo da sallama, da k’yar sallamarta ta fita a k’arshe saboda abinda ta sake tararwa.

Har zata juya ta koma Mama tace “Farha shigo mana.”

A hankali ta juyo ta shiga takowa kamar wacce k’wai ya fashe ma, cikin dubara ya janye Sarah daga jikinshi ya zaunar da ita kan k’ugunta, mik’a mata kofin yayi ta karb’a hannu biyu tana sha bata ko damu da Farha ba.

D’an zaune tayi ta kalli Mama tace “Sannu da dawowa Mama.”

“Yawwa Farha, kina lafiya?”

Saida ta sake satar kallonshi amma ba tace komai ba, jin tayi shiru yasa ta kalleta tace “Farha kina son wani abu ne?”

Girgiza kai tayi tace “A’a dama na shigo na gaishe ki ne kawai.”

Murmushi tayi tace “Nagode, da safe zan fita ai ke kuma baki fito ba.”

Shiru ta sake yi a hankali ta mik’e tana kallonshi ta fita daga d’akin, saida ta gama tayi kwance kan k’afafun Mama, kallonshi Mama tayi tace “Anjima ina son ganinku kai da su Zeid gaba d’aya.”

Kallonta yayi yace “Mama lafiya ko? Ko wani abu ne ya faru?”

Girgiza kai tayi tace “Ba komai, ka fad’a musu dai.”

“To.” Ya fad’a cikin girmamawa.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:03 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               1锔忊儯4锔忊儯

Sun fita farfajiyar gidan dan cin abinci Sarah taje bakin panpo ta wanko hannunta, ta juyo zata koma Farha da bata kula da ita ba tasa iya k’arfinta ta bangaji kafad’arta, baya baya tayi da k’arfi tana neman fad’uwa tayi saurin rik’e kan panpon gam, kallonta tayi da mamaki sai dai bata san da wane yare zata mata magana ba, Farha kuma cike da tsanarta ta kalleta ta nuna ta da yatsa tace “Ke makauniyar ina ce? Baki gani ne da zaki bige ni?”

Sakin panpon tayi ta tsaya kan k’afafunta sosai tana ci gaba da kallonta, da sauri ta kai hannu kamar zata tsone mata ido tana fad’in “Malama daina kallo na da idonki kamar na aljanu, kuma kika sake had’a hanya dani saina yi k’asa k’asa dake a gidan nan.”

Ganin ita dai kallonta kawai take tana gane wane yaren wani kuma ko a jikinta yasa Farha mata alama da hannu cikin tsawa kamar ta samu ‘yarta tace “Dallah wuce ni ki bani wuri.”

Saida ta jinjina mata kai ta wuce inda ta bita da fad’in “Aikin banza kawai.”

Duk abinda ya faru kan idon Mama da kuma Mamuh, hakan yasa ko da Farha ta shiga d’akinta Mama ta bi bayanta dan bata ji dad’i ba, duk da ta amsa sallamar Mama amma bata iya d’aga kai ta kalleta ba bare tace ta zauna, wani murmushi Mama tayi mai ciwo ta zauna kan kujerar dake nan, kallonta tayi sosai yanda zata fahimci kowane motsinta da yanayinta kafin tace “Farhana me yasa kika ma Sarah haka?”

K’ara sunne kanta tayi tana ta auka lomar abinci baki da gani kasan ranta a b’ace yake sosai, jin bata tanka mata ba yasa tace “Farha karki jawa kanki raini wajen Sarah bare har ki bata damar da wata rana zata mayar miki da martani, nan gidan mijinki ne da kike da iko dashi, amma ki fahimci wani abu d’aya, a halin yanzu da muke ciki Sarah ma nan gidan mijinta ne, Farhana banda niyyar cutar dake dan ina miki so kamar su Iffatu dana haifa, ni na raineki da hannaye na biyu tun bayan rasuwar iyayenki, ba na amince da aurensu dan a b’ata miki rai bane.”

Dafa kafad’arta tayi ta ci gaba da cewa “Farhanatu yarinyar tana cikin matsala sosai, mahaifin daya haifeta ne yake son kasheta saboda abun duniya, ganin rayuwarta tana cikin hatsari ne yasa Salahadeen tausaya mata ya taho da ita nan, ba komai tsakaninshi da ita hasalima ya fad’a min ita ko sunanshi bata sani ba har yanzu, kawai yana so al’amarin ya daidaita ne ta yanda zata iya samun tsaro daga jami’an can garin, haka na faruwa kuma zai d’auke mata igoyin aurenshi dake kanta ne tayi tafiyarta, kin fahimta?”

Kai kace ba cikin ilimi da sanyi aka mata magana ba sai kuwa ta kalli Mama rai b’ace tace “Amma mama me yasa d’azu na same shi a d’aki shi da ita? Akan me zai dinga yarfa yana tab’a jikinta in har babu komai tsakaninsu.”

Kallonta tayi sosai tayi wani murmushi dan ta fahimci haukan kishi ne zai fara d’awainiya da ita, kuma idan bata yi gaggawar tsayar dashi ba zata wahala a banza, cikin murmushin tace “Kiyi hak’uri to zan fad’a masa ya kiyaye, kuma bana jin haka kawai ma zai tab’a jikinta ba tare da wani dalili ba.”

Bata kula mama ba haka ita ma ta fito daga d’akin tana jinjina sabon canji na lokaci kad’an daga an shiga sabgar mijinta.

Da yamma suna zaune Mamuh ta fito daga d’aki cikin shirin atamfa riga da zani, kallonta Sarah tayi cike da birgewa tace “Kayanki sunyi kyau sosai.”

Dariya mama tayi tace “Kina son irinsu ne?”

Jinjina kai tayi alamar eh tana murmushi, kallon Mamuh mama tayi tace “Auta d’auko mata kayanki ta saka, idan Salahadeen ya shigo zan sa ya samo mata atamfa.”

Murmushi tayi tace “Mama nawa zasu mata?”

Kallon Iffa tayi da bak’in rai ya mata yawa tace “To na waccen ne zasu mata? Sai na ki ai kunfi dacewa.”

Tsaki Iffa tayi hakan yasa Mama kallonta cikin taushin murya tace “Iffatu sai nawa zan fad’a miki ki daina saran yin tsaki? Me yasa kika cika d’acin rai ne? Kina mace amma kin d’auko bak’in hali ki d’orawa kanki.”

Mayar da kallonta tayi kan Sarah ta kalli gashinta tace “Gobe dai zan miki kitso a gashin nan, dan bana son ganinshi haka yana ta yawo.”

Jinjina kai kawai tayi alamar to, fitowar Mamuh yasa ta mik’e tsaye tana karb’ar kayan, cikin zumud’i kawai ta cire rigarta bata damu da wanda suke tare da ita ba, da sauri Mamuh ta d’auki rigar ta zuge mata zip ta mik’a mata, sakawa tayi Mamuh ta juya ta saka mata zip d’in.

Ikon Allah sai kuwa rigar nan ta mata kip gwanin birgewa kamar dan ita dama akayi d’inkin, saida Mamuh ta d’ora mata zanin mai yanka kamar siket sannan ta kalleta tace “Cire wandon ta ciki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button