NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Cire wandon tayi sai Mama data juyota ta d’aura mata zariyar zanin ta baya, masha Allah tubarkallah shine abinda mama ta fad’a, kallonta tayi da kyau tana mamaki, tayi kyau sosai a cikin kaya wanda ta kasa gane sune suka fito da ita ko ita ce ta fito da d’inkin, zanin ya mata kamar ta saka siket ya fito da shap d’in faffad’an k’ugunta, haka ma rigar ta zauna daram kan k’ugun amma bata rufe shi sosai ba, inda a gaban kuma gidan nonuwan da aka ma rigar sukayi daidai nata maman suka zauna.

Iffa dake zaune ganin yanda kayan suka karb’i jikinta daga sawa d’aya da kuma gashinta daya zauna baya saita fito mata kamar wata bafulatanar asali ko kuma buzuwa, tsaki taja saboda kawai haushi ta sake bata, Mama kuma cikin washe baki tace “Ah wallahi bari Salaha ya shigo, irin wannan kyau haka da kika d’auka ‘yata, kinga yanda atamfa ta miki kuwa?”

Sarah dai banda kallon kanta tana juyawa babu abinda take sai murmushi, haka har aka kira sallah magriba suka mik’e dan yin alwala, saida Mama ta fito daga ban d’aki ta zauna kan kujera tana alwala Sarah ta kalleta tace “Mama.”

Da “Na’am.” Ta amsa mata tana kallonta, cikin nutsuwa tace “Wani abu na bani mamaki sosai.”

Tana shak’a ruwa a hanci tace “Kamar me fa?”

A hankali ta shiga fitar da kowace kalma a harshen hausa tana fad’in “Nayi yawo a duniya da k’asashe daban daban, abu d’aya dana lura dashi akwai abin bautar da mutane d’aid’aiku ne ke bauta masa, amma a kowace k’asa a kowane gari kuma zaka samu akwai musulmi, ko me yasa haka?”

Murmushi mama tayi tana alwala tana fad’in “Sarah wannan alk’awari ne na ubangiji cewa zai kare addininsa da kuma shigar dashi a kowane lungu da sak’o, ita gaskiya duk yanda aka so danneta jijjiga take ta fito da k’afafunta, addinin musulunci shine addinin gaskiya wanda ubangiji ya tsarkakeshi sannan ya aiko mana manzannin da zasu haska mana hasken, wannan shine dalilin da yasa kika ga a ko ina sai kin samu musulmi.”

Jinjina kai tayi cike da gamsuwa ta bi mama da kallo data mik’e ta shiga d’aki dan gabatar da sallah, suna idar sallah su Salahadeen ma suka shigo, ita kad’ai suka samu zaune tana daddana yatsun k’afarta, Mustafa ne kad’ai ya iya ce mata “Barka da hutawa.”

Da murmushi ta amsa mishi da “Sannu.”

Kallon juna sukayi da Salahadeen saida dukansu gabansu ya fad’i sakamakon tunawa da abunda ya faru d’azu, d’auke idonta tayi daga kanshi, rankaya sukayi d’akin Mama da sallama suka shiga, kan sallaya suka sameya ta idar da sallah.

Zaune sukayi dukansu kafin ta kallesu dukansu tace “Har kun dawo?”

“Eh mama, anwuni lafiya?” Cewar Zeid, gyara zama tayi ta fuskance su sosai tace “Dama magana nake so muyi daku.”

Mamuh data idar da sallaha take zaune sai Iffa dake zaune ita ma dan ba sallah take ba mik’ewa sukayi zasu fita Mama tace “Dawo ku zauna.”

Zaunawa sukayi suna kallonta cikin nutsuwa, ita ma a nutse ta kallesu tace “Magana ce dama akan gadon wajenku wanda sanda aka raba shi kai Salahadeen baka nan, sauran kuma duk suka ce na rik’e musu har ka dawo sai asan abunyi, shine nake so naji wace shawara kuka yanke zakuyi da kasonku da zai anfanar daku?”

Dukansu kallon Salahadeen sukayi hakan yasa ya kallesu shima yace “Ya kuka kalle ni? Kowa ya fad’i abinda yake ganin zai iya yi mana.”

Mustafa ne yayi saurin cewa “Ni Mama a bani kud’in nan so nake na fara siyo kaya daga Libye ina kawowa nan ina siyarwa.”

Dukansu dariya suka saka mishi sai mama da tace “Meye na mishi dariya kuma? Abinda yake so ne ya fad’a, mu bishi da addu’a mana ta fatan dacewa.”

Kallon Zeid tayi tace “To kai fa?”

Kallon Salahadeen yayi yace “Mama ni duk abinda yaya Salahadeen zaiyi shi nake so.”

Kallon Salahadeen tayi tace “To kaji kai, me kace kenan?”

Saida ya numfasa yace “To mama ni dai nafi so na fara da babbar harka.”

Nisawa tayi tace “Tunda hakane kawai zanje k’auye sai nayi magana da Baffan naku a siyar da gonakin, kaga sai a baku kud’in kuyi abinda zakuyi dasu.”

Salahadeen ne yace “Hakan ma yayi Mama, yaushe zaki tafi kenan?”

Kallonshi tayi tace “Eh to sai dai zuwa jibi insha Allahu, tunda gobe akwai makaranta amma ranar litinin ba ma karatu saina tafi, auwa washe gari da safe saina dawo.”

“To mama Allah yarda.”

Da “Ameen.” Ta amsa kafin ta mik’e ta cire hijabi.

Ko da suka fito mazan waje suka nufa, Sarah dake tsakar gida ita kad’ai da sauri ta mik’e ta bi bayansu, suna fita ta gansu tsaye k’ofar gidan. Shi kanshi kallonta ya shigayi na ganin shigar jikinta, har ga Allah bai tab’a jin ya kalli mace ta birge shi ba kamar yau, tayi masifar d’aukar hankalinshi cikin kayan da suka zauna mata daram.

Yayi nisa cikin kallonta kawai yaji tana fad’in “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:03 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               1锔忊儯5锔忊儯

“Mr. zamu iya fita tare?”

Kallonta duk sukayi sai dai ba da Salahadeen take ba sai Musfata da ta ga ya hau moto, cikin murmushi ya kalleta yace “Matar yaya suna na Mustafa.”

Murmushi ta masa tace “Please Tafa zan iya zuwa mu tafi? Na gaji da zamane haka.”

Zeid ne ya bushe da dariya jin sunan data saka mishi, hararenshi yayi kafin ya kalleta ya kalli Salahadeen da shima yake hararan da yace wai matar yaya, cike da zolaya yace “Ga mijinki nan ki fad’a masa saiya fita dake.”

Saida ta turo baki gaba ta kalleshi, wani kallon kar ma ki fara ya mata tare da juya kanshi, kallon Mustafa ta sake yi tace “U see? Ba zai yarda ba ya fita dani ba, she hate me.”

Saida yayi saurin juyowa ya kalleta, ganin bashi take kallo ba yasa shi d’auke kanshi, cikin rashin damuwa Mustafa yace “Muje to, amma ba zamu jima ba.”

Da sauri ta tako zata nufe shi Salahadeen yayi saurin cewa “Ke.”

Tsayawa tayi ta juya ta kalleshi tana rik’e da zanin a hannunta, babu alamar wasa a tare da fuskarshi yace “Koma gida.”

Sake turo baki tayi gaba sosai ta sake tattare zanin ta shiga bubbuga k’afafu ta fashe da kuka ta shiga ciki, dariya Mustafa yayi yace “Baka so na fita da ita kuma kai ba zaka fita da ita ba.”

Kallonshi yayi yace “Tafi inda zaka je.”

Har zai fice daga k’ofar gidan yaji mama na k’wala kiran sunanshi, saida ya girgiza kai ya juya ya shiga ciki, tsaye ya same su amma kanta na saman k’irjin Mama tana kuka, cike da tuhuma mama tace “Kai ka korota?”

Cikin ladabi yace “Mama ni fa nufi na shin…”

Dakatar dashi tayi da cewa “Kaga Salahadeen, ya kamata ace ka fahimci k’ok’arin yarinyar nan, fita da zatayi ne zaka hana ta, akan me to?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button