NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Cikin son kare kanshi yace “Mama ni fa ba hanata nayi ba, kawai dai ta saka hijab ta canza wannan takalmin saita tafi.”

Kallonta tayi ta d’ago kanta tace “Je ki ce Mamuh ta baki hijab ki saka da takalmin daya siyo miki sai ki zo ya tafi dake.”

Da sauri ta juya ta shiga d’aki ya bita da kallo, saida ta shige ya kalli Mama yace “Mama Mustafa har ya tafi, ta hak’ura har gobe mana.”

Juyawa tayi zata shige d’aki tana fad’in “Da kai zaku tafi.”

Da sauri yace “Ni kuma Mama?”

K’ala ba tace mishi ba ta shige ciki ta bar shi, fita yayi yana k’wafa da niyyar doguwar tafiya da ita kuma a k’afa, saita gwammace bata fita ba tunda dai jaraba gare ta, wani dogon hijabi Mamuh ta bata wanda ya kusa rufe har k’afafunta, sai takalmin daya siyo mata suma masu d’an tsini ta saka ta fito, ko da ta ga baya nan farfajiya da gudu ta fita tunanin karya barta.

Turus ta tsaya ganinshi a k’ofar gidan, juyowa yayi ya sauke idonshi akan ta, a hankali ta shiga takowa har ta tsaya gabanshi ta kalli kanta ta kalleshi tace “Mu tafi.”

Nuna mata hanya yayi yace “Muje.”

Kallon hanyar tayi ta kalleshi tace “A k’afa?”

Cikin shu’umin murmushi ya jinjina mata kai alamar eh, takawa tayi suka jera a hankali suka fara tafiya, k’afafunta ya kalla yayi murmushi a ranshi yace “Za aci kwakwa.”

Fuskarta ya kalla, tsaf zaka iya gane tana da yalwar gashi sosai kuma mai sulb’i saboda hijabin ya d’anyi baya kuma babu kallabi? Amma yanda hijabin ya mata kyau sai tafi birgewa a cikinshi, amma rashin sabo yasa yana gani sai tayi kamar zata cire hannayen dake ga hijabin kuma saita mayar, sai ta kama sama wajen goshi ta janyo gaba kuma ta koma ta mayar dai, sannan k’asa ma wajen wuya sai jujjuyashi take.

Suna cikin tafiyar ta kalleshi tace “Mr., zan iya cirewa dan Allah? Ya shak’eni sosai fa.”

Hararanta yayi yace “Sai dai ki koma gida in dai hakane to.”

Kyab’e fuska tayi kamar zatayi kuka tace “Shikenan to.”

Sun d’an tafi kad’an ta sake kallonshi tace “Mr., me yasa ne anan mata ke saka wannan?”

Kallonta yayi tare da kallon hijabin data nuna, murmushi yayi ya kalli gabanshi yace “Ya kika ji kanki da kika saka shi?”

Saida ta numfasa tare da d’an matsawa kusanshi ta zura hannunta cikin hannunshi ta rik’o, kallonta yayi ya kalli hannun data rik’e gam tana k’ara mitsitsikewa ba tare data wani damu ba tace “Ina jin duk ya takura min ya hana ni sakewa, zafi ya dame ni bana shan iska da numfashi mai kyau, but…”

Sai kuma tayi shiru, kallonta yayi yace “Uhum.”

Saida ta sarkayo hannunshi ta kan kafad’arta ta gyara hannunta ta rik’e hannunshi ta gaban wuyanta sannan tace “Ina ji a jikina ba kowane irin iska bane ke ratsa jikina yana shiga, haka kuma ba wanda ke ganin abinda ke cikin jikina saini dana rufe shi, sai nake jin kamar ina cikin wata rundunar sojoji mai k’arfin gaske wacce ke bani kariya daga dukkan abun cutarwa.”

Kallon fuskarshi tayi tace “Dad’i nake ji haka kawai, sannan ina ji a cikin zuciyata kamar nayi abinda ya dace.”

Murmushi yayi tare da b’anb’are hannunta daga nashi ya d’an ja nesa da ita sannan yace “Haka abun yake to, banbancinki a yanzun da wacce bata saka hijab kamar banbancin dake tsakanin rufaffen abinci ne da kuma bud’add’e, kinfi kyau a cikinshi, kin samu kwarjinin da ba kowane irin sakarai bane zai samu k’arfin gwiwar yi miki magana, kin samu kariya daga shed’anu na mutane dana aljanu, fatarki ta samu kariya daga iska mai cutarwa, hatta shi kanshi gumin da kike wani babban sirri ne da wanda ya kusanci kawai zai iya fayyace miki shi, fatarki kanta zata k’ara laushi da d’aukar d’umin da kowane namiji zai so samun wannan d’umin a jikin mace, san..”

Cak ya tsaya saboda yanda ta k’ura mishi ido tana kallo, yana kallonta tayi sauri mayar da kanta kan titi, jin yayi shiru bai sake cewa komai ba yasa ta saci kallonshi, a daidai lokacin ya kalleta sai kawai ta sake sunne kai.

Babu wanda ya sake magana haka suka dinga bin titi tafiya kuma a hankali, sannu sannu ta ji ta gaji sosai da tafiyar, k’afafunta sun mata zafi sosai, ko a garinsu ta kanyi gudu yayin motsa jiki da tafiya, amma ba da takalmi irin wannan ba kuma, cikin furzar da iska ta kalleshi tace “Mr. mu koma gida mana, i am tired.”

Kallonta yayi cikin son yin dariya yace “Daure mu d’an k’ara kad’an sai mu koma.”

Marairaicewa tayi tace “Na gaji fa sosai, k’afata zafi take.”

Saida ya fashe da dariyar da yake rik’ewa kafin yace “Daure mu k’arasa, akwai abinda nake son nuna miki ne.”

Janta ya ci gaba da yi sai gasu har sun kawo foir, tun kafin su kai wurin ta shiga baza ido tana hangen k’yalk’yalin da wuri keyi tare da tashin k’amshi, da sauri ta kalleshi tace “Ina ne nan?”

Ba tare daya kalleta ba yace “Kasuwa.”

Ci gaba tayi da kallo har suka k’arasa, abu na farko daya fara shiga idonta shine turaren data gani fari bak’i ja da mai kalar k’asa k’asa cikin kwalabe masu kyau.

Salahadeen na tafiya shi dai yaji kamar wani nauyi ya d’an rage masa, waigawa yayi b’angarenta kawai ya ga wayam, da sauri ya shiga jujjuyawa yana dawowa baya ya ga inda ta mak’ale, ai kuwa shagon nan ya hangota tana d’aukar kwalaben turaren tana ta shinshinawa tana lumshe ido, mai turaren yayi tsaye yana kallonta yana k’ara fad’a mata nagartar turaren.

Yana zuwa ya tsaya daf da ita yace “Me kike yi anan?”

Juyowa tayi ta kalleshi tace “Mr. ina son wannan?”

Kallon inda ta nuna mishi yayi ya sake kallonta yace “Wane daga ciki?”

Duka ta sake nuna masa ya mata wani kallon baki da hankali, juyawa yayi ya tafiyarshi, saida yayi nisa ya juyo dan ganin wai tana biye dashi, tsaye ya hangota inda ya barta, tsaki yayi ya taho a hassale sai gani yayi ta b’uya a bayan mai shagon tana fad’in “Please mr. ina so.”

Kallon mai kayan yayi yace “Nawa suke?”

Saida ya d’auko kwalaben yace “Duka ake so yallab’ai?”

Saida ya kalli Sarah da har yanzu ke tsaye bayanshi tana ci gaba da kallon wasu abubuwa yace “Eh, duka take so.”

Had’e masa kud’in yayi inda a take ya ciro ya biya ba tare da ciniki ko wani abu ba, a leda ya saka musu ya mik’a ma Sarah, gaba yayi ta bi bayanshi tana ci gaba da kalle kalle, sun kusa kaiwa k’arshe ta ratse ta shige wani shago da taga su pant da bras masu kyau.

Yanzu ma yana juyowa bai ganta ya dawo baya, a shagon ya ganta sai dubawa take kamar mai kud’i a hannu, yana zuwa cikin turanci yace “Ki wuce mu koma gida dare yayi.”

Kallonshi tayi cikin shagwab’a tace “Mr. ina so fa, wanda ka siyo min jiya basa isa ta.”

D’an kallon kaikaice ya mata kamar zai ga abinda take fad’a, da sauri tace “Da gaske nake fad’a maka, basa isa ta wannan watak’ila kallon tsoro kake min.”

Cikin basarwa ya kawar da kanshi kafin ya kalleta yace “Amma kinsan ba siyayya muka fito ba ko?”

Jinjina masa kai tayi alamar eh, da kai ya mata alamar su wuce tare da cewa “Dan haka wuce mu tafi.”

Da sauri ta shiga tattare hijabinta har tayi nasarar d’aga sama tana fad’in “Dubi fa yau ban saka komai ba da zai bani kariya, haka kake so na ci gaba da yawo?”

Da sauri yaja hijabinta yayi k’asa dashi dan rigarta yaga tana neman zamewa daga kamar yanda wasu keyi in zasu bawa yaro nono, da sauri yace “Naji d’auki wanda kike so.”

Murmushi tayi ta juya cikin farin ciki ta ci gaba da dubawa, mace ce mai shagon da taimakonta ta fito mata da wasu kaloli ta zabi har kala goma, nan ma jimillar kud’in aka masa ya biya, suna fito a k’ofar shagon ta ga jigida, yanda take walk’iya duwatsun gwanin kyau yasa ta kamowa da hannu tana kallo tace “Menene wannan mr.?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button