SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Sanda ta gama rabawa ta d’auki nata ta fita, mama tare da Sarah ta zauna suka saka hannu, tunda ta kai na farko a baki ta kalleta tace “Mamie naman nan da dad’i, idan da shi nake samu ma sai nayi ta ci kullum.”
Dariya mama tayi ta kalleta kawai dan a harshen turanci tayi maganar, suna idawa suka wanke hannayensu da sabulu, kallonta mama tayi tace “Muje waje na kutse miki kan nan kinji.”
Daga yanda mama ta mata nuni yasa ita ma ta d’ora hannu akai da alamar tambaya, jinjina mata kai mama tayi tare da k’ara nanata mata tace “Kitso, kitso zan miki mai kyau na hausa.”
Da sauri ta d’aga kai alamar to, tsinka abun caje kai da mai mama ta d’auko suka fita farfajiya, mama na zaune kan kujerar k’arfe mai tsayi ita kuma kan tabarma.
Lafiya lau mama ta d’an sharce mata shi ta tsaga, ko da mama ta kama kitson tare da bismillah sai Sarah taji wani ziiii kamar zatayi fitsari, wani zafi taji ya ratsa kwanyar kanta har zuwa tafin k’afa, hakan ya haddasa mata had’e k’afafunta tana mutsitsikasu, duk’e kan ta fara yi tana so ta kubce tare da d’ora hannayenta biyu duk ta rufe kan. Mama ce tace “Lah Saratu, karki sa na miki dariya mana, ko kukan kitso zakiyi?”
Cikin jin rad’ad’i tace “Mamie saki, sake ni zafi bana so.”
Sake jawo kanta mama tayi tana fad’in “Ke zauna haba na miki kitso, a hankali zan miki fa.”
Jin mama bata saki ba kuma zafin k’aruwa yake sai kawai ta fashe da kuka tana kiciniyar k’watar kanta, Mama ko da abun ke bata dariya saita k’i sakinta sai dariya da take tana fad’in “Yau ni naga k’atuwar banza ganin idona, ke kuka kitso ne kike?”
Iya k’arfinta ta sake bud’e baki tana turmutsutsun tserewa, jin wannan kukan yasa Farha fitowa da sauri dan ganin me ke faruwa, tana ganinta taja tsaki ta juya ta koma. Shima zai shigo gidan yaji wannan kukan, da sauri ya k’ara sautin tafiyarshi ya shigo ido bud’e da son hangon meke faruwa.
Da k’yar ya iya kawo kanshi kusansu ya tsaya tsabar mamaki, ba tare daya daina mamakin ba yace “Mama me ye haka? Kuka ne take?”
Kafin mama tayi magana ta warto k’afarshi da yake tsaye kusanta, jawo k’afar tayi a dole ta tilasta mishi matsowa kusanta, tana rik’e da k’afar tayi k’ok’arin mik’ewa tana fad’in “Mr. ka ce ta sake ni, bana so bana so, zafi ke akwai a sake ni.”
Kallon mama yayi yace “Mama sake ta mana tunda bata so.”
Ko kallonshi ba tayi ba tace “Rufe min baki, haka zata yi ta mana yawo a gida da gashi a hargitse?”
Da sauri yace “Amm..”
Bai gama fad’a ba Sarah tayi nasarar yin wuf ta mik’e, bata b’ata lokaci ba wajen zabgawa da gudu tayi k’ofar fita, da sauri mama tace “Ke ke, karfi fita a haka.”
Tsayawa tayi ta juyo amma ba tace komai ba sai kallon Mama da take tana share hawaye da hannu d’aya kuma tana shafar kitson da aka fara, kallonta Salahadeen yayi yace “An ji kunya dai wallahi, kukan kitso da girmanki.”
Gwalo ta musu tana juya kanta hakan yasa mama yin dariya, shi kanshi saida ya murmusa tare da girgiza kai ya aje ledar hannunshi gaban mama.
Hanyar fita yayi hakan yasa mama cewa “Yawwa kamo min ita.”
Wuf ta k’arasa waje tana fad’in “Bana so Mamie.”
Dariya ta sake yi shi kuma ya fice, tsaye ya same ta sai kallon tsoro suke wa juna ita da Kasim, kallonta yayi yace “Shiga ciki.”
Mak’ale kafad’a tayi alamar a’a tare da cewa “Um um, Mamie zata kama ni.”
Saida ya d’an saci kallon Kasim kafin ya kalleta yace “Ba zata kama ki ba, kije ciki kinji ko.”
Da sauri tace “Sai dai kaje ka fad’a mata da kanka karta kama ni.”
Saida ya mata wani kallo kamar zai bigeta ya lek’o cikin gidan, fad’awa Mama tayi kafin ya kalleta yace “Wuce to, idan kuma kika tsaya babu ruwana aka d’auke ki.”
Yana fad’a ya shige mota suka bar wurin. A hankali ta shigo saida mama tace ba zata mata ba kad’ai.
Da dare ya so bata sak’on wajen mahaifinta amma ya samu har tayi bacci, dan haka kawai ya k’yaleta da tunanin gobe ya bata. Inda mama kuma ta shirya tsaf tana jiran wayewar gari ta tafi k’auye.
Daren yau ma kamar jiya, dan abunda ya faru sak irin na jiya kamar maimaici, yau ma mama ta mata addu’a ba tare da an taso Salahadeen ba. Ko da ta samu nutsuwa mama ta kalleta tace “Ya kamata ki dinga addu’a kafin ki kwanta, saboda idan kikayi addu’a zaki tsira daga duk wani sharrin abun hallita.”
Kamar za tayi kuka ta kalleta tace “To amma mamie me yasa haka ke faruwa dani? Ban tab’a jin irin haka ba.”
Shafa kanta tayi tace “Kinga ko gashin nan haka a sake shed’anu suna saurin cutar da mace idan kanta na zama sake, amma idan kika kiyaye zaki ji ki a sake amma kuma cikin kariyar ubangiji.”
Jinjina kai tayi ta kalli mama sosai tace “Mamie me kika fad’a min a kunne na?”
Murmushi tayi tace “Littafi mai tsarki kenan, littafin da babu kamarshi, littafi dake daidai da kowane zamani, littafi da har yau duk kushen mai kushen da k’irk’irar mai k’irk’ira an kasa kushe ko tusa wani abunda a cikinshi bare a k’irk’iri kwatankwacinsa.”
Wani murmushi ta saki tare da fad’in “Amma da dad’i.”
Ita ma murmushin tayi tace “Dad’insa ya wuce misali, tsarinsa ya wuce tunani, fikira da zalak’ar dake cikin ta wuce hangen mai hangen, fasaha da harshen da akayi anfani wajen fad’an kalmomin cikinsa ya wuce aikin mutum ko mala’ika, Alqur’ani mai girma kenan.”
*Washe gari*
Tana bacci Mama ta tafi k’auye ba tare da sunyi sallama ba, su Iffa kuma duk sun tafi makaranta, dan haka yau ma ko da ta farka daga ita sai Farha a gidan, a lokacin Farha na d’aki tare da k’anwar Mamanta, ita ma ta zo gidan nan dan taji mijinta ya zo, sirrikka ta gama had’a mata na gyaran jiki, sun fito zata rakata ta tafi daidai Sarah ta fito zata shiga wanka tana d’aure gashinta.
Kallonta tayi a tsorace ta lab’e bayan Farha tana fad’in “La’ilaha Illalahu aljana, Farhanatu aljana a gidanku.”
Kururuwarta ce tasa Sarah kallon wajen, wani murmushin takaici Farha ta saki tace “Aunty ba aljana bace, bak’uwar gidan ce.”
Ajiyar zuciya ta sauke ta fito daga bayanta tana fad’in “Bak’uwar gidan? Yaushe kukayi wannan bak’uwa ku kuma?”
Cikin hararan Sarah tace “Kwananta uku.”
Kallonta tayi da kyau tace “To daga ina kuma suka had’a iri da wannan jar fata haka?”
Saida ta kama hannunta suka nufi k’ofar fita tace “Aunty tare suka zo dashi.”
Da sauri taja ta tsaya ta rik’e hannunta tace “Ban gane tare suka zo ba, da wa?”
Saifa ta tab’e baki tace “Yaya Salahadeen mana.”
“To me ye had’inshi da ita?” Yanda ta kakkafeta da ido yasa ta kawar da kanta tace “Matarshi ce, amma sun ce ta bogi ce.”
Juyawa tayi ta kalli Sarah data d’ebi ruwa a panpo ta d’auka ta shiga ban d’aki, kallo ta mata na tsanake tace “Farhana me yake faruwa? Matarshi fa kika ce?”
Da sauri ta kalleta tace “Yi shiru aunty, yau kwana biyu kenan da d’aura auren, wai mahaifinta ne ke son kasheta ko me? Sun ce dai rayuwarta ce a had’ari shiyasa ya taimaketa, kuma a k’a’ida dole zata koma k’asarsu idan lokacin da suka d’iba ya cika, shine fa ya aureta amma wai zai saketa idan komai yayi daidai.”
Jinjina kai tayi tace “Kinji wani iskanci kuma? To ke kuma kika yarda?”
Murmushi tayi tace “To ya zanyi aunty? Abinda ma aka d’aura shi anan tsakiyar gidan?”
“To uban wa ya bashi auren? Ta fad’a cikin fad’a fad’a, ita kam da zata fahimta data bar maganar nan dan bata so, cikin rashin damuwa tace “Ubanta mana, aunty labari ne fa mai tsayi, zan zo gidan sai muyi magana.”