NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Wani kallo ya mata yace “Goyaki za tayi to? Ko mu duk ba mutane bane?”

“Amma ai babu mai so na a cikinku.” Ta fad’i hakane tana sunne kanta, zai wuce ta sake tare shi tana fad’in “Me Mamie taje yi a k’auye?”

Rik’e hab’a yayi alamar mamaki, cikin jin haushi yace “Wace irin tambaya ce wannan? Ba yan uwa gareta a k’auyen ba? To ban sani ba.”

Tsuke bakinta tayi tana mishi kallon Allah ya baka hak’uri, ficewa yayi ya barta nan inda ta tattara kayan ta aje kan kujerar.

Tana zaune su Iffa suka dawo, Mamuh kad’ai tace mata “Aunty Sarah ke kad’ai zaune?”

Da murmushi ta amsa mata da “Har kun dawo?”

“Mun dawo, Mama har ta tafi ko?”

Cikin farin ciki tace “Ta tafi, ni ma gobe zan biki idan zaki tafi.”

Juyowa tayi ta kalleta tace “Da gaske?”

Kai ta d’aga mata alamar eh, juyowa Iffa tayi taja tsaki tana fad’in “To waya fad’a miki kafirai na zuwa waje mai tsarki ne? Ki fara zama musulma kafin kice zaki je mana islamiyya.”

Kallonta Sarah tayi sosai, kalmar kafira ta sakata a kunnenta sai dai bata san ma’anarta ba, amma daga yanda ta mata magana tasan ba magana mai dad’i bace, dan haka bata kula ta ba ta d’auke kai, kallon Mamuh Iffa tayi tace “Ke da take fahimtar yarenki ki fad’a mata ta tashi ta share mana d’aki, bama zama da k’azanta, dubi yanda ta hargitsa mana d’aki.”

Kallonta Mamuh tayi tace “Ina aka hargitsa d’akin anan? Ni banga abinda yayi ba Iffatu.”

Cikin rashin kunya tace “Au baki gani ba ke? To bari kiga idan kunyar fad’a mata kike ji.”

K’ofar d’akin ta fita ta d’auko tsintsiya ta dawo, mik’awa Sarah tayi dake zaune tana kallon bakunansu tana jin wasu kalmomin wasu kuma sai dai taji kawai, karb’a tayi tana mata kallon tambayar me zanyi da ita? Da hannu ta mata alama tana fad’in “Shara, shara zakiyi malama.”

Da mamaki ta sake kallonta tana kallon tsintsiyar, ta mata tsaye akai tana jiran taga ta mik’e, Farha dake zaune tana wankin kayanta ta ji abinda suke magana akai ce ta shigo d’akin da sallama, ganin abinda ke faruwa yasa ta kalli Iffa tace “Karki ba kanki wahala, ba yi zatayi ba saboda yar hutu ce ita, yayanki kuma yana jin kin saka ta aiki zai miki tatass.”

Kallonta tayi tace “Ai kuwa sai dai ya kashe ni wallahi, haka kawai tana zaune sai dai a mata komai, Mama duk ta bi ta lik’e mata kamar ta haifeta, ina ma tsoron mayya ce wallahi ta kame mana uwa.”

Dariya Farha tayi tace “Har sai kin fad’a ma, ai da gani kinsan mayya ce.”

Cikin rashin jin dad’i Mamuh tace “Haba ku kuwa dan Allah, me yasa kuke hakane? Ko da dai ba komai take ji ba ai bai kamata kuna ci mata mutumci haka ba.”

Nunata tayi da yatsa da fad’in “Ke rufa mana baki kinji ko.”

Kallon Sarah tayi dake zaune har yanzu rik’e da tsintsiya tace “Tashi malama.”

Mik’ewa tayi tana binta da kallo, nuna mata daga inda zata faro tayi, girgiza kai tayi cikin koyon hausarta tace “Ban iya ba, ban san ya zanyi ba.”

Farha ce tace “To waye aka haifeshi da iyawa dama? Kowa ai da koyo ya iya.”

Wani kallon wulak’anci ta wa Farha tare da jefar da tsintsiyar gaban Iffa ta sake cewa “Ban iya ba, ba kuma zanyi ba.”

Kallon tsintsiyar tayi ta kalli Sarah, a k’ufule ta d’auki hannu ta kwad’awa Sarah mari, marin daya gigita tunaninta, ba wai dan zafinshi ba sai dan mamakin yanda yarinya kamar wannan ta mareta, bayan marin da mahaifinta ya mata a ranar yau shine karo na biyu, hawayen da bata so suka fito mata bane suka fito mata. Sakin wayarta tayi ta fad’i ta fita da sauri tana kuka, takalminta ta saka ta fice a gidan gaba d’aya.

Sai yanzu ne ta kalli erea da kyau, bata da cunkoso ko yawan mutane, sai dai akwai mutane na ta kai da kawowa, su kansu kallonta suka shiga yi dan babu wanda yasan da zamanta har yanzu. Hanyar da suka bi jiya ita dashi ta bi tana tafiya tana share hawaye, tunani take sosai yanzu banda sauyin rayuwa taya har za’a mata wannan cin fuskar haka? Komai dare yau ya dawo saiya mayar da ita inda ta fito ko ya kaita inda ita zata mayar da kanta, amma ba zata k’ara kwana a gidan ba tunda mutanen gidan basu da kirki idan ka cire Mamie.

Tana fita Mamuh ta juya da niyyar fita Iffa ta rik’eta tace “To azagwaigwai binta za kiyi?”

“Eh mana, idan fa ta b’ata?”

Cike da rashin damuwa tace “To sai akayi me? Ba ita ta so ba? Malama wuce ki d’ora mana girkin rana ni zan wanke kayan Mama.”

Fizge hannunta tayi ta fita a d’akin, karo na farko da dai wayonta ta fita k’ofar gida babu hijabi, tana hango Sarah ta k’wala mata kira, duk da taji amma bata kulata ba dan ranta ya b’ace. Bata da wata dubara daya wuce ta zuba a guje ta rik’ota, tirjewa sukayi a wajen ita tana so ta sake ta ta tafi ita kuma tana so su dawo tare, saida ta marairaice tace “Dan Allah ki zo mu koma, yaya fa idan ya zo bai same ki ba zai mana duka ne dukanmu.”

Turo mata baki tayi cikin shagwab’a tace “Ba zan koma gidanku ba, yarinyar nan bata da kirki bata so na.”

Cikin rarrashi tace “Yi hak’uri mu koma, idan yaya ya dawo zan sanar dashi yayi maganinsu.”

Saita ta sake turo leb’e gaba kafin ta biyota suka taho, suna zuwa k’ofar gidan taja ta tsaya tace ai ba zata shiga ciki ba har sai Salahadeen ya dawo. Saida ta mata alk’awarin babu inda zata je kad’ai ta shiga ciki dan aikin gabanta.

Duk da tana aiki amma tana yi tana lek’owa sai kuwa ta ganta zaune a k’asa tana kallon masu wucewa, dariya kawai take yi ta koma cikin gidan.

Shiru da rashin motsi yasa bacci d’auketa bata sani ba a wurin, gyangyad’i ta shiga sirfawa kamar tsohuwa daga zaune, tana haka har Kasim ya tsaya da mota ya sauke Salahadeen bata motsa ba. Shi dai kallonta yake ya ga ko da gaske ne? Saida ya sunkuya yasa hannu ya daddab’ata, zunbur ta bud’a ido kamar wacce ta tuna da wani muhimmin abu, kallonshi tayi da sauri ta mik’e tsaye tana kakkab’e jikinta tana fad’in “Dama kai nake jira, mr. ka mayar dani gida ba zan iya zaman gidanku ba, na fad’a maka babu mai sona anan.”

A dak’ile yace da ita “Shiga ciki to.”

Saida ta d’an juya baki kafin ta wuce ciki tana sumalin gyangyad’in da tasha, had’e fuska yayi ya bi bayanta da kallo, har zai shiga yaji Kasim yace “Sannu da k’ok’ari mijin baturiya.”

Yana juyowa yayi sauri ya shige mota yana mishi dariya, k’wafa yayi shi kuma tare da soka kai ciki ya shige, yana shigowa kai tsaye d’akin Mama ya shiga inda ya ga ta shiga, yanda ya shiga da k’arfi cikin jin haushi da niyyar mata bala’i, sai kuma yaja cak ya tsaya ganin tana duba fuskarta a madubi tana shafawa, yanda ya kula da fuskar yasa shi hango shatin yatsun hannu. Tambayar kanshi yayi “Waya mareta? Ko tun wanda mahaifinta ya mata ne?”

Kafin ya samu amsar tana ganinshi tayi saurin matsowa tana fad’in “Yawwa mr. na rok’eka ka mayar dani wajen Abhi, zan zauna dashi a duk yanda yake, please na rok’eka.”

Cikin hararenta yace “Bana ce ki bari Mama ta dawo ba.”

Ita ma hararenshi tayi tace “Nima ba na tambayeka me taje yi a k’auye ba amma baka fad’a min ba.”

Sakin baki yayi ganin yanda ta jujjuya mishi baki ga kuma uwar harara sama da k’asa, lallai! Ya fad’a a ranshi kafin ya juya zai fita, da sauri ta rik’eshi tace “Yaushe Mamie zata dawo?”

Saida ya kalli hannunta data rik’e rigarshi yace “Gobe.”

Sakinshi tayi tare da nuna masa kwalin kud’in nan tace “Ka d’auki kud’in ka tafi dasu to, ni idan zaka kaini wajen Abhi ma ka rik’e su duka.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button