NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Rik’e k’ugu yayi yana kallon fuskarta yace “Amma kina da k’arancin fahimta ko?”

Yanayin fuskarta ne ya canza amma ba tace komai ba, d’orawa yayi da “To naga dai na baki takardar daya rubuta miki, amma kamar baki fahimci komai ba.”

Cikin sanyin jiki da murya tace “Na fahimci komai, na gane Abhina yana cikin had’ari, shiyasa nake so na koma dan ni ya kashe ni, bana so na rasa shi na zama marainiya, ina tsoron Abhi ya kashe kansa dan na san waye shi, ba zai iya rayuwar talauci ba.”

Fita kawai yayi daga d’akin, Mamuh dake girki ya tsaya kusanta yana kallon fuskarta yace “Me aka mata?”

Saida ta saci kallon Iffa dake wanki wacce ita ma take kallonta dan taji abinda zata fad’a, a hankali ta kalleshi tace “Wacece?”

Hararenta yayi yace “Ban gane wacece ba? Sarah mana.”

Saida ta had’e yawu tace “Ba komai, me tace an mata?”

Juyawa yayi ya kalli Farha dake k’ofar d’akinsu zaune tana daka, jinjina kai yayi tare da k’wafa ya kalli Mamuh yace “Duk mai gani na da daraja ya kamata ya darajata abinda yake zamana a gidan nan.”

Juyawa yayi ya fice a gidan inda Iffa da Farha suka bishi da kallo, tab’e baki tayi tace “Kiji fa dani yake.”

Kallonta Iffa tayi tace “Ai wallahi ke kika k’yalesa ma da har ya had’aki da waccen aljanar.”

A ranar daya aiko da sak’on nan zuwa ga Salahadeen, a lokacin har cikin gidanshi shugaban k’ungiyarsu ya zo tare da Alhaji Kabeer, duk da sun ganshi ba cikin hayyacinshi ba duk ya lalace amma bai hana shugaban yace mishi “Shakoor alamu sun nuna ba zaka cika alk’awarin daka d’auka ba, to fa ka sani zaka tab’e tab’ewar ma ta wulak’anci, sannan zaka mutu ba da jimawa, a k’arshe kuma ‘yarka saita shigo hannunmu.”

Cikin lumsassun idonshi ya kallesu yana murmushi yace “Sarah tana cikin aminci, shed’anu kamarku ba zaku iya tunkararta ba, ni dana siya da kud’ina dai zaku iya kashe ni, amma princess tafi k’arfinku.”

Cikin jin haushi shugaban ya mik’e tare da jefa mishi wani abu a tsafi a fuska, ko shurawa baiyi ba kanshi ya fad’a saman teburin da yake gabanshi hannunshi rik’e da kofin barasa, jini ne ya shiga bulbulowa ta hancin shi da baki. Mik’ewa Kabeer yayi yace “Ka kashe shi fa.”

Kallonshi yayi yace “Babu abinda zai gagare ni a duniyar nan, ‘yarsa zata shigo hannu na kuma saina yankata.”

Ficewa sukayi daga gidan, s茅curit茅 dake k’ofar shiga wajen karatun nashi ganin shiru har lokacin daya kamata ya fito yayi ya wuce bai fito ba yasa shi lek’awa, tashin hankalin daya gani yasa shi fita a guje yana danna abun maganar dake mak’ale a kunnenshi yana sanar da sauran jami’an gidan da babu lafiya, sannana gaggauta bin motar data fita yanzun nan.

Awa d’aya da faruwar abun gidan nan ya zama kamar wani filin daga, jami’an tsaro kala kala kama daga na lafiya dana tsaro, an killace daga falon zuwa cikin d’akin karatun, masu d’aukar hoto nayi masu bincike nayi duk dan son gano me ya haddasa mutuwar tashi. Saida aka kwashe awanni ana ta kai da kawowa kafin aka d’auki gawar aka saka a wata jaka aka fita dashi.

Kaf garin da kewayenshi da sauran k’asashe labarin mutuwar shahararren mai kud’in ya game ko ina, labarai a social media duk maganar ake, musamman da har yanzu babu wani rahoton daya bayyana da cikakken bayanin abinda ya zama ajalin nashi, dan hatta kofin da aka samu hannunshi saida aka killace shi aka yi gwaji na musamman kan kofin da barasar, amma basu samu wani sinadari ciki daya haddasa mishi abun ba.

Da yamma lis ya ga abinda ke faruwa a wayarshi, ya jijjiga ganin lamarin sai lokacin maganganunta suka shiga masa yawo a kwanyar kai, hakan zai iya kasancewa kenan shi ya kashe kansa, duk sai yaji tausayin yarinyar ya baibaye shi, daga inda yake ya ji yana son sanin halin da take ciki. D’azu ma shatin hannu ya gani a fuskarta, yana tsoron ko Farha ce ta mareta amma kuma ta kasa fad’a masa, ana kiran sallah magriba yayi sallah saiya d’auko hanyar zuwa gidan dan kawai ya ga ya take.

Da rana ma bata iya cin abincin ba saboda bayan Mamuh ta idar ta shiga sallah, da gangan Iffa ta d’auki yaji sosai ta zuba a cikin miyar, sannan ta saka loma a bakinta bata had’eta ba ta maidota, ita kanta Mamuh taji yaji amma su sun saba cin abincinsu da yaji, sai dai tayi mamakin ganin bata saka tarugu dayawa ba.

D’aki ta shige tayi kwance kan katifar Mama, sanda Iffa ta shiga d’akin ma saida ta mata sababi ta tashe ta kan katifar wai ko su basa kwantawa bare ita, har zata zauna kan kujera ta daka mata tsawa kamar wata yarinyar ta tace ta zauna k’asa karta goga musu najasa.

Tunda ta zauna k’asa kusan kujerar bata kuma tashi ba daga nan ta rakub’e, duk k’ok’arin Mamuh na son taimaka mata sai ta k’i saboda ta riga data saka tsoronsu a ranta. Haka ta k’yaleta ita ma har yamma tayi ta tafi gidan wasu tsofaffi ne kishiyoyi da take musu bitar karatunsu.

Sanda ta fita Sarah lokacin taji fitsari ya matseta sosai, mik’ewa tayi ta fito daga d’akin, har ta saka takalmi zata wuce taji wata tsawa daga bakin Farha tana fad’in “Ke mahaukaciyar ina ce ina shara zaki mayar dani baya? Malama ko ma inda kika fito ni bana son ganinki.”

D’ago kai Iffa tayi daga karatun da take ta kalleta tace “Me ya fito dake kuma, ki zauna acan mana kafin mu shiga kwana ke saiki fito.”

Rud’ewa tayi cikin tsoro ta shiga cire takalmin ta juya da sauri ta koma d’akin ta zauna, inda ta tashi ta koma ta zauna ta had’a kai da gwiwa tana kuka, ‘yar k’uran data shak’a sanda Farha ke shara ce ta saka ta daddagewa ta feto atshawa, k’arfin atshawar yasa fitsarin da take rik’o gabce mata. Da sauri ta mik’ar da k’afafunta ta shiga matseshi amma ina ya riga daya danno kai, saida ta gama tas kawai ta fashe da kukan tausayin kanta.

Iffa tayi alwalar magriba ta shiga ta d’auko hijab da sallaya, ta juyo zata fito ta ji k’afarta cikin ruwa tsundum, kallon abun tayi sai taga da yar kalar a ciki, sake kallon abun tayi ta kalli tsayinshi daga inda ya taho, hakan yasa kallonta ya dangane da Sarah, tana kallonta taga ita ma ita take kallo da matuk’ar tsoro a fuskarta duk ta sakar mata ido, yamutsa fuska tayi tace “Miye nan?”

Saida ta had’e k’afafunta da kyau tana cumimiye rigarta daga sama wajen k’irji cikin gurbatacciyar hausarta tace “Kiyi hak’uri ki gafarce ni, ban sani bane ya taho min.”

Wani mamaki ne ya kashe Iffa tare da k’ara zaro ido tace “Ya taho miki? Wanene?”

K’uri ta sake mata da ido tana kallonta ba tace komai ba, cikin tsanarta da gaba d’aya zuciyarta ta tunkareta, hannu tasa ta dafe gwiwarta ta turata baya da k’arfin tsiya, ai kuwa sai taga daga nan abun ya fito, kallonta tayi baki bud’e tace “Wai kina nufin fitsari ne kikayi daga nan zaune ko me?”

Mik’ewa tayi tana sake fad’in “Fitsari daga nan zaune? Da girmanki da komai.”

Jefar da sallayar tayi tare da hijab d’in ta fita, Farha ta kalla dake rik’e da buta za tayi alwala tace “Wai kinsan me aljanar can tayi a d’aki?”

Da sauri ta kalleta tace “A’a, me tayi?”

Da k’arfi tana nuna d’akin tace “Fitsari wai, fitsari daga zauna tayi mana a d’aki.”

Zaro ido tayi tace “Fitsari? Da girman nata? Ah wallahi iskanci ne dan taga Mama na sakar mata fuska.”

Bokitin wanka ta d’auka ta zuba ruwa masu yawa, k’ofar d’akin ta aje bokitin ta shiga ciki, shak’o wuyan rigarta tayi da k’arfi ta fito da ita waje, da k’arfi ta cillata k’asa ta fad’i, kafin ta ankara ta juye mata ruwan nan a jikinta baki d’aya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button