NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Saida tayi kamar zata d’auke numfashi ido rintse baki bud’e, hannu tasa ta mayar da gashinta baya tana furzo ruwan bakinta tana kallon Iffa, cikin huci da b’acin rai ta nuna mata d’akin da hannu tace “Wallahi ba zanyi gugar fitsarin k’atuwa kamar ki ba, dan haka ki cire rigar jikinki ki goge mana d’aki tas, idan kin gama ki mana turaren wuta ko maji k’amshi.”

Cikin akasi ta jefa bokitin ba da nufin ya sameta ba, sai kuma rashin sa’a ya fad’a kan fuskar Sarah, a tsakiyar goshinta ya daka wanda hakan ya haddasa fitowar jini daga goshin da kuma hancinta. Ita kanta saida gabanta ya fad’i sanda taga jinin, dan tasan idan ta b’oye marin data mata d’azu yanzu wannan ba zai b’oyu ba.

Cikin fad’uwar gaba ta juya ta shiga d’aki ta d’auko hijabin da sallaya ta fito akan tabarma ta kabbara sallah.

Sarah na zaune bata da niyyar tashi Farha data mik’e zata shiga d’aki tace “Ke baki ji me aka fad’a miki bane?”

Saida ta shiga mata alama da hannu tana fad’in “Rigarki aka ce ki cire ki goge fitsarin da kikayi a d’aki, ko ba kya ji ne ke?”

Mik’ewa tayi a hankali ta wuce d’akin tsamo tsamo da ita sai d’igar ruwa take, tana shiga ta cire rigarta ya rage mata bras kamar wacce ta d’an kamata sosai, duk’awa tayi ta saka rigar ta fara sharewa, wani irin d’aci take ji daga mak’ogwaronta zuwa baki, zuciyarta a karye take kiris kawai take jira ta fashe da kuka.

Ita bata gama gugar ba sai shafar wurin take, a haka Mamuh ta shigo da sallama wanda shigowarta yayi daidai da shigowar Salahadeen kusan kamar a tare suke, shima sallamar yayi wacce tasa gaban Iffa ya shiga dokawa da k’arfi, hanjinta taji sai yamutsawa suke ta fara tausayin kanta ita ma.

Iffar dake zaune tana azkhar ya tambayeta “Ina yarinyar nan take?”

A d’arare ta kalleshi cikin rashin gaskiya tace “Ta..na ci.ki.”

Kai tsaye ya tunkari k’ofar d’akin, yana bud’a labulen ya tsaya turus, me zai gani haka? Gabanshi ne yaji ya fad’i shima saboda yanda yaga fuskarta ta damalmale da wahala k’arara da kuma jini, babu riga a jikinta tana goge goge, ba aikin da take bane yafi damunshi, hasalima a matsayinta na mace zai so ta iya aiyukan gida, jinin dake b’ullowa a goshinta dana hancinta wanda ya d’auki alamar daskarewa.

Da sauri ya k’arasa kusanta yana durk’ushewa, sam bai wani damu da rashin rigarta ba saima tunawa da kalaman Mama wanda yanzun yana kan hanyarshi daya kira saida ta sake jadadda masa yar amanarta. Hannaye biyu yasa ya tallabo fuskarta yana mai zuba mata ido cike da tausayinta da kulawa yace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:07 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               1锔忊儯8锔忊儯

“Sarah meya same ki haka? Me ya faru?”

Dama jira a tanka mata take, bata b’ata lokaci ba wajen sakin rigar ta fad’a jikinshi ta rumgumeshi tana mai fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, cikin matsanancin kuka ta shiga fad’in “Mr. ka taimaka ka kaini wajen Abhi na, na gaji sosai ba zan iya zama anan ba, babu mai sona anan yan uwanka zasu kashe ni, ka kaini wajen Abhi na na rok’eka ka taimaka min, ba zan iya rayuwa daku a gidan nan ba bana son zaman a yanzu, gida nake so na koma wajen Abhi na, shi kad’ai ne ya so ni kuma shi kad’ai zai ci gaba da sona, please mr. please and please i beg u.”

Wani tausayinta ne yaji ya lullub’eshi lokaci d’aya, duk da baya neman kusanci da ita amma saida ya k’amk’ameta shima ya shiga had’ata da jikinshi, dafe k’eyarta yayi ta baya ya d’ora bakinshi cikin kunnenta, wani huci ya dinga sauke mata mai zafi wanda ya saukar mata da wata kasala a gabb’an jikinta, tsit tayi daga kukan saita d’an fara mutsumutsun son k’wacewa saboda wani iri take ji a jikinta. Sam hanata damar k’watar kanta yayi sai ma magana daya shiga mata cikin sanyin murya yana fad’in “I am so sorry Sarah, i am sorry, ki gafarce ni abisa rabaki da mahaifinki da nayi, a halin da ake ciki yanzu ba zan iya mayar dake wajen Abhinki ba.”

Saida ta sake shi daga rumgumewar data masa ba tare daya saketa ba shi tace “Why? Bana son zama nan mr.”

A hankali ya raba jikinshi da nata ya d’ago fuskarta yana kallonta, hanckiciep ya fiddo daga aljihun rigarshi, a hankali ya shiga goge mata jinin daya fara bushewa a hancinta tare dana goshinta, k’asa tayi da idonta duk yau sai taji wata kunyarshi da rashin son had’a ido dashi.

Cikin muryar kulawa yace “Me ya faru dake Sarah? Me aka miki?”

Cikin dubara tasa hannayenta ta rufe k’irjinta kanta na kallon k’asa cike da kunya tace “Fitsari na musu a d’aki.”

Waro ido ya sake yi ya d’orasu kan wurin daya samu tana guga, sai kuma ya kalleta da mamaki yace “Fitsari Sarah, gar…”

Bata bari ya k’arasa ba da sauri ta kalleshi tana fad’in “Ba laifi na bane, na matsu sosai kuma k’anwarka ta hanani fita a d’akin, shine ya kubce min ba tare dana ankara ba, please i am sorry.”

Tallabo fuskarta yayi ya k’ura mata ido, madadin yaji ya k’ara tausayinta sai yaji kawai ta birgeshi, wani basaraken murmushi ne ya saki, hakan ita kuma yasa ta jin kunya ta sunne kanta k’asa, shima sunkuyar da kanshi yayi ya had’a goshinta da nashi wuri d’aya, kallon fuskarta yake amma ita ta k’i yarda su had’a ido.

Cikin tattausan murya yace “Kiyi hak’uri kinji, ba zasu sake miki iskanci ba.”

Da k’yar ta bud’a ido ta kalleshi tace “Gaskiya ni ka d’aukeni daga nan, basa so na ko kad’an, ni kuma ina jin tsoronsu.”

Saida ya shafo kumatunta kafin ya mik’e tsaye, dafe k’ugu yayi ya k’walla kiran sunan Iffa, duk da ta sallame sallah amma sai tayi gum kamar bata ji ba inda fad’uwar gabanta ya nunku, saida ya k’ara kira na biyu ta iya amsawa da “Na’am.”

Mik’ewatayi ta fara takowa jikinta duk a sanyaye, bud’a labulen tayi tare da sallama ta shigo, sunkuyar da kai tayi ganin kallon da yake binta da shi, cikin dakakkiyar muryar da babu wasa a cikinya yace “Shigo tsaya nan.”

A hankali ta k’arasa inda ya nuna mata ta tsaya kanta k’asa, tana kallo ya sunkuya ya kamo hannun Sarah ya mik’ar da ita tsaye, kallon Sarah yayi ya kalleta yace “Mareta.”

A tare suka kalleshi duka da mamaki a fuskarsu, rik’o hannunshi tayi tana satar kallon Iffa, murya k’asa k’asa tace “Ba zan iya ba mr., i forgive her.”

Kallon Iffa yayi yace “Ai kinji me tace ko?”

A hankali cikin rashin ta d’aga kai ta kalleshi ta d’aga kai alamar eh, jinjina kai yayi yace “Da kyau.”

Saida ya ware iya k’arfinshi ya kasheta da wani mahaukacin mari, wata ihu ta saki tare da saka hannu biyu ta dafe kunci, da sauri Sarah ta shiga gabanshi tana bashi hak’uri, matsar da ita yayi gefe yana kallon Iffa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button