NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Juyawa tayi ta kalleta ita ma sai taga har yanzu hannunta akan kumci, da sauri ta matsa kusanta ta shiga k’ok’arin b’anb’are hannayenta tana fad’in “Yi hak’uri sister, bani nace ya mare ki ba, kiyi hak’uri ki yafe min.”

Cikin jin haushi ta fizge hannayenta daga rik’on da take mata, hakan yasa ta kula da hawayen da take fuskarta har tayi wata iri alamar ta maru sosai. Cike da tausayi ta sake rirrik’eta tana son saita d’ago da fuskarta tana fad’in “Bari na gani baki ji ciwo ba.”

Tsabar bak’in hali Iffa ta tureta da k’arfi cikin jin haushi, baya baya tayi da k’arfi ta kaiwa Salahadeen karo dake bayanta, da sauri ya zura hannunshi ya sakayo ta cikinta ya had’ata da jikinshi, kallon Iffa yayi zaiyi magana sai gani yayi ta kalleshi da harare harare ta murgud’a baki ta fita a d’akin rai b’ace.

Sakin Sarah yayi zai bi bayanta ta rik’e rigarshi tana fad’in “Please mr. rabu da ita.”

Bai kulata ba saida ya fita inda tabi bayanshi, Iffa na tsaye k’ofar d’akin Farha da ita ma ta fito ta idar da sallah kenan, saida ya kallesu yace “A gani na a gidan nan ko kare na d’aure za’a kula dashi, ba wai dan kimarshi ta kai ba sai dan ni ne na kawo shi, amma mutum, mutum mai daraja kuke wulak’antawa saboda kun raina ni, to ba damuwa kuji ni da kyau, Sarah dai ni ne na kawota gidan nan kuma daga yau ni ne zan kula da kayata, hakk’ina wannan, kar kuga nayi banza da aurenta da ke kaina, nayi hakane saboda dole zamu rabu da ita, amma daga yanzu har sanda zamu rabun zan kula da duk wani hakk’inta dake kaina.”

Ko da ya fad’a ya juya ga Sarah dake kallonshi, mafi aksarin kalamanshi taji me yace sai dai ma’anarsu kam bata fahimta ba, wasu kuma ta gane me suke nufi, hannunta ya kama suka koma d’akin.

Da kallo ta bisu har suka shige ciki, k’afafunta ne taji sun kasa d’aukarta, hawaye ne taji sun fara bin fuskarta kamar da bakin k’warya, da k’yar ta d’aga k’afarta data mata nauyi ta koma cikin d’akin, kan gado ta zauna ta fashe da kuka, a gaskiya ba zata iya wannan abun ba, ba zata iya jurar wannan wulak’ancin ba, kawai mama ta dawo ta fad’awa kowa matsayinsa a gidan nan, amma inba haka ba zata bar masa gidan sa.

Suna shiga ya saki hannunta yace “Canza kayanki na kaiki asibiti.”

Wucewa tayi kamar yanda ya umarceta, kayan ta cire ta canza da wata doguwar riga bak’a, takalmi ta saka dogaye ta saki gashinta gaba d’aya kan gadon bayanta, fitowa tayi a hankali wanda fitowarta yasa hankalinshi komawa kanta.

Tun daga k’asa ya kalleta har zuwa sama kafin ya dire kan fuskarta, tayi kyau sosai duk da babu komai a fuskarta, da sauri ya juya ya fita saboda wani marairaicewa da tayi zatayi magana. Bin bayanshi tayi ta fita suna kallonsu sai dai babu wanda yace wani abu, ko da suka fita ya shiga motar ta Kasim daya taho da ita, zagayawa tayi ita ma ta shiga, tayarwa yayi lokacin da ita kuma take d’aura belt d’in, kallonta yayi ya tab’e baki ya ja suka wuce.

Wata k’aramar asibiti ce kuma sabuwa da ba’a jima da bud’ata ba, wanda mamallakin asibitin ya kasance abokinsa ne sosai, tun a hanya daya kirashi ya fad’a mishi yana asibitin yasa shi kaita can, daga waje baiyi kama da asibiti ba saima wani matashin gida mai birgewa, suna shiga ciki suka same shi tare da wata ma’aikaciyar zaune suna hira, zaune sukayi kan kujerun dake fuskantar juna inda Salahadeen ke gaisawa dasu.

Nuna mishi ita yayi tare da fad’in “Gata nan duba min ita.”

Da murmushi ya kalleta ya kuma kalleshi yace “Amma a garin yaya taji ciwo haka?”

Saida ya kalli fuskarta babu alamar wasa a tare dashi yace “Wajen k’iriniya.”

Kallonshi yayi yana nunawa likitar dake kusanshi alamar ta dubata tare da tsaki yace “Karka raina min wayo mana, k’aramar yarinya ce ita?”

Fuska a d’aure ya kalleshi yace “Nine na fad’i k’arya kenan?”

Ruwan wanke ciwo ta fara sakawa a kad’a ta wanke mata, ruwan alcohol ta saka a kad’a ta d’an shafa mata, da wata irin zabura ta rik’e hannunta gam tana kallonta bayan ta furta “Aouch.”

Murmushi ta mata tace “Pardon.”

Jaye hannunta tayi tare da sake kaishi zata d’ora, zunbur ta mik’e tsaye tana kallonta tana rarraba ido, kallonta Salahadeen yayi yace “Zauna a k’arasa miki.”

Turo baki tayi tace “Mr. da zafi fa.”

Fuska a had’e yace “To daman da sanyi ne? Dad’i kike so kiji?”

Cikin shagwab’a tace “To ai baya min ciwo, kawai mu koma gida na hak’ura.”

Dr. d’in ne ya kalleshi yace “Haka ake lallab’a ne?” Tsaki yayi ya kalleta yace “Madame kiyi hak’uri kinji, zauna ai yanzu za’a k’arasa miki kad’an ya rage.”

Wani kallo ya watsa mishi yace “Madame?”

Tab’e baki yayi ya d’auke kanshi, matsawa likitar tayi Sarah ta sake ja baya, a hassale ya kalleta yace “Malama in zaki tsaya ki tsaya mana, zan tabbata anan ina jiranki ne? Kinga yer uwa dan Allah ki tausheta ki k’arasa mata.”

Jin yace ya tausheta saita zuba a guje ta shige d’akin dake bayanta, gado biyu ne a ciki d’ayan babu kowa sai d’ayan da wata tsohuwa da k’arin ruwa. Ganin haka yasa Dr. d’in kallonshi yace “Taimaka ka rik’eta mana, idan ba’a wanke mata ciwon ba zai iya mata miki a gaba, kuma kaga abu ga jar baturiya.”

Wata harara ya daddala masa yana fad’in “Kai ka rik’eta mana, yarinya ce bata san wahala ba sai dad’i, ni ina zan iya da wannan fitinar.”

Mik’ewa yayi ya nufi d’akin yana fad’in “Shikenan bari na rik’eta da kaina, amma dai kasan taka ce ko.”

Da kallo ya bishi yana mamakin kalmar taka ce daya fad’a, yana daga nan zaune yaji Sarah na ihu tana fad’in “Na rantse muku bana so, nifa ban tab’a jin irin wannan ba, inda Abhi na ne lallab’a ni zaiyi yana shafa kaina yana min magana mai dad’i, na rok’eku ku k’yaleni bana so.”

Baisan sanda ya mik’e ba ya shiga d’akin da sauri, can k’asan gado ya hangota likitar na tsaye suna kallonta suna dariya, likitar ce tace “Dr. kawai mu k’yaleta tunda bata so.”

Juyowa yayi yana fad’in “Dole mana, wannan na so naga yanda za’a mata allura.”

Dariya tayi tana fad’in “Lallai kam, a hakan fa dan bata tsinin bakin allura ba.”

Juyowar da sukayi suka ga Salahadeen ne yasa suka tsaya, da hannu ya musu alamar su tsaya tare da durk’usawa ya lek’a k’asan gadon, wata dariya ce yaji ta taho mishi daya ganta kwance k’asan gadon. Girgiza kai yayi tare da zura mata hannu yace “Come.”

Mak’ale kafad’a tayi hakan yasa ya sake cewa “Please.”

Cikin muryar shagwab’a tace “Ba zaka saka su min ba?”

Girgiza kai yayi tare da fad’in “Ba zan saka ba.”

A hankali tace “Kayi alk’awari?”

Cikin sakin murmushi yace “Je te promis.”

Hannunta ta d’ora kan nashi ta fito daga durk’ushe, saida ta fito ta mik’e tsaye tare dashi tana kakkab’e rigarta data sha k’ura.

Kallonta yayi yana murmushi yace “Look at u.”

Kallon kanta ta sake yi tare da turo baki, zaunar da ita yayi kan gadon tare da juyawa ya kalli likitar, tana matsowa ta yunk’ura zata sauka ya rik’eta, rik’e hannayenta yayi yana kallon fuskarta yace ” Princess.”

Da sauri ta sake soka idanunta cikin nashi tana kallo, Allah sarki tayi kewar sunan nan daga bakin mahaifinta, a take yanayinta ya nuna ya fama mata wani abu a zuciyarta. Yanda ta kafeshi da ido ya bashi damar d’orawa da “Ke fa babbar yarinya ce kuma mace, mata kuma an san su da juriyar zafin kowane rad’ad’i, kuka jure rad’ad’in zafin ciwon da kuke ji sanda zaku kawomu duniya ma bare d’an wannan.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button