NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

D’an juyawa yayi ya kalli likitar ya mata alama da ido, matsowa tayi amma sai Sarah ta k’i kallonta ma bare hankalinta ya tashi, ganin haka saiya ci gaba da cewa “Duk da ke baki san wannan rad’ad’in ba, amma a ganina rad’ad’in zafin neman kud’i ma da kike da shi ai yafi wannan, ko ba haka ba ma business girl?”

Wani irin murmushi ne ta saki tare da rintse ido d’aya saboda zafin alcol d’in daya ratsa goshinta, amma saita daure bata nuna ba tana ci gaba da kallonshi tana murmushi, har aka rufe mata ciwon bata kula ba, yana ganin an gama ya mik’e yana hararenta sama da k’asa da fad’in “Sai kin bawa mutane wahala.”

Wani kallon shagwab’a ta bishi da shi inda Dr. d’in yace “Allah in ban zugata tayi zaune saika d’auketa ba kace d’an iska ne ni.”

Saida ya kalleshi sama da k’asa yace “To ka zugatan mana kaga me zai faru.”

Da dariya yace “Me zai faru?”

Ficewa kawai yayi a d’akin ya barsu, sauka tayi daga kan gadon ta bi bayansu ita ma, suna zuwa sallama sukayi suka bar asibitin, a hanyarsu ta komawa gida ta kalleshi tace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:08 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               1锔忊儯9锔忊儯

“Mr., yaushe zaka kaini wajen Abhi?”

Ba tare daya kalleta ba yace “Ba lokaci.”

Cikin zak’uwa tace “To ka d’ora ni a hanyar da zan kai kaina mana.”

“Ba zai yiwu ba.” Ya fad’a a tak’aice, saida ta d’auke kanta daga kallonshi tace “To ka kaini wajen da Mamie take.”

“Shima ba zai yiwu ba.” Ya sake fad’a a tak’aice, cikin jin haushi tace “To ka kashe ni mana, wai me yasa baka da tausayi ne? Me yasa ba zaka fahimci bana son zama anan ba tare daku, me ya shafeka da matsalata ne? Ka kaini wajen Abhi na kawai.”

Birki ya taka haka yasa ta kalleshi da sauri, kallonta yayi yace “Ai dai kina so ki koma ko? To ki bari Mama ta dawo zaki koma, nima na gaji da caza min kai da kike, ba zan iya da jarabarki ba ko kad’an.”

Cikin nuna kanta tace “Ni ce ma jarabar a wurinka? Amma ai kai ka d’aukoni ba ni nace ka d’aukoni ba, ka mayar dani idan kayi zuciya mana.”

Nuna mata titi yayi yace “Ki wuce mana ga hanya nan, idan kin shirya rasa kanki kije mana.”

Cikin hararenshi tace “Amma ai kasan da dukiyata a gidanku ko?”

Cikin kallon idonta shima yace “Sa kije ki d’auka mana.”

Saida ta rumgume hannaye tace “Ka kaini to ni kuma zan bar muku gidanku.”

D’ora hannushi yayi kan mabud’in k’ofar ya rik’e baki yana kallon titi, ganin baiyi niyyar tafiya ba yasa ta bud’e k’ofar ta fita, saida ta lek’o ta kalleshi cikin d’aga murya tace “Monster.”

Rufe k’ofar tayi da k’arfi ta wuce, daga nan zaune ya bi bayanta da kallo, sauri take sosai duk da dogayen takalmi ne a k’afarta amma tsaf take tafiyar, kasa d’auke idonshi yayi har ya ga ta karya wata kwana ta shiga. Wani tsaki yayi tare da tashin motar ya bi bayanta, kwanar ya shiga saiya ganta cikin wasu yara da suke wasa a k’ofar gida.

Tsayawa yayi daga nesa yana kallonta, kallon yaran take tana tafa musu kan wak’en da suke cikin nishad’i, ya jima yana kallonta amma ita hankalinta na kan yaran, tayar da motar yayi a hankali ya k’arasa wajen, tana ganinshi ta b’ata rai ta wuce da sauri, cikin tafiya a hankali ya bi bayanta, oda ya dinga mata amma da taji haushi saita juyo tana fad’in “Ka rabu dani mana, ba zan bika ba.”

Saida ya furzar da iska na b’acin rai ya tsayar da motar ya fito ya bi bayanta, da sauri ya cabko damatsenta ya fincikota da k’arfi ya danna a motar, yana shiga ya figi motar rai a b’ace suka nufi gida.

Suna tsayawa k’ofar gidan ta kalleshi tace “Ina so nayi magana da Abhi na a waya.”

Cikin jin haushi yace “Abhi, Abhi, Abhi, wai ke baki da wata magana ne sai ta Abhi?”

Da k’arfi tace “Yeah, saboda mahaifina ne, ina son yin magana dashi ina so naji ya yake.”

Bata ankara taji ya jefo mata wayarshi a jiki ta daketa a k’irji a daidai poitrine d’inta, da sauri ta dafe nononta ta rintse ido, a hankali ta bud’e ta kalleshi tace “Miye haka? Baka gani ne?”

Sai lokacin ya kalleta ya kuma d’auke kanshi ya basar, cikin jin haushi tace “Malam bani hak’uri mana, a nono fa ka jefe ni.”

Ba tare daya kalleta ba ya lumshe ido, ganin baida niyya yasa ta d’aukar wayar ita ma ta jefa mishi a k’irji, da sauri ya dafe k’irji yana kallonta da d’an banzan mamaki, d’aukar wayar yayi ya saka aljihu ya fita daga motar. Da sauri ita ma ta fita har tana ha’dawa da gudu tana fad’in “Ka bani wayar to, mr…”

Kai tsaye d’akin Farha ya wuce ranshi a b’ace, har zata bi bayanshi sai kuma ta tsaya tana lura da kallon da su Iffa ke jifarta dashi, tsaye tayi tana kallon d’akin kamar ta bishi kuma mai d’akin ta mik’e ta bi bayanshi.

Farha na shiga ya fito rik’e da wasu takardu cikin sauri, ta gabanta ya wuce zai fita ta juya tana tattare doguwar rigarta ta bishi, har zai shiga mota ta rik’e hannunshi tace “Please mr..”

A hassale ya juyo ya kalleta yace “What?”

Cikin turo baki tace “Ka bani wayar to zan kira Abhi, sorry.”

Cikin d’aga murya da jin haushi ya fizge hannunshi yana fad’in “Abhinki ya mutu, ba zaki sake jin muryarshi, ki rabu dani da maganarsa kinji, zan mayar dake can ki gani da idonki.”

Tunda ya fara magana ta saki gaba d’aya jikinta ta k’urawa fuskarshi ido tana son gano ma’anar kalamanshi, ya juya zai shiga motar ta d’aga labb’ata da k’yar tace “Abhi…ya mutu kace?”

Juyowa yayi da niyyar tabbatar mata sai kuma ta tafi luuuu zata fad’i, da k’arfin hali yayi azamar rik’ota ta fad’a jikinshi, da sauri ya k’arasa d’aukarta ya shigo cikin gidan da ita, yanda ya d’auketa kamar bai d’auki mutum ba saboda rashin nauyi, akan tabarmar dasu Iffa ke zaune ya direta yana kallon Mamuh yace “Kawo ruwa.”

Da sauri ta mik’e ta kawo ruwa lokacin Farha ta fito, ga hannu ya zuba ruwan ya shafa mata a fuska, wani numfashi ta sauke da k’arfi tare da rik’o hannun Mamuh dake kan kafad’arta ta rik’e gam, tana kallon sararin samaniya ta ga hasken farin wata da taurari sai tayi saurin mik’ewa zaune a zabure. Ko da yaga haka ya mik’e ya kalli Mamuh yace “Bata abinci ta ci.”

Yana fad’a ya fice a gidan gaba d’aya, da kallo ta bishi saita rasa abin fad’a ko abun yi, tashi Mamuh tayi dan kawo mata abincin sai ita ma ta mik’e ta shiga d’aki, k’uryar d’akin mama ta shige ta kwanta kan gadonta mai rufa dake cikin shinfid’a ta alfarma tayi luf a ciki.

Lokacin ne ta fara kuka kan tuna wai Abhi ya mutu, ya mutu? Kamar ya ya mutu? Anya kuwa ba shiri ne na mutumin nan take tafiya akan shi ba? Anya kuwa komai dake faruwa ba shiryashi ne yake yi ba? Watak’ila ita ma fa kasheta zaiyi idan lokaci yayi, cike da damuwa ta shiga murza fuskarta tana nadamar k’in amincewa da mahaifinta da tayi sanda ya zo tafiya da ita, sam ta k’i tsayawa ta saurareshi ta zab’i zama anan, watak’ila da taji gaskiyar komai da yake son fad’a mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button