NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Suna cikin tattaunawar Sarah ta shigo ta kwanta ta d’ora kanta a saman cinyar mama data mik’e k’afafu, murmushi Mustafa yayi ya kalli Salahadeen yace “Amaryar yaya fa ta zama autar Mama.”

Da sauri ya kalleshi fuska kicin kicin yace “…

Alhamdulillah

Na cika alk’awari
13/04/2021 脿 04:13 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               2锔忊儯3锔忊儯

“Wacece amaryar?”

Rufe bakinshi yayi alamar yayi shiru, k’wafa yayi ya mayar da kanshi ga kallon Mama dake kallonsu, a hankali tace “Naje na samu kawunku da maganar go…”

Da sauri yace “Mama dakata.” Kallon Sarah yayi da ita har bacci ya fara ridarta yace “Malama zaki iya tashi daga nan sirri muke.”

Ba tare data tashi ba ta d’ago idonta ta kalleshi, lumshe ido tayi ta turo baki gaba tare da yin hamma, hannu tasa ta sake k’amk’ame cinyar Mama kawai ta fita batunshi, murmushi Mama tayi kai hannunta ta rik’o hannun Sarah, da sauri ta jaye hannun tare da fad’in “Ashhhh.” Saboda yatsanta data rik’o mai ciwo, cikin kulawa Mama tace “Ciwo kika ji?”

Cikin french tace “Eh mamie, aiki nayi d’azu.”

Mama ce tace “Wane irin aiki kuma?” Kai bacci da Sarah ke ji yasa taji amma tayi shiru, ci gaba tayi da shafa kanta tana kallonsu Salahadeen ta fad’a mishi yanda sukayi, daga bisani kuma ta tabbatar musu zasu tafi k’auye.

Cikin damuwa Iffa tace “Mama to idan muka tafi kinga fa ranar asabar hadda muke, ga hadda da zata hau kanmu kuma ga laifin rashin zuwa, abun zai mana yawa gaskiya.”

Cikin gasgatawa tace “Gaskiyarki kuma, to ko zaku iya tafiya gobe ko jibi?”

Da sauri Salahadeen yace “Ni kuma ina so na raka wannan ta koma inda ta fito zuwa goben.”

A dame mama ta kalleshi tace “Ka barta har jibi mana, kawai goben ku shirya sai ku tafi, idan ka dawo saika rakata ta koma tunda dai naga kamar a saman kanka take zaune.”

Shiru yayi baice komai ba, sai zuwa can kuma ya mik’e tsaye yana fad’in “Saina dawo.”

Fita yayi inda suka d’an tab’a hira sama sama, har saida dare yayi duk lokacin baccinsu yayi Mama na zaune tana shafar kan Sarah, hatta gyangyad’i ma ta nema ta rasa saboda tunanin rayuwar da Sarah zata tsinci kanta a cikinta, tausayawa yarinyar take sosai da sosai, tana ganin k’ok’arinta akan komai saboda ba abu mai sauk’i bane ka karb’i abinda baka saba dashi ba lokaci d’aya.

A hankali kuma bacci ya fara awon gaba da Mama daga zaune ita ma, sunyi nisa sosai a bacci hankali kwance, a baccinta ta dinga mugayen mafarkai akan Abhinta, abinda yafi d’aga hankalinta shine yanda yanda ta samu kanta cikin tarkon wasu mutane masu shiga ta ban tsoro, duk k’ok’arinta na gudun tsere musu saida suka cimmata, ba tsayawa suka d’ora bindiga akanta, ta had’e hannaye zata fara rok’onsu kawai taji sun tayar da bindigar a kanta. Wannan k’arar tasa ta firgita ta farka a matuk’ar razane tana sakin ihu tun k’arfinta.

Ya fito daga ban d’aki kenan daga wanka zai shiga d’aki yaji ihun, da gudu ya taho kamar an kirashi, saida ya shigo d’akin kuma ganin Mama ma ta farka a tsorace tana rirrik’eta saiya tambayi kanshi me ya shigo dashi ma? Miye ya razani haka? Da k’yar Mama tayi nasarar rik’eta ta rumgumeta sosai a jikinta tana fad’in “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, hasbunallah wani’imal wakil, a’uzu billahi mina shaid’anin rajim.”

Cikin kuka da rud’ewa take fad’in “Mamie kashe ni sukayi, kashen ni sukayi, zasu kashe ni Mamie, ki taimake ni karki barni na rok’eki.”

Sake matseta tayi sosai tace “Karki damu kinji Saratu, babu abinda zai same ki, ba zasu kasheki ba tunda baa hannunsu rayuwarki take ba.”

A hankali ya matso ya tsugunna gabansu yana kallonsu, d’an hararan iska yayi dan kawai sai yaji ya tsargu da yanda zuciyarshi ke zak’ewa sosai akan lamuranta da kuma yanda take tsananta tausayinta. Kallonshi Mama tayi tace “Yarinyar nan zata wahala ita kad’ai Salahadeen, tana cikin had’ari fa.”

Sarah kawai ya kalla bai ce komai ba, a hankali ta dinga samun nutsuwa tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ta d’ago ta kallon Mama cikin muryar sanyi sosai tace “Nagode Mamie, kina sona sosai, kin zama kamar mahaifiyata, lokacin dana rasa mamana mai san dad’in soyayya ba, ba dan hotonta ba da ban gama gane fuskarta ba, amma yanzu dana same ki sai naji kamar mahaifiyata ce ta dawo duniya, ina zata dawo ta rayu dani.”

Kallon Salahadeentayi tace “Kunyi sa’ar mahaifiya kamar Mamie, da zan iya zama a gidan nan saboda ita zan zauna, amma ina so na koma mahaifata na fuskanci k’alubalen dake gabana, idan zan mutu ne to ina so na mutu acan.”

Mik’ewa tayi tsaye ta fita daga d’akin, can kusa da k’ofar fita taje ta zauna k’asa, had’a kai tayi da gwiwa kawai ta fashe da kuka, tabbas daga zuciyarta yake dan a hankali take tariyar abubuwan da suke faruwa da ita. Tare suka fito da Mama har zasu tunkareta sai kuma Mama ta tsaya tace “Je dan Allah ka rarrasheta tayi hak’uri.”

Baice k’ala ba dai ya wuce wajenta, yana zuwa ya sake tsugunnawa yace “Miye kuma yanzu?”

Bata kulashi ba sai kukanta daya fara jinshi kamar tana watsa mishi tafasashen ruwa, har k’asan zuciyarshi yake jin rashin dad’in kukan nata, da zai iya kamar ya d’an jawota a jikinshi ya tambayeta matsalarta, wasu bak’ak’en yawu ya had’e da yaji sun mishi d’aci yace “Sarah me yasa kike so ki tafi inda baki da kowa?”

A hankali ta tsaya da kukanta ta d’ago tana kallonshi, kawar da idonshi yayi daga kallonta, cikin muryar kuka tace “Ko bana da dangi acan ina da abokai, anan kuma wa nake da? Ban san kowa ba.”

Saida ya sauke ajiyar zuciya yace “Kina da mu Sarah, Mama, yan uwana duka naki ne.”

Wani kallo ta mishi tare da girgiza kai tace “A’a, duk gidan nan Mamie kad’ai ke so na, amma ko kai daka kawo ni nan baka k’aunata, ka tsane ni baka son gani na, shiyasa na bar muku gidanku.”

Kallonta yayi sosai, shi dai sam baiji dad’in abinda ta fad’a ba, cikin kafeta da ido yace “Waya fad’a miki ba ma sonki? Ni na fad’a miki hakane da bakina?”

Da sauri tace “Amma ai aikinka ya nuna haka, tunda muka zo ka tab’a tambayata ya nake ya na wuni? Na ci ko ban ci ba? Yanayin da nake ciki ya min ko yana karb’ar jikina? Abinda nake ci yana son cikina ko ya lalata min ciko? Me kike so miye ba kya so? Duk ka tambaye ni wannan? Ko sau d’aya baka tab’a ba sai dai ma idan ina maka magana ka dinga jin haushina kana min tsawa.”

A hankali ya dafe goshinshi da hannu, baida hayaniya a rayuwa kuma baya son hayaniya, doguwar maganar nan da tayi sai yaji ta hau mishi kai, sai dai asalin dalilin da yasa yaji ta hau kanshi bai sani ba kam, saboda kalaman nata basu mishi dad’i ne ko kua dan baida jurar jin doguwar magana? A hankali ya sauke hannun ya kalleta cikin sassauta murya yace “Kiyi hak’uri, ba rashin so yasa nake miki haka ba, idan kin fahimta ni ba cika son magana bane kawai.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button