SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Turo baki tayi gaba tace “Kuma na fahimci babu ruwanka da damuwata ma.”
Girgiza kai yayi alamar A’a ba haka bane, cikin kalar tausayi tace “Hakane mana, kai daka fi kowa sani baka tab’a zaunawa kaji me nake ji a game da matsalata, kasan me yasa na zama marar damuwa da damuwata nima?”
Da ido kawai ya mata alamar a’a, d’orawa tayi da “Sanda na shigo gidan nan naji ni kamar kurkuku ne aka kawo ni, ban tab’a rayuwa a irin wurin nan da yanayin nan ba, na so na tashi hankalinka kan ka mayar dani, na so na k’i saka komai a bakina saboda ban san abincinku ba, amma daga yanda kowa ya fara kallona saina sha jinin jikina, wasu suna min kallon mamaki wasu kuma na tsana da k’yama, bana jin dad’in komai sai dai dole nake hak’ura nayi anfani da abinda na samu, kai kafi fahimtar yarena sama da kowa, amma baka son magana dani sai dai ka hantare ni, sai kawai na rumgumi k’addara ina cin duk abinda aka bani.”
Iska ya furzar yace “Sarah dare yayi yanzu, kije ki kwanta da safe zamuyi magana.”
Girgiza kai tayi tace “Ni anan zan kwana.”
Mik’ewa yayi yana kallonta cikin rarrashi yace “Kije ki kwanta da safe na miki alk’awarin kai ki k’auye ki ga gona, kina so ai?”
Murmushi ne ya sub’uce mata ta mik’e tsaye tana kallonshi tace “Ina so, da gaske zaka kaini?”
Jinjina mata kai yayi alamar eh, yanayinta ne ya canza tace “Amma kuma Abhi na, ina so naga gawarshi na k’arshe…”
Duk da ta kai k’arshe saida ta sako da kuka, lumshe ido yayi a ranshi yace “Ya Allah.”
K’ura mata ido yayi yana kallo kawai, ganin ya k’i ce mata komai saita ruga da gudu ta shige d’aki tana fashewa da wani kukan, tana shiga Mama har bacci ya d’auketa, uwar d’aki ta shiga ta kwanta kan gadon tana kuka, abubuwa dayawa ta dinga tunawa a game da mahaifinta wanda suka dinga saka ta kuka. Ba zata samu wanda zai sota kamar shi ba, ya jure k’uruciyarta da wautarta, yayi hak’urin shagwab’arta da sangartarta, ya nuna mata soyayyar uwa goma da uba goma, bata tab’a kallon abu da idon sha’awa ba ya kasa yi mata shi, harara ko tsawa ko tsaki bare kyara babu wanda ya tab’a mata. Sai dai duk da haka ya d’ora akan k’yamar yawan gidajen rawa da shan giya, ko sigari wannan saida ya horeta sosai ya nuna mata rashin dacewarta, a haka ta k’arar da daren nan ba tare data rintsa ba sai kuka daga zuciyarta.
Kamar wasa kuma ko da safiya tayi yace ai tafiya zasuyi kowa ya shirya, babu wanda ya damu musamman da yace yaje ya karb’o motar Kaseem kafin ya dawo kowa ya shirya, tsaf kowa ya shirya har da Farha da kuma mazan suka zauna jiranshi, bai jima sosai ba ya dawo ya same su, har sun d’auki hanyar fita ya juyo ya tsaya yana kallon mama dake ta Allah ya kiyaye hanya yace “Banga Sarah ba? Tana ina?”
“Bacci take har yanzu, ina jin tana ta sauke ajiyar zuciya da alama kuka tasha, kuje idan ta tashi zan fad’a mata kun tafi.”
Gyara tsayuwa yayi ya had’e fuskarsa sosai yanda babu wanda zai masa kallon tuhuma yace “Zamu jirata a mota ta tashi tare zamu tafi.”
Duk zuba musu ido sukayi inda ya juya zai fita Mama tayi saurin cewa “Salahadeen.”
Juyowa yayi ya dawo ya tsaya kusanta, kallonsu tayi ganin sunyi cirko cirko tace “Ku tafi gashi nan zuwa.”
Farha ce ta rigasu fita kafin suka bi bayanta, saida ta ga fitarsu ta kalleshi tace “Ban gane da ita zaku tafi ba? K’auyen?”
A tak’aice ya amsa da “Eh mama.”
Cikin girgiza kai tace “A’a ban yarda ba, k’auyen nan basu santa ba kuma ka san su da abun magana baya k’aramta a wajensu, ace ina muka samu k’abila kuma sai ka ce me?”
Ba tare daya kalli Mama ba yace “Alk’awari na mata zan kaita k’auye.”
Cikin tuhuma tace “Idan suka ce wacece ka ce me?”
A hankali ya kalleta yace “Kin yarda dani Mama?” Cikin tabbatarwa ta jinjina kai tace “Eh, nasan ba zaka ja min magana ba.”
Kallon fuskarta kawai yayi kallon dake nuna a tashe mu tafi to, juyawa yayi ya fita ita ma ta shiga d’aki, da k’yar ta tasheta saboda baccin dake idonta, da k’yar Mama ta fahimtar da ita suna jiranta amma hakan baisa tayi sauri ba, har saida mama ta tayata wajen saka riga da zanin data bata cikin kayan Mamuh, bak’in hijabi ta bata ta saka dogo sosai mai hannaye dai kamar kullum, tsaf tayi ka rantse balarabiya ce idan ba magana tayi ba. Har ta bata kwalli ta saka tace ba zata iya ba sai ja girar Iffa ta bata ta saka a idon, jan bakin data gani ja ta d’auka ta shafa, ita kanta Mama sai taga ta birgeta kamar ta had’iyeta, murmushi ta mata tace “To yi sauri kafin su gaji da jiranki.”
Sumbatar kumatun Mama tayi tace “Muahhh, sai mun dawo.”
Hannu ta shiga d’aga mata har ta fita, tana dosowa ya d’aga idonshi ya sauke kanta, tsaye yake dama a b’angarenshi yana danna waya, su kuma duk sun shiga amma basu rufe k’ofar ba. Yayi iya k’ok’arinshi wajen ganin ya d’auke idonshi amma ya kasa, d’an d’agowa yayi daga jinginar da yayi amma bai kawar da idonshi ba, baisan daya zai kwatanta kyan data mishi ba, un yace bata birge shi ba bai kuma ji wani abu ya tsirga masa ba to hak’ik’a k’arya ya fad’a.
Saida ta zo daf dashi tana ta sakin murmushinta tace “Na shirya, zamu iya tafiya?”
Rufe idonshi yayi da k’arfi dan ya lura suna son ja mishi magana, juyawa kawai yayi tare da bud’e idonshi ya shiga mazauninshi ya zauna ya rufe.
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:13 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA GA
_DUK_
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
Talla
*Talla*
*Talla*
Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
2锔忊儯4锔忊儯
Tsaye tayi inda Iffa ke zaune da nufin ta matsa mata ta zauna, amma Iffa saita d’auke kai tana jin haushi na ganin duk abinda ta saka saiya mata kyau, ganin bata da niyyar gyarawa Salahadeen kuma ya juyo yasa Mamuh saurin bi takan Iffa ta fito daga motar, gaba ta koma inda Farha ke zaune abisa umarnin Salahadeen d’in, matsa mata tayi suka zauna a matse, fitowa Iffa tayi nufinta Sarah ta fara shiga sannan ta shiga ita. Gyara madubin dake kallon tsakiyar motar yayi ya saitashi kan fuskar Iffa, cikin sigar gargad’i yace “Wallahi Iffa idan ba so kike kiga jini a fuskarki ba ki kiyayi b’ata min rai a safiyar nan, inba iskanci da raina mutane ba ke ba yan uwanki bane da ba zaki wuce kusa dasu ba?”
Cikin turo baki ta matsa ranta a b’ace tana hararan Sarah data shiga ta zauna ta rufe, cikin sakin murmushinta ta kalli su Zeid tace “Ina kwana.”
Amsa mata sukayi da “Antashi lafiya.”
Wata harara Iffa ta sake wurga mata daidai nan Salahadeen yaja motar suka tafi, ba tare daya d’auke idonshi daga kan hanya ba yace “Kin karya ne?”