SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Wacce ta fitan ce ta dawo ta sanar dasu ta fad’a musu sunce zuwa zasu k’arasa wani aiki kad’an, hakan yasa suka tashi suka ce zasu kewaya sauran gidajen su dawo, har ta mik’e tare dasu ya kalleta yace “Ki zauna ki jiramu yanzu zamu dawo.”
Da mamaki ta kalleshi ta kalli fad’in gidan tace “Anan d’in? Ni kad’ai?”
D’aga mata kai yayi alamar eh, girgiza kai tayi tace “Ba zan iya ba, kowa fa kallona yake.”
Cikin had’e fuska yace “Ba komai ki zauna, zaki gaji idan kika taho tare damu, ba zamu jima ba yanzu zamu dawo.”
Cikin damuwa tace “Amma ni da na…”
Cikin gajiya da zancen yace “Ki zauna nace.”
Tiro baki tayi gaba ta koma ta zauna kan kujerar rai a b’ace, juyawa yayi ya fita dan baya so ya tafi da ita ne sai kowa ya tambayi wacece? Babu wata tafiya mai tsayi tsakanin gidajen da suka je, kuma duk inda suka tafi saiya musu alheri kamar yanda kowa ke saka ran samun wani abu daga gare shi duba daga tafiya ya dawo, har sha biyu na rana kafin su dawo a gajiye inda su Iffa ke gaba sai Salahadeen da Farha a baya suna tafiya a nutse.
Kallonta yayi ganin duk ta gaji ya kama hannunta, duk da taji dad’i amma sai bata nuna ba ta shareshi, cikin kulawa yace “Kin gaji ko?”
A k’asan mak’oshi ta amsa da “Um.”
Ba tare daya kalleta ba yace “Me yasa kikayi saurin fad’a musu matata ce?”
Ita ma ba tare data kalleshi ba tace “Saboda matarka ce.”
Wani murmushi yayi mai ciwo kawai bai ce mata komai ba, suna k’arasowa gidan da sallama, a cikin masu amsa sallamar harda mazan duk sun dawo sunyi wanka. Bai kalli kowa ba saida ya fara kallon inda yar amana take, har yanzu tana kan kujerarta sai dai da gani kasan a takure take, duk kusan a kewaye take da mutane suna kallonta, musamman ma yaran da suka dawo daga makaranta, duk sunyi tsaye a bayanta abu d’aya kawai suke son gani shine gashinta, sai wata yar budurwa dake zaune k’asa ta k’urawa k’afafunta kallo sai shafasu take tana fad’in kamar na jarirai.
Su kansu mazan kallonta suke da mamaki da kuma tambayoyin da suke son Salahadeen ya zo ya amsa musu, ance matarshi ce.
Zaune duk sunayi aka shiga sabuwar gaisuwa, a haka kuma aka cika gabansu da ruwa da gasashin kajin da suka saka yaransu suka gasa ma bak’i, sai ruwa masu sanyi da fura tasha nono, basu wani tsaya b’ata lokaci ba suka shiga ci hankali kwance amma banda Salahadeen da yake so ya fara gamawa da yar amana amma idon da zasu hau kanshi yake fargaba.
Inna Salamatu ce ta kalleshi ta kalli Sarah tace “Ku ba zaku ci bane?”
Sama da k’asa Farha ta hararesu tace “Gimbiya bata ci ba ai ba zai ci ba, saita zab’i wanda take so tukuna.”
K’asa yayi da kanshi cike da rashin jin dad’i, ya ji ba dad’i sosai ta yanda yaji zai nuna mata a zahirance, ba wata soyayya sukayi ba bare yace ta nan raini ya shiga tsakaninsu, rayuwar da sukayi a gida d’aya tun tana cikin zanin goyonta yasa ta raina shi ko me? Ba dan mahaifinshi ya had’a aurensu ba da shi dai ko kallon so ba zai mata ba bare matar aure, idan kuma tana ganin tafi kowa saninshi ne a yanzu to mu’amular aure ma ai sau d’aya ne hakan ya faru tsakaninsu, kamar yanda baida hayaniya haka bai cika son haye mata ba, watak’ila hakan na da nasaba da rashin jinta a zuciyarshi ne ko kuma dai haka Allah yayi shi. Yayi nisa a tunaninshi yaji baffanshi Idris yace “Salahadeen me take ci sai a nemo mata?”
Kallonshi yayi a hankali ya girgiza mishi kai ya mik’e tsaye, saida ya tsaya inda Sarah ke zaune ya mik’a mata hannu alamar ta taso tare da fad’in “…
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:14 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA GA
_DUK_
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
Talla
*Talla*
*Talla*
Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
2锔忊儯5锔忊儯
“Zo muje na nuna miki abinda nayi alk’awari.”
Da sauro ta d’ora hannaunta akan nashi ya rik’eta suka kama hanyar fita, da kallo duk suka bisu sai Farha data rasa me ke mata dad’i kawai ta fashe da kuka, Idi ma daya bisu da kallo ne yayi saurin kallonta yace “Lafiya ke kuma?”
D’aya daga cikin matan ce tace “Baban Abdu har sai kun tambayeta? Tana kallon mijinta na mata wannan wariyar akan wata k’abila mai jan kunne kafira.”
Cak ya tsaya sai dai kuma bai juyo ba, tsaf ya d’auke abinda ta fad’a a kunnenshi, ficewa kawai sukayi sai k’ara matse hannunta ma da yake, Idi ne yace “To wai abinda ban fahimta ba ma shine, wacece ita? Da gaske ya aureta d’in?”
Cikin nutsuwa sosai Mustafa ya gyara zama ya fad’awa baffan nasu duk abinda ya faru, suna tsaka da jajantawa da jimami da al’ajabi Farha tace “Da farko na yarda da abinda suka fada amma banda yanzu, yanda yake shishige mata da yanda yake kulata fiye dani ya nuna dama akwai wani abu a tsakaninsu.”
Kallonta Idi yayi yace “Daina kukan to zai dawo ya same ni, da kanshi zai min dalla dalla naji abinda kenan, ni ina na tab’a jin haka ma a duniya.”
Turo baki ta dinga yi saida ya lallab’ata ta ci gaba da cin abincin, suna idawa sallah duk sukayi suka d’an kishingid’a, wasu bacci ne ya fara d’aukarsu amma banda Farha data harzuk’a mijinta har ya bar gidan tare da hannun wata mace cikin nashi hannun.
Labarin da yake ta yad’awa bai wuce mutuwar Shakoor da kuma fad’an zunzurutun dukiyar daya bari ba, sai kuma labarin da Kabeer ya shiga ta Internet ya wallafa cewa ‘yarsa tayi aure a wata k’asa ne, inda kowane gidan telebijin ke aika tambayar shin zata zo ne dan gudanar da jana’izar mahaifinta tare da kwasar abinda ta gada, ko kuma dai shikenan ta tafi kenan ba zata dawo ba duba da auren nata ma babu wanda ya sani, kowa ya d’auka an sace ta ne sai yanzu ace tayi aure a wata k’asa. Babu wanda ya musu cewa aure tayi duba da hotunan da suka dinga yawo sanda suka je filin jirgi zasu bar garin, babu abinda ya nuna cewa saceta akayi.
Sanda aketa wannan kwaroronta kuma k’ungiya hankalinta ya fara tashi saboda tashin hankalin da shugaban ya fara shiga, Sarah ita kad’ai ce yar data basu wahala, dan haka yanzu duk hankalinshi ya koma kan yanda zaiyi ya kasheta, ya jaraba bila adadin amma abu d’aya ne kullum, suna tunkararta amma basa iya mata komai duk da k’arfin ikonsu, suna kallonta suna ganin yanda take gudanar da rayuwa a cikin mutane da kuma garin da ba nata ba, amma sun kasa mata komai.
Kabeer ne yayi alk’awarin kawo mishi ita ya kwantar da hankalinshi kawai, saida ya bashi tabbacin hakan kad’ai sannan ya bashi izinin fara aikin. Shiri yayi sosai dan ganin bai samu matsalar da zata ja mishi samun matsala da shugaban ba kafin ya fara aiwatarwa.