SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Ba tare daya kalleta ba yace “Idan kina so saina barki anan.”
Kallonshi tayi tana murmushi tace “Ban da wani dalili na zama anan.”
D’agowa yayi ya kalleta, tab’e baki yayi ya sake mayar da gabanshi yayi yace “Ni kuma fa?”
Da sauri tace “Garinku ne ai.”
A hankali ya kalleta yace “Ke kuma fa?”
Da mamaki ta kalleshi tace “Garinsu wanda ya sace ni ne.”
Da sauri ya kalleta, yanda tayi murmushi kawai baisan ya kece da dariyar da shi kanshi ya manta rabon da yayi ta ba, tana ganin wannan dariyar ita ma saita sake darawa. A take kuma ya had’e fuskarshi kamar ba shi ba, da haka suka isa gida ko da suka je kuma sun samu baffan nashi a k’ofar gidan tare da k’annan mahaifinshi, nuni ya mata da hannu ta shiga ciki shi kuma ya tsaya wurinsu ya zauna kan tabarmar.
A tsanake dukasuka kalleshi musamman Baffanshi Idris daya d’ora da fad’in “Salahadeen ka fad’a mana gaskiyar maganar nan, da gaske mai jan kunnen cen matarka ce?”
Ko d’aga kai baiyi ba sai ma wasa daya shiga yi da babbar yatsar k’afarshi wanda ya tank’washe k’afafun, kawunshi Garba ne yace “Salahadeen me ya had’aka da yarinyar nan? Kana da matarka ta sunna me ya had’aka da waccen kuma? Ko dan kaga mahaifinka baya raye ne zakayi wasa da amanar daya bar maka? To inma hakane ka sani mu muna raye ba kuma zamu tayaka ka ci zarafinta ba.”
Alamar gajiyawa ya shafi gaban goshinshi kawai ba tare daya kalli d’aya daga cikinsu ba yace “Kuyi hak’uri.”
Cikin fad’a Idris yace “Ban gane muyi hak’uri ba? Kana nufin ka gama kenan babu yanda za ayi da kai? Yanzu kai in ba ma sakarci irin na yaran zamani ba me ya kaika aure baturiya, baturiyar ma ba musulma ba, ko tana sallah ne?”
Da sauri Garba yace “Ina kaga alamun sallaha a goshin yarinyar nan, ka ganta fa da idonta kamar na mage sai dai ta zuba mana ido kawai tana kallo kamar mun ci bashinta.
Hannu yasa aljihu ya ciro lalitarshi ya shiga zaro sabbin kud’in da dama ya tanade su saboda zuwansu tunda ba wata tsaraba ya zo musu da ita ba, yanda suka ga yana ciro da jajayen nan sai k’yalli suke a mik’e kar dasu yasa duk suka d’anyi shiru, a hankali ya zubesu gabansu tare da fad’in “Ga wannan ayi hak’uri ba yawa, ina so ne zamu koma yanzu saboda ita kanta baturiyar ta kawo muku tsaraba amma bata samu damar zuwa da ita ba saboda bata san zamu taho ba.”
Duk da idonshi akan Salahadeen daya mik’e amma hannayenshi akan kud’in suke daya ke k’ok’arin d’auka, cikin farin ciki yace “A’a karma ku fara Salaha, ai ku da barin garin nan saida safe kuma.”
Garba kam cewa yayi “To in kun tafi yaushe zaku dawo da baturiyar kuma?”
Salisu ne yace “Wai ni kam ta ci abinci ma? Naga haka kuka fita ko? Ka tambayeta me take so mana saia samo mata.”
Duk zuba musu ido yayi bai ce komai ba, a hankali yace “Ku barshi ma, kayan lambu ma zasu wadatar da ita.”
Da sauri Idris ya kalli Salisu yace “Maza maza tashi kabe lambu a samo mata.”
Da “To.” Ya amsa amma bai iya tashi ba saboda ganin Salahadeen ya wuce jin an fara kiran sallah, da sauri kowa ya dawo da kallonsa kan kud’in dake hannun babbansu…
Kad’an daga ciki dai duk sunyi haramar sallah ta hanyar d’aura niyyar alwala, tana zaune tana kallo saita tuna da maganar mamie kan cewa addinin ya shiga ko ina duk k’ank’antar gari zaka samu bai bautar Allah shi kad’ai, yanzu kam gashi ta gani da idonta, haka kawai ta tsinci kanta da son yin abinda sukeyi duk da bata san komai a kai ba. Mik’ewa tayi tsaye ta cire hijabinta ta aje kan kujerar, butar da Iffa ta idar ta d’auka ita ma ta dubi ruwa inda taga kowa ya d’iba, kusa da Mamuh ta durk’usa tana kallonta dan ganin yanda zatayi, tana ganin haka tace “Zakiyi sallah ne?”
D’aga mata kai tayi alamar eh, murmushi ta mata tace “Kina son addinin nan ne?”
Kallon tuhuma ta mata tace “Zaki ce na bar nawa addinin ne?”
Murmushi ta mata tace “To ke wane irin addini kike da tunda kika zo ma ban ga kin gaishe da ubangijin naki ba? Ko ba kya waiwayarsa ne kema kamar yanda baisan da zamanki ba?”
Cikin rshin damuwa tace “Ni ko acan ba mai wata zuwa church bace.”
Murmushi ta mata tace “Ai ko church d’in ma ba kullum kuke zuwa ba sai ranar lahadi, mu kuma kinga a kowane wuni kai tsaye muke ganawa da ubangijinmu, babu shamaki babu mai fassarawa, babu d’an aika sak’o bare a samu tsaiko, kai tsaye ne daga ubangiji sai bawansa, kinga kenan a kullum kana tare da mahallicinka.”
Jinjina kai tayi tace “Hakane, nima kuma idan na tashi aikawa zan iya kama k’afa da father saboda sak’ona yaje da wuri.”
Murmushi Mamuh ta sake yi tace “Kinga muyi alwalar to kar lokaci ya k’ure.”
Ta ture d’an kwalinta sun shiga alwalar kenan taji ana jan gashinta ta baya, da sauri ta juyo har tana neman fad’uwa, yaran ne ta gani sai dariya suke alamar su fa abun tsokana suka samu ko wasa, juyawa tayi kawai ta sharesu suka ci gaba da alwalarsu.
Sun idar sun shiga d’aki Mamuh ta kalleta tace “…
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:14 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA GA
_DUK_
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
Talla
*Talla*
*Talla*
Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
2锔忊儯6锔忊儯
“Kafin kiyi sallah akwai matakan da dole akwai buk’atar ki takasu, ki zauna idan na idar sai muyi magana.”
Iffa ce taja tsaki sanda take saka hijab d’in ta tace “Musulmi ma yayi sallah babu alwala da gangan ya zama kafiri bare kuma ke da jiki duk najasa kice zakiyi sallah, ki fara tsabtace kanki tukuna malama.”
Kallonta Mamuh tayi tace “Idan kina wani abun sai naga kamar baki da maraba da jahilai da basu san hanyar islamiyya ba.”
Zaburowa tayi tana fad’in “Mamuh nice jahilar? Ni kike fad’ama haka?”
Tab’e baki kawai tayi ta kabbara sallarta ta barta tana kumfar baki, kamar yanda tace mata bayan ta idar ta zauna kusa da ita cikin nutsuwa tana kallonta tace “Sarah kina son addininmu ne?”
D’aga mata kai tayi tace “Ina so.”
Cikin sakin murmushi tace “Zaki shiga ne?”
Jim tayi ta kalli Iffa data idar da sallah amma bata sallame ba ta kuma kalli Farha data idar ita ma tana kallonsu, a hankali ta kalli Mamuh tace “Kiyi hak’uri ba zan iya shiga ba.”
Da sauri ta zaro ido tace “Saboda me?”
Girgiza kai tayi ta mik’e ta fita daga d’akin dan duk numfashinta ba bata jin shi da kyau, juyawa tayi ta kallesu suma duk sun tsareta da ido, mik’ewa tayi tace “Wallahi inhar saboda muzgunawarku ta k’i karb’ar musulunci ku sani laifinku mai girma ne, tunda dai ku ba jahilai bane da iliminku.”
Ficewa tayi ita ma daga d’akin inda Farha ta tab’e baki tace “Idan tayi niyyar shiga ai banu abinda zai hanata shiga.”