NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Kallonta Iffa tayi tace “To wuk’a muka saka mata a wuya ne da zata k’i shiga saboda mu?”

Sake tab’e baki tace “Ohon mata.”

A k’ofar gidan ta sameta tsaye, dafata tayi tace “Sarah lafiya? Me yasa kika ce ba zaki shiga ba? Kina tsoron wani abu ne?”

Murmushi ta mata kawai tana kallon fuskarta, ba aata iya fad’a mata ba sai bata so ta shiga su Iffa su ci gaba da muzguna mata, dan maganar data fad’a a ranar tana nan cikin kanta sanda ta bisu makaranta. Ganin ba tace komai ba ta kama hannunta suka k’arasa cikin wata inuwa suka zauna k’asan bishiyar suna kallon gari babu wata hira.

Yamma sosai ya dawo yace kowa ya shirya zasu koma, nan fa kawun nan suka dire akan ba zasu tafi yanzu ba sai sun kwana, su ma kuma sun dage ba zasu kwana ba dama su biyu ko uku ne, duk gidan kowa ya d’auka ana fad’in wajen kwana ai ba matsala bane, a k’arshe dai haka suka fi k’arfinsu musamman da suka kira mama suka fad’a mata, umarnin kwanan ta basu dan dai kwana d’aya kawai a cewarta.

An ci abinci yara duk kowa ya kama tabarmarshi ya kwanta, Salamatu ce ta shiga d’akinsu da robar lalle data kwab’a, zaune tayi tana kallon Farha data kishingid’a tace “Tashi ga lalle ki k’unsa a k’afafun ki.”

Tashi tayi zaune tana fad’in “Kam, Iya ina ni ina lalle yanzu, wallahi ba zan iya ba.”

A nutse ta kalleta tace “Farhanatu kina lafiya kuwa, dubi k’afafun Mamuh da Iffatu mana su dake yan mata, sun sha lalle bak’i wulik amma ban da ku dake da miji, kinsan mahimmancin lalle kuwa?”

Turo baki tayi tace “To Iya ai ba bana so bane, yanzu dai ne ban shirya ba zai bani wahala, tunda ban iya saka shi da kaina ba ni kad’ai.”

Gyara zama tayi tace “Tunda hakane to zo saina saka miki da kaina, ai ba wuya ne dashi ba yanzu za’a gama, baturiya ma zan saka mata ita ma.”

Juyawa tayi duk cikin d’akin bata ganta ba dan haka ta kalli Iffa tace “Ina baturiyar?”

Cikin rashin damuwa tace “Tana waje tare da Mamuh.”

Kallon Farha tayi tace “In tambayeki to?”

Da ido kawai ta bita hakan yasa Salamatu cewa “Yau kwanan waye a cikin ke da ita?”

Wani haushi taji ya taso mata da tambayar data mata, ita fa gani take kamar iskanci ne ake mata, amma a ganinta ita ma gatsali ne take musu kawai sai tace “Kwananta ne.”

Murmushi tayi tace “To bari ke na miki yau ita da asuba saina kunsa mata.”

Siririn tsaki taja tana kawar da kanta kamar tace bata son lallen ma, nan da nan Salamatu ta shiga d’ora mata scot ta shiga shafa mata lallen, ko da aka idar da sallah isha’i har ta ida mata dan su abun ba wuya ne a wurinsu ba ya zama jiki, tana idawa ta kwashe kayan ta fita, yarinyar data shigo ne ta kalla tace “Ke ina baturiyar gidan nan da Mamuh?”

Cikin gudu wanda da alama abu ta shigo yi ta koma tace “Suna waje kallon wasa, har da baturiya ma.”

Kallon yarinyar tayi sai dai har ta shige ban d’aki da gudu, aje kayan tayi k’ofar shiga d’akinta ta fita k’ofar gidan ba tare da mayafi ba, tsaye tayi tana hangensu sai kuwa ta hango yara na wasa wasu na tapawa suna wak’a, Sarah da Mamuh ma a tsaye suna tapa musu sai dariya take tana bin kowa da kallo.

Duk motsinta yana lura dashi daga cikin mota da yake zauna, komai nata k’are masa kallo yake yana sake mata wuri a zuciyarshi, lokuta da dama idan tayi murmushi shi kanshi saiya samu kanshi da yin murmushin ba tare da yasan ita me tayi ma ba, kawai dai ya tsinci kanshi da jin dad’in kallonta. Bai gaji ba bai kuma tashi ba kamar yanda suma basu gaji ba saida dare yayi duhu ya k’ara yi sannan yaran suka shiga rera wak’ar saida safe suna shiga gidajensu, lokacin yaran gidan suma suka shiga ciki tare da su Sarah, ko da suka shiga aka nuna musu wurin kwanciyarsu, har ga Allah ba zata iya bacci a d’akin nan ba a hakan ma wai an zab’a musu d’akin da yafi kowane ne, sai dai ina ba zata iya ba sadaukarwar da tayi a gidansu b’arawonta ma ya isa haka, idan tace zatayi anan kam zata rasa ranta ne.

Ta daiyi zaune akan shinfid’ar tana kalle kalle da kallon k’afafun Farha dake rufe cikin leda ita kuma har bacci ya d’auketa, sannu sannu Mamuh ma sai bacci ya kwasheta ya rage ita kad’ai, ajiyar zuciya kawai take saukewa ta rasa yanda zatayi, yanda take jin shirun yayi yawa babu motsin komai yasa ta kasa fita farfajiyar gidan, tana haka taji magana a sama duk da bata jin me ake fad’a, sai dai maganar namiji da mace ne sannan ana tab’a k’ofar wani d’akin, tana zaunen nan ita dai taji an bud’e d’akin nasu an shigo.

Kallon kallon sukayi muryar k’asa k’asa Salamatu tace “Ba kiyi bacci ba baturiya? Taso muje to.”

Kallonta ta shiga yi hakan yasa ta shiga kwatanta mata da hannu da baki da ido tana fad’in “Baban mijinki ne yace bai kamata yana da mata har biyu ba kuma ya kwana shi kad’ai, fad’a yayi ta min kamar zai cinyeni wai bansan ta kamata ba, yanzu taso muje ke saina kaiki d’akin mijinki.”

Ita in banda kalmar miji da ta so babu abinda taji, amma saita alak’anta maganarta da tunanin ko mijinta ke kiranta, tashi tayi tana mik’a mata hannunta kam ta mata jagora, d’akin yana can kamar bayan gidan kusa da garken awaki, bubbugawa tayi ba jimawa aka bud’e, kallon juna sukayi cikin mamaki yace “Gwaggo lafiya a wannan daren? Halan ta tsorata ne kamar yanda ta saba?”

Girgiza kai tayi tare da mik’a mishi hannunta tana fad’in “Yawwa ga matarka nan to, baffanka masifa yayita min wai ya kana magidanci ka kwana kai kad’ai anan, ka fito ga d’aki can yasa a ware muku.”

馃槀 (Kaka na da naje ganin gida akayi sallah magriba yanzu ya fara cewa tashi kije gida mijinki na can, da yanda iyayenmu ke girmama mazajensu haka muke da munji dad’in rayuwa mu ma.)

Shi rasa abin fad’a ma yayi sai binta da kallo harta shige nata d’akin, kallon Sarah yayi da take kallonshi kamar tana son k’arin bayani, cije leb’e yayi ya kalleta yace “Ke, je ki koma ki kwanta saida safe.”

Juyawa tayi ta nufi inda aka biyo da ita zuwa nan, shima juyawa yayi zai rufe k’ofar yaji muryar Idris na fad’in “Kai me kuke har yanzu baku kwanta ba wai?”

Duk tsayawa sukayi suna kallonshi, cikin rashin wasa yace “Dallah ka fito kaja matarka ku wuce ku kwanta, kowa ya kwanta daga ku sai aljanu kuna safa da marwa a balbalin gida.”

D’an k’aramin tsaki yayi ya fito daga d’akin yana mayar da k’ofar ya rufe ma su Zeid da sun jima da bacci suma, d’akin data nuna musu ya nufa yana ma Sarah alama da ido cewa ta taho, da sauri ta bi bayanshi gabanta na fad’uwa tsoro ya lullub’eta da tunanin ko wani abu ne ke faruwa ko zai faru, saida ta shiga d’akin taga yaja k’ofa ya rufe, kallon d’akin ta shiga yi sosai babu komai a cikinshi daga shafen sumunti sai leda sabuwa fil da kuma katifa da shinfid’a mai kyau, pillow d’aya ne akai bayana shi babu komai a d’akin hatta da labule ma.

Baaa tsaya komai ba ta haura shinfid’ar ta kwanta tana lumshe ido tana kallon sama, kallonta yayi ya k’ara jan tsaki ya k’arasa kusan katifar ya zauna ya tank’washe k’afafunnshi yana sake waigawa yana kallonta.

Shkru d’akin ya d’auka kamar babu mutane sai kuma ta zil ta tashi zaune tana cire d’an kwalin atamfarta tana firfita dashi, ido biyu sukayi dashi hakan yasa ta cewa “Kai ma ka gagara bacci ko? Akwai zafi sosai.”

D’an kwalin ta shiga mishi firfita shima da iya gaskiyarta kam shi saiya kawar da kanshi ma, gajiyar da tayi ne yasa ta dakata ta kalleshi a tsanake tace “Mr.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button