SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Ba tare daya juyowa ba yace “Uhm.”
A nutse tace “Ina so na shiga addininku, amma ina tsoron wani abu.”
Da sauri ya kalleta sai kuma ya kawar da kanshi yace “Me kenan?”
Gyara zama tayi tace “Ina tsoron kar na shiga kuma a dinga min gori da kirana da sunan da bai dace ba.”
Jim ya d’anyi tare da d’aukar wayarshi ya shiga dagulawa yace “Duk wanda ya miki gori kema ki masa gori mana, ai dake dashi duk d’aya ne.”
Da mamaki tace “Kamar ya?”
Cikin nuna halin ko in kula yace “Manzon Allah (S.A.W) ya fad’a mana kowane abun haihuwa ana haihuwarsa ne akan addinin musulunci, sai dai idan ya zo duniya iyayenshi su canza shi ta hanyar mayar dashi addinin da suke so, bamajuse, bayahude ko kuma banasare. Asalin hallitarki akan hanya madaidaiciya aka halliceki, samun kanki ba musulma ba wannan kuskure ne na mahaifinki.”
Numfasawa yayi ya ci gaba da cewa “Duk wanda zai kalleki ya miki gori akan kin musulunta ko ya nunaki da baki, ba lallai ya gama fahimtar miye ma addinin ba, tayiwu shima kawai ya tashi ya ga iyayenshi da kakaninshi a musulmai ne shima yake musulmi, bayan haka baisan fa’idar dake tattare da kasancewarshi musulmin ba, idan kuwa ya kasance hakane kinga zai zamana ke d’in nan da kika shiga addinin a bayanshi zaki fishi cin moriyarshi, domin kuwa kina shiga addinin nan zaki dawo tamkar yau ne mahaifiyarki ta haifeki, yanda kika zo duniya babu sutura ko wani abu daya danganci ado, to haka ma baki zo da wani abu daya shafi lada ba bare zunubi. Dan haka ki nutsu ki aje hankalinki ki sake tunani da kyau, idan har kina son shiga addinin musulunci to ki shiga kanki tsaye da duka k’afafunki biyu, kiyi tsayuwar daka tanda k’aramar tangard’a ko wani tasko bai isa ya wujijjiga k’afafunki daga kan turban addininki ba bare har ki razana ki motsa, kin fahimta?”
Saida ta had’e labb’anta ta d’aga mishi kai alamar eh, kallonta yayi yace “Zaki iya kwantawa.”
Kamar yanda yace kuwa kwancen tayi, ta rufe ido ne amma tunanin maganganunshi ta shiga yi dalla dalla, kamar daga sama taji yace “Me ya fara jan ra’ayinki ne?”
Bud’a ido tayi da sauri ta tashi zaune tana fad’in “Ka gane mr..?”
Duk tayi maganar ne tana k’ok’arin mik’e k’afafunta, d’orawa tayi da “Mamienku tana birgeni sosai, a gaskiya kunyi sa’ar mahaifiya, ta zamar min uwa nima ta raba da kewar mamana kaso tasa’in a cikin d’ari, sannan naga duk sanda na farka da dare cikin firgici ita take min du’a na koma bacci mai dad’i, sannan ina son prayer d’in nan ma da kuke saboda Mamuh ta fad’a min a kowace guda biyar da kuke kuna ganawa da ubangijinku ne.”
Cikin fahimtar duka kalamnta yace “To me ya kawo barazanar tsoron kenan?”
Jim tayi kamar ba taji me yace ba, d’an kallonta yayi lokaci d’aya kuma ya d’auke kanshi, a hankali tace “Yar uwan nan taka da matarka, sun tsaneni sosai basa k’aunata.”
Shareta kawai yayi sai dai a zuciyarshi ya ji ba dad’i sosai da har muzgunawarsu take neman saka rud’u a cikin hasken dake k’ok’arin shiga rayuwarta, ta wutsiyar ido ya lura da yanda tayi jugum sai kawai yace “Kina son Mama sosai ne?”
Murmushi ta saki cikin zumud’i tace “Sosai ma, da ace kud’i na da darajar da zasu iya siya min Mamie, dana sadaukar da duk abinda na mallaka dan na fanshi Mamie a hannunku na tafi da ita k’asata, mutuniyar kirki ce da bata damu da komai ba.”
A tsanake ya kalleta yace “Da gaske kike?”
Kallon idonshi tayi kamar mai son tuna wani abu sai kuma tace “Na rantse maka da ubangijin da kake bautawa, ubangijin daya halliceni ya halliceka, ko ba haka bane?”
Juyar da kanshi yayi yana basar da dariyar dake son taho mishi yace “Idan kin tashi ki tafi da ita mun bar miki.”
Zaro ido tayi tace “Da gaske mr.? Ba wasa kake min ba ko?”
D’aga kafad’a yayi yace “Babu wasa, ki tafi da ita tunda kina so.”
Wata siririyar ihu ta saki tare da zaburowa daga zaunen ta mak’aleshi a wuya tsabar jin dad’i kuma ita ta yarda har zuciyarta, kamar a mafarki ta shiga jera mishi sumba a kumatu tana k’amk’ame da wuyanshi tana fad’in “Nagode nagode, nagode sosai mr., mr ka taimake ni nagode sosai, nima na samu uwa.”
Ita bata saki wuyanshi ba kuma bata daina sumbatarshi ba, jin abun ya mishi yawa har ya fara wahala da numfashinshi saboda shake mishi wuya da tayi yasa shi d’an d’ago kanshi ya juyo kad’an zai mata magana, a akasi ta kai bakinta ta sumbaci kumci shi kuma ya juyo ta dannawa labb’anshi sumba…
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:14 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA GA
_DUK_
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
Talla
*Talla*
*Talla*
Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
2锔忊儯7锔忊儯
Da sauri ta janye bakinta tare da yin zaune tana sunkuyar da kanta, ba tare data had’aido dashi ba cikin murmushi tace “Nagode fa.”
Ko da ta fad’a ta juya mishi baya ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya da sauri sauri, shiru babu mai magana sai shi da yake fitar da numfashi da k’yar, dan ya yarda d’ari bisa d’ari sak’on nata ya zo akan daidai kuma a bakin gab’a, ya kasa motsawa ne dan kar ya sake jijjigo wata matsalar, ba tare da wani ya sake k’wak’waran motsi ba har bacci ya d’auki Sarah a cikin duniyar tunaninta.
Da wayarshi ya shiga karatun Alqur’ani inda nutsuwa ta fara sauko mishi a hankali, dare yayi sosai Sarah dake bacci a gefenshi ta fara juyawa tana cije bakinta tana yamutsa fuska, aje wayar yayi ya d’an matso kusanta ya fara tofa mata addu’a, madadin raguwa sai yaga abun na k’ara yawa sai jujjuya kanta take kamar tana so tayi magana, fuskarta da kanta zuwa wuyanta yaga sai zufa ke tsatsafo mata, sake matsawa yayi daf da ita ya d’auki d’an kwalinta data jefar akan katifar, gyara shi yayi cikin nutsuwa ya d’orashi saman wuyanta da nufin goge mata gumin, dama a tsorace take hakan yasa ta daka ihu tare da zabura da k’arfin tsiya ta mik’e zaune.
Da azama kafin ta gama ihun ya rufe mata baki tare da saurin zura hannunshi ta bayanta ya jawota ya mannata a k’irjinshi, dan inhar aljanu ne ke tsorata ta to tashi a tsoracen zai basu damar cutar da ita, shafa bayanta ya shigayi yana sake matseta yana d’an bubbuga bayanta yana mata “Shiiiiii, shikenan ya isa, ya wuce.”
Jin d’umin mutum da kuma maganarshi yasa ta sake k’amk’ameshi ita ma da kyau tana numfashi da sauri sauri, jin yanda take ta cukuikuyeshi yasa shi sakinta gaba d’aya, amma ita tana rik’e dashi gam, hannu yasa cikin dubara ya d’agota daga jikinshi, kamar yarinyar da za’a k’wata daga hannun Mamanta sai kuwa ta shiga rik’e rigarshi tana jawowa alamar bata son su rabu, hakan yasa shi d’ago kanta yana kallon fuskarta, ta lik’e ido gam sai bakinta dake ta rawa kamar mai jin sanyi, ga sirara hawayen dake sirarowa akan fuskarta ta cikin kurmin rufaffun idonta.