NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               2锔忊儯8锔忊儯

Tsoro da mamaki ne suka saka ta saki zanin tana sunkuyawa, da iya k’arfinta tasa hannu ta kai mata duka a labcecen mayanta da babu komai akai, wata zabura tayi a rud’e tare da fad’in “Waouch!”

Sosa bayan ta shiga yi tayi zaune tana kallon Farha dake tsaye kanta tana huci, cikin tsanarta da d’aga murya tace “Ke ina kika kai min mijina? Da gani dai dama ba zan tambayeki yar iskar ina ce ke ba, amma ki fad’a min tun yaushe kike iskanci da mijina?”

Sarah da ba ta gama gane yaren nata da kyau ba ta d’aga baki za tayi magana Farha ta kwad’a mata mari a fuska, cikin jin haushi ta durk’ushe duka gwiwoyinta ta dadumo gashin Sarah da hannu biyu ta shiga wujijjiga kanta tana fad’in “Zaki fad’a min me ye tsakaninki dashi tun a can da kuka zo kuna raina mana hankali? Ko saina kasheki a d’akin nan.”

Sarah da take jin abun kamar mafarki take ihu ta shiga zumdumawa tana ta k’ok’arin kare fuskarta, ta riga data mata rarumar da ba zata iya kare kanta ba, gashi bata son motsawa saboda babu komai a jikinta, dukanta ta dinga yi kamar aikota ne akayi ko ta samu baiwa. Da k’yar ihunta ya riski yan gidan dake can balbali, a sukwane suka taho da tunanin ganin me ke faruwa.

Ai da sauri Salamatu da Rakiyya sukayi kan Farha suna salati suka rik’ota, suna d’agata amma sai k’ok’arin sake kai mata duka take tana fad’in “Ku sake ni na kashe yarinyar nan, har ni zata kulawa miji a gabana.”

Tana jin sun d’agata ta sake jawo zanin ta rufe jikinta sai sunne kai take tana had’a kai da gwiwa tana gyara gashinta daya yamutse, fuskarta da wuyanta sunyi jawur da duk wani wuri da Farha ta d’ora yatsunta akai, Mamuh ce ta k’arasa tana shirin rik’ota ta zille taja baya tana fashewa da kuka, cike da taisayinta ta sake matsawa tana fad’in “Bari na taimaka miki Sarah.”

Ja baya ta sake yi ta girgiza mata kai tana fad’in “No, dont tauch me, please leave me alone.”

Cikin rarrashi Mamuh tace “Sarah, ni fa k’awarki ce, ki bari na taimake ki mana.”

Salamatu ce ta matso kusanta ta dafata tana kallonta tace “Kiyi hak’uri kinji, tashi ki saka kayanki.”

Da ido kawai ta bita sai shan majina da take, Mamuh ce ta fad’a mata abinda take nufi, sunkuyar da kanta kawai tayi dan haka Salamatu ta kalli su Iffa dake tsaye tace “Dan Allah ku bata wuri ta mayar da kayanta.”

A harzuk’e Farha tace “Yar iska dama babu kaya na sameta, haka ta kwana tare dashi Allah kad’ai yasan abinda sukayi, shima bari zai zo ya same ni a gidan ai.”

A hassale ta fita, sauran na fita Salamatu data jima da lura da abinda ke kan katifar ne ta kalli Mamuh tace “Ki ce Rakiyya ta d’ora mana ruwan zafi.”

“To.” Ta fad’a tana fita da sauri, kallon juna sukayi ganin sai fitar da kowa na d’akin take, cikin k’ok’arin fahimtar da ita tace “Ke ke, jiya…shine daren farkon…ki..ki ke daren farkonki ne?”

Kallon fuskarta tayi sosai, sai tayi tunanin kar dai saboda abinda ya faru tsakaninsu ne matarshi ta mata haka, da k’yar ta shiga k’ak’aro hausar ita ma tana fad’in “Ni fa ba laifina bane..laifinshi ne, saida na fad’a masa ya daina amma bai sau..rar..eni ba, ina so na bar nan…bana son ci gaba da zama anan, please ki fad’a masa ya d’aukeni daga nan.”

Abun mamaki sai kawai taga matar ta rik’e hanci da yatsu biyu ta rangad’a gud’a, mik’ewa tayi ta fita daga d’akin tana fad’in “Baturiya ta kawo gidan miji, ta kawo martabarta da kimarta.”

Da wannan mamakin ta bita da kallo amma sai taji gidan ya sake gaurayewa da wannan gud’a, me suke ma? Oho! A cewarta, mik’ewa tayi kawai ta d’auki pant d’in ta ta saka ta d’auki zani, duk da ita d’in tana aiki da dama ne a madadin ta saka hab’ar hagu a cikin dama sannan ta d’ora ta dama a hagu saita d’aura, sai kawai ta birkita hannayen ta wani irin sagalashi ta barshi haka wanda kad’an zai motsu ya since, dama Mama ta d’auro mata shi tun a gida, ta juya zata d’auki riga ne taga jini jini dake kan katifar, a take taji gabanta ya fad’i sai kuma ta share ita ba wani abu bane a wajenta, saka bras d’inta tayi da riga ta d’auki d’an kwalin ta ta fito cikin sand’a.

Ganin kamar zata ganta ne yasa ta saurin juyawa ta koma d’akin, tana shirin b’oyewa dan bata son sake ganin kowa taji matar ta shigo, kama hannunta tayi suka fita daga d’akin, kamar amaryar da za’a ma wanka haka ta dinga gud’a wasu na binta da tapi da wak’a har suka shiga ban d’aki. Akan kujerar katako ta zaunar da ita, nuna mata ruwa tayi da alamar tayi wanka ta fito sannan ta fita ta barta, dafe goshi tayi cike da jin an fa takura mata, kallon ruwan tayi taga har da wasu hakukuwa a ciki da saiwa saiwa ita dai bata san miye a ciki ba.

Cike da rashin so ta cire kayanta da k’yamk’yamin wurin ta aza kan katangar ban d’akin, sanda ta d’ebo ruwan ta zuba a jiki saida ta lumshe ido, d’umin ruwan ya mata daidai yanda rake buk’ata, ga kuma wani sihirtaccen k’amshi da ruwan ke fitarwa wanda ta tabbatar na wannan hakukuwan ne data gani, a nutse tayi wankanta ba tare data goga ko da sabulun data gani ba bare soson wurin, tana idawa ma butar k’arfe data gani ta d’auka ta shiga wanke gabanta da kyau, tana idawa ta tsane kanta ta mayar da kayanta ta fito a hankali kamar mai tsoron fitowa.

Fitowarta ya dace da shigowarshi, kallo d’aya ta mishi ta d’auke kanta, haushinshi take ji ba dan abinda ya mata ba sai dan tafiya da yayi ya barta matarshi na neman kasheta. Shima yana shigowar idonshi suka jagorance shi ya fara kai kallonshi kanta, wani d’aukar masa ido yaji tayi sai kawai ya d’auke kanshi, shi fa har ga Allah kunya ce tasa shi k’in dawowa gidan na abinda yayi, sai dai da yasan abinda ya faru da bai fita ba ma, Farha dake zaune bakin bishiya ce ta tarbe shi cike da jin masifa, yanda ta tareshi tana wani jijjiga yasa shi kallonta yace “Ina ji?”

A take tace “Me ye had’inka da yarinyar can?”

Shima taken ya mayar mata da “Idan munje gidan zan sanar dake, ku shirya zamu tafi.”

Ko da ya fad’a ya wuce ya nufi d’akin da suka kwana, Salamatu na ganin haka ta kamo hannun Sarah suka nufi d’akinta, zaunar da ita tayi kan gado ta bata mai tace ta shafa, bata iya shafawa ba dan duk bata cikin yanayin dad’i, Salamatu kuma bata damu ba sai dire mata kwanon budurwar kazar data gaggauta b’ararraka mata ita tasha yaji da kuma had’i, yanda taga dahuwar ne yasa ta yamutsa fuska tace bata ci, amma Salamatu ta dage har saida ta saka mata a baki, da k’yar ta ci sau uku bata sake loma ta hud’u ba shima ji tayi kamar zatayi amai.

Lek’owar da yayi ce tasa su kallon k’ofar a tare, kallon fuskarta yayi yace “Muje ke muke jira.”

Da sauri ta mik’e dan dama tana neman abinda zai rabata da matar, mik’ewa tayi ita ma ta biyo bayansu tana fad’in “Salaha idan kun koma dan Allah kace ma Amina nace ta mata lalle a k’afarta.”

A cikin mak’oshi ya amsa da “Uhum.”

Duk a farfajiyar suka tsatsaya jiransu, matan gidan ma duk sun hallara sai addua’r Allah ya kiyaye hanya suke musu, nan ya sa hannu aljihu ya ciro sabbin kud’ad’e suma ya basu nasu rabon, zo kaga murna kowace baki bud’e tana ta godiya, sai dai suma basu barsu haka ba saida kowace ta musu guzuri na abinda ya sawak’a kafi k’arfinshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button