SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Da sauri ya juyo ya kalleta, yanda d’umin bakinta ya sauka kan fuskarshi da yanda ta kira sunanshi sun kusa zautar dashi, bai tab’a jin dad’in sunanshi ba irin yau, yanda ta cire harafin a d’in dake kusa da s ta farko saita had’eshi da Sla ya matuk’ar birgeshi. Yanda yake kallon fuskarta yasa ta yin k’asa da idonta ta rik’o hannunshi tace “Ba zan tambayeka da kaina ba, amma nasan zaka sake ni idan na tafi tunda kace zaka min saki irin na addinin musulunci ne.”
A hankali ta saki hannunshi tare da fad’in “Bye.”
Da sauri ta fita daga motar yana k’ok’arin rik’o hannunta, da kallo ya bita har ta shige ba tare data juyo ba, wani d’an tsaki ya saki tare da kawar da kanshi, da sauri ya fita daga motar da gudu gudu ya nufi shiga ciki, a daidai k’ofar zai shiga ya hangeta ta ciki, babban tashin hankalin daya shiga shine hangota da wani matashin sauri kuma da gani shima kasan bature ne, to amma wanene? Yanzu ne suka had’u ko kuma dama sun san juna? Waye shi? Me yake nema tare da ita?
Sanda ya gama ma Sarah bayanin waye shi cikin jin dad’in samun abokin tafiya ta bashi hannu suka gaisa kamar yanda ya bata hannun tun farko, tunawa da kalaman Mama yasa ta k’ok’arin janye hannunta, amma saiya rik’e ya jata suka ci gaba da tafiya. Wani kukan kura yayi zai shiga wurin sai masu tsaron k’ofa suka rik’eshi suka hanashi shiga, cikin jin haushi ya dawo motarshi ya zauna yana ta tambayar kanshi waye waccen? Wanene shi?
Da sauri ya d’auki wayarshi ya shiga latse latse, Richard ya sanar ma da sak’on zuwanta tare da neman alfarmar ya isa filin jirgi dan ya tabbatar mishi da saukarta, duk da Richard ya amsa da to amma saiya kasa matsawa daga wajen, tunani ya shiga yi tabbas tana cikin had’ari fa, dan haka kawai ya nemi wani hotel ya sauka yana so yaji daga bakin Richard idan har yace da matsala to zai tafi shima komai ta pamjama pamjam.
Yanda kowa ya samu damar yin bacci saboda dare yayi amma banda ita, gaba d’aya tunanin darenta na jiya da mr. ne ke kai kawo da ita, ta yarda ya zama jarumi a wurinta dan shine ya fara yin abinda babu wanda ya tab’a kwatanta yi mata shi, ajiyar zuciya ta sauke tare da k’ara jan d’an bargon da take lullub’e dashi ta sake k’urawa tagar ido banda sararin duhu babu abinda take gani. Bayan awoyin da aka share ne suka sauka lafiya, abun al’ajabi shine filin jirgin cike yake da mutane sun zo tarbanta har da yan jarida mak’il a wurin.
Sanda Salahadeen ya kasa tsaye ya kasa zaune sai yake jin a jikinshi tabbas akwai abinda ke shirin faruwa, sai kawai ya sanar da Richard ya shelanta zuwanta ta kafafan labarai da kuma social media, hakan zaisa mutane su isa wurin, idan kuma akwai nufin wani abu to zasu rage mishi kaifi ne. Sanda David ya ga wannan taron mutane kuma ga yan jaridu dake d’auka mafi aksari kuma live ne saiya tura sak’o da wayarshi cewa “Akwai matsala fa, mutanen gari da yan jarida duk suna wurin nan, ba zan iya saceta anan ba.”
A wayar da sak’on ya shiga ne aka duba, cikin jin haushi aka maido mishi da “Baka da hankali ne? Kar kayi k’ok’arin yi mata komai a gaban mutane, ka rakota ku taho gida.”
A tak’aice David ya amsa da “Ok boss.”
Maido mishi da sak’on akayi da “Ya akayi suka sani?”
A tak’aice ya amsa “Ban sani ba nima.”
Cikin rashin jin dad’i Alhaji Kabeer ya aje wayar, amma dai anyi mai wuyar tunda ta shigo garin ai, daya ya tura David ne dan yaje har can ya d’aukota, sai kuma suka gane ai tana hanyar zuwa filin jirgi daga bayanan bin diddigi da suka mata, kuma insha Allah da taimakon yaron zata shigo hannunsu tunda aljanu sun kasa ai sai mutum yayi.
Kallon mutanen take da murmushi a fuskarta har suka k’araso, da sauri s茅curit茅 d’in data tabbatar na mahaifinta ne suka taho da azama suka zagayeta tare da tura David baya nesa da ita, kareta suka shiga yi da bata tsaro na ban mamaki, mutanen wurin kam sai d’ago allunan da sukayi rubutu akai suke wasu na jeho mata flawers d’in da suka kawo mata sai ihu ake, wasu allo biyu ne suka tafi da imaninta ganin abinda yan matan suka rubuta akai, d’aya ta rubuta da manyan bak’i cewa “You are the best for me Sarah.”
D’ayan kuma ta rubuta “You are my roll model, i love u.”
Matsawa tayi kusansu nan fa yan jarida suka fara jifarta da tambayoyin ya akayi me ya faru? Tambayar da aka mata a had’e ta bawa talatin baya, saida taji sun lafa ta had’e hannayenta tana kallonsu tace “Babu wanda yayi kidnapping d’ina, da kaina na tafi tare da saurayi na.”
Wata ce ta tambayeta “Ina kuka tafi? Kuma me yasa babu wanda yasan da labarinshi sai sanda aka ga barinku k’asar nan?”
A hankali tace “Yeah, ni na nemi mu b’oye alak’armu har sanda zamu tashi aure, sannan munje k’asarsu ne, saboda ina son zaga duniya shiyasa muka tafi.”
Wani d’an jarida ne yace “Amma me yasa ko mahaifinki baisan da labarin ba?”
Ba tare da gazawa ba tace “Saboda idan ya sani ba zai barni ba, baya son na fara kula kowa a yanzu bayan kasuwancinmu.”
Wasu tambayoyin aka dinga jefo mata amma bata kulasu ba ta wuce tana d’aga musu
Hannaye ta nufi inda s茅curit茅 d’in ke nuna mata, har zata wuce sai kuma ta tsaya cak, da sauri ta sake kafe allon da ido ganin wata dattijuwa ta rubuta “My business girl.”
Samun kanta tayi da murmushi sanfa ta tuna abinda mr. ya fad’a mata, business girl, girgiza kai tayi ta sake sakin murmushi ta wuce suka tafi, suna daf da shiga mota motar police suka k’araso da gudun tsiya suka sha gabansu, tsayawa sukayi suna kallonsu har insp. d’in daya fara bincike kan b’atanta ya k’araso, nuna mata id card d’inshi yayi yace “Madame zaki biyomu office domin yi miki wasu tambayoyi akan b’atanki.”
D’aya daga cikin s茅curit茅 d’in ne zaiyi magana ta d’aga mishi hannu, kallon insp. d’in tayi tace “I hope ba zamu jima ba?”
Girgiza mata kai yayi yace “Yanzu zaki dawo gida madame.”
Har ta taka zata wuce s茅curit茅 d’in kasancewarshi babba a cikin masu tsaron yace “Madame yau ne fa jana’izar mahaifinki, yanzu haka nan da minti talatin za’a kaishi.”
Da mamaki ta kalleshi tace “Waya shirya haka bayan kuma ni ya dace nayi?”
Da ladabi yace “Joseph da Sandra ne (tsofaffi ne da suke aiki a gidansu tun tana yarinya, mahaifinta kanshi na girmama su).”
A tsanake ta kalleshi tace “Ok kuje ku fad’a musu ina zuwa.”
Girgiza mata kai yayi yace “Madame an turo mu ne mu tafi tare dake mu baki kulawa.”
Kallon insp. d’in tayi ta mishi alama da su wuce, a jibgegiyar motarta ta shiga suka jata suna biye da motar police d’in har suka isa, d’akin interrogation suka shiga da ita, inda wasu daga waje ta wani kakkauran madubi suke hengenta da jin abinda take fad’a ta lasifikar dake kunnensu, sai cctv cam茅ra dake nuna musu ita ta ciki, duk abinda ta fad’a a gaban yan jaridar shi ta sake maimaitawa anan ma, sai k’arin bayani kawai data tabbatar musu ba saceta akayi ba da k’afarta ta tafi da saurayinta, sun tambayeta yana ina yanzu tace akwai abinda ya rik’eshi amma da kanshi ya kawota airport kuma yana nan zuwa shima, da a tsarinsu zasuyi shirin jana’izar mahaifinta tare ne amma sun samu har an rigasu shiryawa, haka suka gamsu suka sallameta suka tafi gida.
Babu abinda ya sauya a gidan sai manyan mutanen dake zuwa da bak’ak’en kayansu, nan fa aka shiga mata ta’aziya tare da gaisheta haka ma’aikatan gidan sukayita gaisheta da girmamawa, tana had’uwa da Sandra suka rumgume juna suna kuka, godiya ta musu na shirin da sukayi, Sandra ce ta kalleta tace “Madame kije ki shirya ki fito father Daniel ya zo.”