NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Jinjina kai tayi ta wuce ciki, d’akinta babu abinda ya canza sai ma gyarashi da ake, k’amshin kad’ai da taji ya tabbatar komai can da nan ba d’aya bane, hoton fuskarta wanda aka zana shi ta k’urawa ido, hawaye ne
taji sun cika mata ido saboda ta tuna mahaifinta sanda ya bata hoton a murnar rana k’ara shekarar haihuwarta. A hankali ta dinga kallon komai na d’akin, duk wani abu mai kyau da tsada a d’akin mahaifinta ne ya bata kyautarshi, da sauri ta cire kayanta ta shige ban d’akinta.

Ba dan ana jiranta ba ta so zama a cikin ruwan d’umin data tara, amma da gaggawa tayi wankan da sabulunta mai shegen k’amshi ta fito, tana tsaye gaban madubi tana shiryawa ta hangi shatin cizon da mr. ya mata, shiru tayi tana kallon wurin kamar bata motsi, saida ta dawo hayyacinta tayi sauri ta shafa lotion d’inta ta saka wata doguwar riga bak’a da hularta bak’a ita ma wacce ta rufe mata rabin fuskarta har kusan hanci amma shara shara ne tana ganin komai a ciki, bak’ak’en takalmi ta saka sai wani mahuci bak’i na kayan data rik’e a hannu ta fito.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:16 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               3锔忊儯0锔忊儯

Kowa na ganin saukowarta ya mik’e akayi haramar fita, cikin tattausar murya tace “Ku dakata.”

Duk tsayawa sukayi suna kallonta, saida ta sauko ta sake kallon kowa tace “Nagode da halartarku zuwa wajen wannan taron, amma kuyi hak’uri ni zanyi jana’izar mahaifina yanda addininmu yace ayiwa duk wani musulmi.”

Kallon Sandra tayi tace “Ki sallami kowa ku same ni a bayan gida.”

Ficewa tayi da sauri tana jefar da mahucin hannunta, tana zuwa ta samu d’aya daga cikin s茅curit茅 d’in tace mishi “Duk inda zaka shiga ka samo min malamin addini na musulunci, ko ka zo min dashi ko kuma ka kaini wurin shi.”

Da girmamawa yace “Ok maa, akwai masallaci anan gaba kad’an, anan ma za’a samu.”

Kallonshi tayi tace “Are u sure?” D’aga kai yayi yace “I am very sure.”

Juyawa tayi ta nufi shiga ciki ta k’ofar da kai tsaye zata sadata da library suka shiga, saida ta danna wasu lambobi sannan k’ofar ta bud’e ta shiga, zaune tayi akan makekiyar kujerar ta d’auki biro da takarda ta shiga rubutu kamar haka.

“Ban san komai ba a game da addinin musulunci, amma ni musulma ce haka ma mahaifina, sai dai zama anan yasa sam mahaifina ya manta da addininsa da al’adarsa, yanzu gashi ya rasu ana neman binneshi a cikin kafirci, bana son haka ta faru shiyasa nake naman taimakonka, dan giraman Allah ka zo kayi wa mahaifina abinda ya dace dashi, idan za’a biya ne a shirye nake da biyan ko nawa ne, amma dan Allah ka taimaka mana.”

Tank’washe takardar tayi ta mik’a mishi tace “Ka kai mishi, idan ya amince zai zo saika taho dashi nan.”

Karb’a yayi ya juya da girmamawa yana fad’in “Ok maa.”

Yana fita suka had’e da Alhaji Kabeer ya shigo ciki, har ta mik’e daga kujerar ganinshi yasa ta saurin tahowa da sauri ta fad’a jikinshi tana fashewa da kuka da fad’in ” Thank God u are here Uncle, i am happy to see u.”

Wani murmushin mugunta ya sakar mata tare da rumgumeta shima yana fad’in “Sarah u are a live? Ina kika shiga?”

D’agowa tayi tana share hawayenta tace “Ina nan uncle, naje k’asarsu Abhi ne.”

Rik’e k’ugu yayi yace “Sandra ce ke fad’a min wai ba za ayi jana’izar mahaifinki ba, what is a probl猫me?”

Kafin tayi magana su Sandra suma suka shigo, saida suka samu wuri suka tsaya ta kallesu tace “Uncle Abhi ma yana da nashi religion, dan haka nake so a mishi jana’iza yanda addininshi ya tsara.”

Cikin makirci ya dafa kafad’arta yace “U are right princess, what do i do now?”

Kallonsu Sandra tayi tace “Na aika a kirawo min malamin addini, zan kula da komai.”

Ajiyar zuciya ya sauke ya nufi k’ofa zai fita yana fad’in “Ok let me handle this.”

Rik’o hannunshi tayi tace “Uncle i want to talk?”

Juyawa yayi ya kalli su Sandra kafin ya nuna mata kujerun alfarma yace “Zauna to.”

Kamar yanda ya fad’a tayi tana kallonshi shima ya zauna, har su Sandra sun juya ta dakatar dasu, nuna musu wurin zama tayi tace “Ku zauna dan Allah, ina buk’atar shawararku kuma matsayinku na amintattun mahaifina.”

Zaune duk sukayi falon ya d’anyi shiru kafin Kabeer ya kalleta yace “Sarah are u allrigth?”

Nisawa tayi ta kalleshi tace “I am okay, uncle i want to tell u something.”

Duk zuba mata ido sukayi hakan yasa tace “Ina so zan bar k’asar nan ne.”

Da mamaki suka kalleta sai Kabeer da yace “Ban gane zaki bar k’asar nan ba? Ina zaki koma?”

Kallonshi tayi tace “Ina so zan koma Spain ne a Barcelone.”

Joseph ne yace “Mma, me yasa zaki bar nan a yanzu? Ko kinsan cewa duk nauyin kula da harkokin kasuwancin yallab’ai ya koma kanki ne?”

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi tace “I know, acan ma akwai wani kasuwancin nashi wanda na mallaka, ina so zan tafi can, ba zan iya zama a gidan nan ba saboda komai dake cikinsa yana tuna min da Abhi ne.”

Kabeer ne yace “Sarah ke kamar ‘yata ce, zaki iya komawa gidana idan kina son haka, zan kula dake fiye da zatonki, zan baki kariya kamar haka yanda nasan mahaifinki nayi har mutuwarshi ta riskeshi.”

Girgiza kai tayi zatayi magana kuma wannan s茅curit茅 d’in ya dawo da sauri ya shigo, kusa da ita ya sunkuya a cikin kunne yace mata “Mun zo tare dashi, yana waje yana jiran izininki.”

Mik’ewa tayi ta juya tana kallonshi tace “Are u mad? Baka san darajar malamai bane, ka barshi a waje ne kana jiran na bashi izinin shigowa.”

Tsaki taja tare da fita da sauri, da kanta ta mishi iso ya shigo ciki, suna kallo suka shiga wani d’akin bayan ta danna wasu lambobi k’ofar ta bud’e, zaunawa sukayi a tsanake ta kalleshi tace “Malam kaji kirana kai tsaye ko? Ka gafarceni idan na shiga lokacinka, bani da zab’i ne.”

Girgiza kai yayi yace “Ba komai, me kike buk’ata yanzu?”

Cikin sanyi sosai tace “Ina so ne ka mishi duk abinda ya dace sannan ka sallace shi, tunda nake ban tab’a ganin Abhi na yayi ibada ba, naji ance babu kyau bawa ya cire rai da rahamar ubangijinsa, ina kyautatawa Abhina zato ko Allah zai yafe masa.”

Jinjina kai yayi yace “Gaskiya ne, kuma kyautata zaton ga musulmi shine abinda ya dace, Allah mai rahama ne ga bayinsa, idan har ba shirka yake ba kai tsaye ba za’a yanke masa k’auna ba, ko da yana aika duk wani kaba’ira na zunubi, akwai yiwuwar ubangiji talikai ya dubeshi da idon rahama da jin k’ai abisa wani k’ank’anin abu da yayi wanda a ganin idon mutane ba komai bane, dan haka yanzu za’a fara masa wankan gawa daga bisani sai a mishi sallah a rufeshi gidanshi na gaskiya, a matsayiki na ‘yarsa yanda Allah ya hore muku inhar kin tabbatar da halalin dukiyarsa zaki iya gina wasu wurare a matsayin sadaqatul jariya, ladar zata same shi a kabarinshi insha Allahu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button