NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Tana fad’a ta shafe jikinta ta sake jan lallausa kuma kakkauran zaninta ta rufa ta rufe ido.

Jijjigar da gadon yayi da ita ne yasa ta bud’a ido, jijjiga da babu kwaramniya a ciki dole ka tashi, dama kuma anyita ne saboda ta tasheka ba sai alarm ya mata kururuwa a kunne ba, zaune ta tashi saida ta gama wartsakewa ta kalli inda tasan zata samu coffee, tana ganinshi ta mik’e ta nufi ban d’akin, saida ta wanko bak’i ta dawo ta d’auki kofin coffeen ta kurb’a, saida ta lumshe ido saboda anjima ba’a had’u ba, a hankali ta ci gaba da sha tana fita daga d’akin ta haura saman bene, daga can saman tana kallon kai da kawo ababen hawa da mutane ita kuma tana shan abunta hankali kwance, rayuwar da tayi gidan mutanen da bata had’a komai dasu ba take, ta samu masu kirki da marasa kirki a ciki, kuma duk haka saboda suna ganin wai taje gidansu ne, suna ganin kamar ta tare musu wuri, wani murmushi ta saki kawai dan sai taji sun bata dariya, ita kam inhar da rai da rayuwa wata rana sai tayi sanadin zuwansu inda take, in haka ta faru kuwa zata nuna musu su k’ananan mutane ne, zata nuna musu ba kowa bane su da muhallinsu, zata nuna musu abinda ake kira da arzik’i da kuma alfarma da daula, zata sa su manta da tasu daular da suka jinta kamar masarauta, zata nuna musu kara tayi musu wajen zama dasu a wannan gidan, sai tayi abinda zasu yarda su jinjina ma k’ok’arinta na zama a cikin k’asarsu ma bare kuma gidansu.

Ta gama shiryawa cikin riga da wando na suit d’inta kalar farare masu kyau, amma abinda bata tab’a yi ba shine d’ora wannan kallabin data taho dashi na Mamuh ta yane kanta, tana fita bayan tayi break s茅curit茅 d’in suka bud’e mata k’ofar mata ta shiga, mota biyar ce suka fita a gidan biyu a gaba ta ta a tsakiya sai wasu biyu a baya duk masu tsaronta, sanin ta fad’a musu inda zasu yasa babu b’ata lokaci suka isa babbar bankin.

Da sauri suka bud’e mata k’ofa ta fito ita ma cikin azama, hud’u ne suka bi bayanta d’aya na rik’e da takardun data fito dasu, suna shiga ofishin kamar dama ita suke jira saboda yanda ta same su, bayan sun gaisa ne sun zauna suke d’ora mata da abinda suka tattauna jiya, a gaban babban alk’ali da shaidu ta saka hannu aka juye mata kud’in a wani account, ana idarwa ta mik’e ba tare data bawa mazan hannu ba sai mata ta sake barin wajen.

Suna cikin mota tana rubutu a check ta kalli s茅curit茅 d’in da suke tare dashi a gaba kusa da driver tace “Ka tsaya a gidan farko da muka fara had’uwa dashi na marayu.”

Abun maganar dake kunnenshi ya danna ya fad’awa sauran motocin, haka kuwa akayi a gidan marayu da suka tsaya ita kad’ai ta shiga.

Sanda ta basu enveloppe d’in kud’i sunyi murna sosai tare da mata godiya da addu’a, fitowa tayi da hanzari ta baro wajen sanda wasu suka fara cewa zasu d’auki hoto da ita wasu kuma na tambayar wacece, tasan abune mai sauk’i su santa amma ba yanzu take so su ganeta ba, da haka Sarah ta dinga rabar da kud’in nan ba tare data yarda sun rufe mata ido ba, manya manyan kyauta ta dinga yi dasu ta hanyar rabawa a gidan gajiyayyu marayu masu neman tallafi da sauransu. A k’arshe wani babban ofishin gwamnati taje aka had’a da wakilian da zasu iya gabatar mata da ginin babbar library a k’asashen nan biyu Niger da kuma Nigeria, an karb’a tare da mata alk’awari da karb’ar duk wasu bayanai da za’a iya tuntub’arta ta hanyarsu dan tasan abinda ke wakana.

Da yamma lis suka koma gida inda ta samu su Joseph suma sun idar da nasu aikin data saka shi, duka ma’aikatan ta tara a babban falon mahaifinta bayan tayi wanka ta ci abinci, duk sunyi cirko cirko suna jiran suji me zai faru?

Saida ta mik’e tsaye tana kallonsu tace “Da fari zan fara baku hak’uri akan abinda zaku ji daga bakina, nasan akwai wanda ba lallai ya masa dad’in ji ba, amma kuyi hak’uri dole ce ta kawo haka, kusan dukaninku nan kun jira tare damu a gidan nan kuna aiki a k’ark’ashin ni da mahaifina, wasunku sun san mu musulmai ne, hakan ne yasa bayan rasuwar mahaifina daga jiya sanda na zo zuwa yau duk na kyautar da dukiyarshi, domin kashi 10% ya tabbata bana halak bane, ni kuma addini na ya haneni da cin haram, wannan dalilin ne yasa na kyautar da komai ga mabuk’ata, a yanzun abu biyu ne kawai ya rage na dukiyar mahaifina, na farko kampanin motocinmu na Renault motor’s, na biyu kuma wannan gidan da muke ciki, wannan gidan ban kyauta dashi bane saboda mahaifina ya jima da tura min takardunshi yana d’aya daga cikin abinda ya samu na halalinshi, kampani kuma ban kyautar bae saboda ina so kaso 50% na ribar da kampanin zai dinga samu zata zamu taku ne.”

Kallon kallo aka shiga tare da tambayar juna sai ita ce ta d’ora da fad’in “Yeah, zaku daina aiki a gidan nan a yanzu, shiyasa nake so kaso hamshin na ribar da kampanin ke samu a dinka kasafa muku ita kuna d’aukar nauyin kanku da iyalenku, dan nasan dayawa daga cikinsu da aikin nan ne suka dogara.”

Wasu abun bai musu dad’i ba ko kad’an, zama da ita babu albashi ma abu ne da zasu iya shi cikin dad’in rai da farin ciki, yanda bata d’aukarsu ma’aikatanta ma yafi musu dad’i fiye da komai, babu wulak’anci babu hantara da kyara, dan daga cikin adalcinta ne ma yanzu har tayi musu wannan dubarar, tunda ai ba aiki bane na dindindin ko na gwamnati dake da inshora, amma saboda kyautatawa shine ta musu wannan tagomashin.

Wasu kuma sunji dad’i dan ko ba komai kason da zasu samu na yanzun zaifi wanda suke samu a duk watan, hakan kuma zai iya basu damar tsayawa da k’afafunsu ma suma har su d’auki nauyin wani, kuma a sanin da suka mata tana da ilimi sun san tana iya zamar da abun na dindindin ta hanyar ko bayan ransu iyalinsu zasu ci gaba da karb’ar kud’in, kamar dai ma’aikatan kampanin suma masu aiki a cikinshi.

Sanda suke ta tattaunawa k’asa k’asa ta matso kusan babban s茅curit茅 d’in mahaifinta ta mik’a mishi wasu makullai tare da fad’in “Amana d’aya ce John Wayne, mahaifina ya yarda da kai fiyr da kowa, kana da amana da sirri haka Abhi ya tab’a fad’a min, wannan makullan office d’ina ne, kaje daga yanzu kai ne zaka ci gaba da jagorantar wurin a matsayin da nake, i know u are graduate.”

Da yanayin da shi dai baya ce yaji dad’i ba ya karb’a yana kallonta yace “Nagode madame abisa wannan yabon, amma taya zan iya gudanar da kampanin nan kamar yanda kikeyi?”

Murmushi tayi tace “Abune mai sauk’i, kana da basira da ilimi, suna nuna maka zaka fahimta cikin sauk’i.”

Joseph ne ya katsesu da fad’in “Madame.”

Juyawa tayi ta kalleshi a tsanake tana sauraranshi, cikin nutsuwa yace “Kina nufin duk kin rabar da dukiyar da kika mallaka a wurin mahaifinki saboda ba halak bace?”

D’aga kai tayi tace “Yes.” Jinjina kai yayi ya gyara tsayuwa yace “Kuma addininki ne ya koyar dake haka?”

Gyara tsayuwarta tayi tace “Hakane Mr Joseph, a addinina ba komai bane kake iya kaiwa bakinka ba har sai ka tabbatar da hallacinshi akanka, hatta da abinci akwai wanda ya dace ka ci da wanda bai kamata ka ci ba, to ina ga dukiya kuma?”

Sake jinjina kai yayi ya juya ya kalli matarshi Sandra sannan yace “In dai hakane ina so na shiga addinin nan nima, dan na fahimci akwai haske a cikinshi, addinin da zaisa kiyi fatalin da tarin dukiyar da dubannin mutane ke son kasancewa a matsayinki, lallai ba k’aramar shiriya bace a cikinshi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button