SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Sosa kai ya shiga yi ya rasa me zai ce mata sai wani “Amm..eh..na..in.”
Murmushi kawai ta sake mishi tace “Ok i get it, bye.” Rab’ashi tayi ta wuce sai kuma ya bita da kallo, to fa daga ranar kawai ya juya ya koma yace ba zai iya ba shi, ran Kabeer ya b’ace inda shi kuma yake ganin dole yayi komai da gaggawa kafin shugaba ya saka masa ido.
Lokaci lokaci ya kan zo mata da sunan ziyara ya zo ganinta, zai sauka a masaukinta suyi hira, idan ya tashi tafiya zai bata kud’i amma bata tab’a karb’a ba sai tace tana da komai, haka zai tafi da cewa saiya sake dawowa ganinta, ita kuma hakan na mata dad’i dan tasan ko Abhi ke raye haka zai mata shima.
**********
Abun kamar da wasa sai gashi yanzu duk wani abu dake fitowa daga lambun nan nasu yana pakejin zuwa yanayin daya dace, saida ya salwantar da abubuwa da dama kafin ya samu siyo inginan da zasu mishi aikin nan daga k’asar waje, yanzu haka mangwaro lemunshi ake wanda ake bugashi da sunan daya zab’a da kanshi ana fitar dashi har sauran garuruwa, tumatur ma haka ake markad’ashi ana sakawa a gwangwani ana siyarwa, sauran kayan kuma ana sakasu a leda mai sinadarin da ba zasuyi saurin lalacewa ba ana fitar dasu birane, cikin hukuncin ubangiji sai abubuwan suka karb’u a cikin wata hud’u suka fara shigo mishi da kud’in da baiyi tsammani ba. A gona kuma sosai ake nomar gyad’a da hatsi suma ana sarrafasu ta hanyar data dace dasu, kafin kace kwabo da kud’ad’en da suka fara shigowa saiya kafa wani kusuwanci a gefe guda kusa dashi wanda yake so, dandanan saiya samu damar k’arasa gininshi har aka fara shirin komawa bayan walimar daya shirya dan godiya ga Allah.
Ya gama shiryawa yana daidaita zaman hularshi akanshi gaban madubi, da sallama ta shigo d’akin cikin kasarshi, cak ta tsaya tana tsinkayenshi, bai amsa ba saboda baisan ta shigo ba, sai danna hular yake a kanshi da tunanin gyara mata zama, amma abinda bai fahimta ba zaman hular yayi harya fara b’ata karin nata, ajiyar zuciya ta sauke dan izuwa yanzu wannan tunanin mai nisan zango da mijin nata keyi ya fara hawa mata kai, sau da dama gashi zaune sai kaga yayi shiru yana kallo wuri d’aya, wani lokacin a cikin dare zata farka wata buk’atar saita ganshi zaune, mutumin mai ibada amma yanzu ya k’ara zab’ar shiru da tunanin a madadin fad’awa Allah damuwarsa, dama ba mutumin magana bane ko can dama, amma yanzu shirun nashi yayi yawa fiye da da. Ita kanta idan ta mishi magana sai yace ba komai kawai, wani lokacin idan tace tana son magana dashi ma tana son taji damuwarsa sai kawai ya b’ige da sumbatarta har abun yayi nisa.
A hankali ta k’arasa shi ta tsaya ta kai hannunta ta gyara masa hular, da sauri ya dawo hayyacinshi tare da kallonta, murmushi ya sakar mata yace “Kun shirya?”
Kafeshi tayi da ido tace “Yaya Salahadeen lafiya? Me yake damunka?”
Juyawa yayi ya kalli madubin kamar ba zai amsa mata ba ya d’auki turare ya fesa sannan ya kalleta yace “Ba komai, muje.”
Da kallo ta bishi har ya fita daga d’akin, suna fitowa tare dasu Mama da Iffa suka fita, da kanshi ya tuk’asu a mota har suka isa unguwar A.D.S d’in a tanfatsetsen gidan da sanda duniya ke rud’arsa yake matuk’ar sha’awar zama cikinsa, amma yanzu duk wannan burin ya wargaje, ji yake ma akwai gurbin daya rage a rayuwarshi da bai cika shi ba dan haka gidan bai dace dashi ba. Sun samu har an fara wa’azi nan suka zauna, yana zaune dai a wurin kuma yana jin wannan kururuwar ta lasipika a cikin kunnenshi, amma me ake fad’a? Akan me ake magana? Duk bai sani ba, tunani da hankalinshi na wani wurin.
Yasan inda take, yasan me take a garin? Sai dai tashin hankalinshi ya k’aru ne sanda Richard ya sanar dashi ya gane akwai mai bibiyarta, sannan Kabeer na zuwa har masaukinta, hakan shine babbar matsalarshi a yanzu, wannan ita barazanar da yake fuskanta, baisan miye nufinsu akanta ba, me zasu iya yi mata a gaba? Rashin sanin haka shi ke wahalar dashi. Ya yarda yana da taurin kai da dagiya akan k’i fad’i, dan har yanzu ma bai yarda abinda yake ji a game da ita daga zuciyarshi yake fitowa ba, kawai yana d’auka ne a matsayin tun farko shi ya d’aukarwa kanshi alhakin kula da ita shi yasa yanzu har abun ke damunshi, sai dai a yanda yake ma al’amarinta rik’on sakaina kashi kuma ya jima da fahimtar abun ya wuce haka, lokuta da dama idan yayi mummunan mafarki akanta yakan tashi a tsorace yana kiran sunanta a bakinshi, wani lokacin ko tafiya yake idan yana tunani akanta yakan kira sunanta ya tambaya me yasa ta tafi?
An gama komai lafiya kamar yanda ya tsara ya kuma yi fatan kasancewarshi, da taimakon bak’in da suka zo aka k’ara share gidan aka goge sannan suka nemi inda ya zama mallakin kowa dan huta gajiya, da sallama ya shiga d’akin Mama ta amsa mishi, wuri ya samu ya zauna sai kuma yayi k’asa da kanshi kamar me nazarin wani abu, a tsanake ta kalleshi tace “Salahadeen?”
Da sauri ya d’ago kamar wanda aka tsikara yana kallon maman, a hankali tace “Lafiya?”
Girgkza kai yayi yace “Ba komai mama, na zo dubaki ne kawai.”
Murmushi tayi tace “Lafiya lau nake, kaje ka kwanta kaima ka gaji fa, Allah yayi albarka.”
A hankali ya yunk’ura zai mik’e sai kuma tayi saurin cewa “Baka ji?”
Komawa yayo ya zauna yana kallonta, cikin kokonto tace “D’azu da muna duba d’akunan nan sai muka ga wani d’akin shima da kaya ciki na alfarma kamar dai d’akin Farha, amma kuma daka nuna mana sai ka wareshi, d’akin waye shi?”
Wani irin bugawa yaji gabanshi yayi da baisan dalili ba, a hankali ya furzar da wani iska, har ga Allah sanda ake aikin gidan haka kawai ya samu kansa da sawa a cire wani d’akin, sanda yake zuba kaya kuma ya dinga saka komai irin na uwar gidanshi, to kenan waya fitar ma da waccen d’akin? To ka nemo mai shi?
Kallon mama yayi sai kawai yace “Mama ni zanje na kwanta, ba fa komai wallahi.”
Murmushi tayi har ya mik’e tace “Salahadeen kar dai ka ce min baka saki Saratu ba?”
Da sauri ya juyo yana kallon Mama, cikin rashin gaskiya ya shiga in’ina yana fad’in “Mama..wa..ce maga..na ce ..kuma wannan?”
Hararenshi tayi tace “Gidanku ma, ka fahimce ni sarai iskanci ne kawai.”
Murmushi yayi ya sosa k’eya yace “Mama, zamuyi magana da safe.”
Ya juya mama ta sake cewa “Salahadeen ya kamata fa ka sawake mata nauyin nan dake kanta, kar kasa kaje tayi ta d’aukar alhakin aure bata sani ba, duba kaga fa yanzu wata hud’u kenan, idan fa tana can tana soyayya da wasu samarin me kake tsammani?”
Kallon Mama yayi ba tare da tunanin abinda ya fad’a zai fito fili ba yace “Ba zan iya sakinta ba mama.”
Girgiza kai yayi yace “Zamuyi magana mama.” Da sauri ta katseshi da cewa “To tunda ba zaka iya sakinta ba ka dawo da ita mana, waccen d’akin ai saita zauna a ciki tunda babu mai shi.”
Wata dariya ya saki wacce ya manta rabonshi da irinta ya girgiza ya juya ya fita yana fad’in “Mamar Saratu kenan rigima.”
Ita kanta dariyar tayi tace “D’an hancin uwa zakayi bayani ne ma, wai ni zai ma wayo.”
Mekka
Yanda ta saba shiryawa yau ta samu nak’asu a cikin kuzarinta, gashi kuma sunyi magana da Kabeer zasu had’u wani babban mall, dan ya mata k’orafi ba zai iya zuwa masaukinta ba yana jin wani d’ar, bata mishi musu ba tace zata zo ko sallah isha’i ba zata tsaya ba saita koma gida, tana gama shiryawar ta mik’e tsaye ta saka beby hijab d’in ta, k’urawa kanta ido tayi a madubin tana kallo, kamar wacce aka zarewa rai haka tayi shiru, ta jima a haka kafin ta nisa tace “Mr. ka manta dani gaba d’aya, gashi ka karb’e min komai da nake da kuma kana can kana rayuwa da matarka.”