SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Wani d’an tsaki taja ta wuce tana fad’in “Forget it Sarah, facing ur future.”
Fita tayi yanda mafi aksari tafi hawa matakala yau ta kasa kawai ta shigq lift, cikin sanyi take tafiya harta samu taxi ta shiga, a motar ma saida zuciyarta ta fizgeta ta tuna dashi da tattaunawarsu sanda suka je k’auye, ta yarda ita kanta k’auyen nan ya shiga tarihin rayuwarta yanda ba zai tab’a goguwa ba, haka kawai wani lokacin sai taji tana kewarshi tana so ya kasance kusa da ita tare da Mamie, har ta kan zubar da hawaye wani lokacin ta dinga kiran sunanshi, daga bisani kuma sai tayi tsaki taji haushin kanta na damuwa da wanda baisan ma tana yi ba. Saida ta ga taxin ta tsaya ne ya tabbatar mata ta zo wurin, fita tayi ta biya kud’inta ta shiga cikin kasuwar.
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:17 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA GA
_DUK_
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
3锔忊儯3锔忊儯
A wurin d’an ci da sha n wurin suka zauna, a tsanake ya kalleta yace “Princess babu wata matsala? Kin tabbatar kina jin dad’in zaman nan wurin?”
Murmushi tayi tace “Sosai uncle, ina jin dad’in zaman nan fiye da gida ma, ina son wurin sosai.”
Jinjina kai yayi yace “To ki fad’a min me kike so na miki, amma karki ce min ba komai dan ba zan yarda ba, kullum haka kike fad’a min princess.”
Dariya tayi tace “Uncle ba komai, duk abinda zaka bani ba zai kai farin cikin da nake samu ba a du sanda ka zo wurina, ina jin dad’i sosai akan haka uncle, Allah ya saka maka da alkairi.”
Murmushi yayi yace “Kenan ba kya buk’atar komai?”
Cikin sauke ajiyar zuciya tace “Yes uncle, ina da kud’i sosai a jikina.”
Cikin kafeta da ido yace “A ina kika samu bayan duk kin kyautar da abinda kika mallaka?”
Kallonshi kawai tayi tana murmushi ba tace komai ba, wani kallon gefen wutsiyar ido ya mata dan ya fahimci akwai abinda take b’oye mishi? Tattara wayoyinshi yayi yana mik’ewa yace “Princess d’in Abhi ni zan koma, kamar yanda na saba zan sake dawowa ganinki.”
Mik’ewa tayi tana “Nagode uncle, Allah ya kiyaye hanya.”
Tare suka fita daga ciki suka nufi wajen ajiyar motoci, ya shiga driver ya jashi ta juya zata koma inda ita ma zata samu taxi, duk da taji motsin mutum a bayanta amma bata juya ba tunaninta masu d’aukar motoci ne ko ajewa, kamar daga sama kawai taji an rufe mata baki da hanci ta baya ruf, daga nan kuma me ya faru ina take ya akayi? Duk bata sake sani ba tsawon lokaci.
D’aki ne mai duhu sosai wanda baka iya ganin komai, wata k’aramar taga ce acan sama wanda take nuna rufin d’akin nada tsayi sosai, tsaye suke akanta inda shugaban k’ungiyar ya kalli Kabeer yace “Kayi aiki mai kyau Kabeer, kamar yanda ka cikawa k’ungiya alk’awarinta kaima k’ungiya zata faranta maka rai.”
K’waryar dake hannunshi mai ruwan tsafi a ciki ya shiga kwarara mata a jiki, sam bata motsa ba ko ta bud’a ido, saida ya juye mata ruwan duka ya d’auki wani abu mai kama da gashi ko jelar wata dabba, a jikinta ya dinga goga abun wanda ya mik’e tsaye cirr, a tsorace ya d’ago ya kalli Kabeer yace “Ban gane ba? Ya akayi haka ta faru?”
Cikin rawar jiki da fatan kaucewa duk wata matsala yace “Lafiya? Me ya faru shigaba?”
Gyara tsayuwa yayi ya rik’e k’ugu da hannu guda yace “Ya akayi yarinyar nan ta samu ciki?”
Waro ido yayi yace “Ciki? Sarah!”
Girgiza kai yayi yace “Wallahi ban sani ba shugaba, amma kuma tayaya? Ban san Sarah da yan biye biye ba.”
Tsaki yayi shugaban yace “Ba kace an d’aura mata aure ba?”
“Eh hakane, amma na ga ai…” Dakatar dashi yayi da fad’in “Ya isa, ka kaita can gidan saman dutsi a ci gaba da ajiyeta, ba zamu tab’ata a yanzu ba har saita haife abinda ke cikinta, riba biyu ce garemu zamu tsira da jininta sannan abinda ta haifa zai zama ganimar k’ungiya.”
Jinjina kai yayi yace “Angama shugaba.” B’acewa shugaban ya fara yi shima ya dafa Sarah ya b’ace tare da ita.
Bayan awa uku ta farka daga wannan bacci mai kama dana mutuwa, jin kanta ya mata masifar nauyi ta kasa tashi yasa ta fad’in “Alhamdulillahillazi ahyana ba’ada ma’ama tana wa ilaihir nushur, A’uzu billahi mina shaid’anir rajim, hasbunallah wani’imal wakil.”
Sake bud’a ido tayi a hankali, da k’yar ta iya gane duhun dake cikin d’akin, tana ganin wurin da bata sani ba ta zabura ta tashi zauna, juye juye ta fara yi tana so ta tashi a baccin da take ko kuma ta gane ina take, cikin siririyar murya ta fara anbaton “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, la’ilaha illa anta subhanaka inni kumtum mina zallimin.”
Tsaye ta tashi tana ta birgima cikin rigarta tana ta juyawa, duk lalubarta bata iya gano k’ofar d’akin ba, cikin d’aga murya ta fashe da kuka tana fad’in “Da mutum a wurin nan? Da mutum anan ne? Dan Allah ku min magana, ku fad’a min me nakeyi anan? Waya kawo ni nan?”
Haka ta gaji da kwaroroto ta koma ta zauna ta had’a kai da gwiwa tana ta jero addu’o’i. A lokacin suna tsaka da zamansu suna kallonta ta majigin bango, sanda ta fara karanta addua’r tsari kama daga ayatul kursiy aywa amanar rasul sai wurin ya fara jijjiga dasu kamar ana girgizar k’asa, duk tashin hankali suka shiga suka rud’e suna neman kifewa a wurin, gashi suna son barin wurin amma abun ya gagara, shugaban ne ke fad’in “Wai me ke faruwa ne? Miye wannan abun kuma?”
Sauran har da Kabeer ne suka amsa da “Bamu sani ba shugaba, kawai ka fitar damu daga wurin nan.”
Wani dattijo ne yace “Nifa ina ga kamar yarinyar can da aka kawo ce, ku lura da abinda take fad’a mana.”
Kabeer ne yace “Tabbas, wanda ya fimu k’arfi take ambata kuma ba shakka zai ceceta dan ta kirashi a inda ya dace, indai har bamu rabu da yarinyar nan ba shugaba to ka sani lokacin tab’ewarmu yayi.”
Wata tsawa ya daka mishi da fad’in “Kaiiiii.”
Nuna shi yayi yana fad’in “Har a nawa take da zata gagaremu, bata isa ba ko dame take tunk’aho, zamu sha jininta kamar yanda muka sha na ubanta sannan musha na abinda ke cikinta ma.”
Da k’yar wani tsoho ya tashi tsaye yana ta k’ok’arin tsayawa da k’afafunshi yana fad’in “A’a shugaba kar a matsanta fa, alamu sun nuna yarinyar nan ba haka kawai take ba, ni ina ganin me zai hana a mayar da ita inda aka d’aukota, a jira ta haihu sai a sake dawo da ita, duba da tunda muke a k’ungiyar nan wani abu makamancin haka bai tab’a faruwa ba sai yau.”
Kabeer ne yace “Gaskiya ne, dan in dai har zamu zauna da ita a haka to fa mune zamu mutu a banza, kunga kenan mu bamu samu abinda muke so gareta ba kuma k’arshe mu mutu.”
Nan shugaban ya amince ba dan ya so ba, amma saida ya kafawa Kabeer sharad’in cewa ya kula da ita sosai kar a samu matsala, in kuma ba haka ba to ya kuka da kanshi, amincewa yayi d’ari bisa d’ari kafin sukayi k’ok’arin barin wajen da k’yar.
Tabbas tana zaune taji kamar an bud’e k’ofa an shigo duk da bata san ta ina k’ofar take ba, saiji tayi kawai ta sake zubewa kamar somammiya a wurin, daga nan bata sake sanin me ya faru ba sai farkawa tayi ta ganta a d’akinta na masauki, yanda taji bata iya tuna komai sai abun ya mata kamar mafarki ne, sai kawai ta tashi ta cire kayanta ta shiga wanka, data fito saida ta had’a zallar tea tasha kafin ta kwanta tana ta so ta tuno ko ta hasasho abinda ya faru, kawai jin abun take yi sai taga dai tabbas mafarki ne tayi, to amma in mafarki ne ai bata dawo masaukinta ba bayan sun had’u da uncle kafin abin ya faru. A hankali sai taji zazzab’i ma na neman rufeta, tashi tayi ta samu maganin zazzab’i a drower ta d’auki gorar ruwa a k’aramar fridge tasha ta dawo ta kwanta, sai dai duk ta fara tunanin komawa wajen kwanan makaranta watak’ila zata fi samun tsaro acan.