SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA GA
_DUK_
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
3锔忊儯5锔忊儯
Da asuba ya fito zai tafi masallaci haka su Zeid, jin babu motsin mama yasa shi nufa d’akinta dan dubawa, k’wank’wasawa yayi sai yaji k’ofar ta bud’e alamar ba rufr take ba, siririyar sallama yayi kuma yaji shiru ba’a amsa ba, har sau uku amma babu amsa ba sai yayi tunanin bacci ne ya d’aukesu, turawa yayi ya shiga yana sake jefa wata sallamar.
A take bugun zuciyarshi ya canza inda gabanshi ya shiga dukan uku uku da k’arfi, wani abu yaji ya tsirga masa sanda baiyi tsammani ba, bccinta take da gani alamar gajiya ta bayyana tare da ita, dan ko motsi ba tayi ba sai sauke numfashi, bras d’inta kalar shud’i ta kamata irin mai rabin nonuwa ce (demi sains), cibiyarta acan ciki ta shige sai mararta daya k’urawa ido, babu wani abu da zai nuna maka wai akwai ciki anan, jin k’arar ruwa a ban d’aki ya tabbatar mishi Mama ce a ciki, a hankali ya lallab’a yana waigen ban d’akin ya k’arasa kusanta, lusmhe ido yayi cikin rawar hannu ya kai hannunshi kan mararta, a hankali ya d’an shiga tausa marar ta ta kamar mai binciken lafiyar abinda ke cikin. Shi dai babu wani abunda yaji daya wuce tauri kawai a wurin, d’an tab’e baki yayi ya d’auke hannu a hankali ya juya ya fita, saida ya fita ya tambayi kanshi “To a ina cikin yake? Anya ma gaskiya ta fad’a kuwa?”
Wata zuciyar ce tace mishi “Me zaisa ta maka k’arya kuma? Da gaske ne mana ai bai girma ba.”
Mama na fitowa ta tasheta dan tayi sallah, sanda tayi alwala ta saka rigarta ta kabbara sallah saida mama ta kalleta duk da a salla take ita ma, yanda ta jawo k’ira’ar sutarul a’ala abun ya birgeta sosai, sai taji har wani tsuma take saboda tana jin ainahin abinda surar ke magana akai ana bawa kowane harafi hakk’inshi, saida tayi salatul fijri sannan tayi sallah subah, ta jima zaune tana azkhar na sabah, har saida Salahadeen ya shigo da sallama, zaune yayi kan kujerar dake k’ofar d’akin yana kallon Mama yace “Mama ina kwana?”
A hankali ta amsa mishi da “Lafiya lau Salahadeen, antashi lafiya?”
“Lafiya lau.” Ya amsa dashi kafin tace “To yayi, Allah yayi albarka.”
Kallon Sarah tayi da kamar bata san da shigowarshi ba yace “Ke baki iya gaisuwa ba?”
A hankali ta juyo ta kalleshi tace “Watak’ila al’adarku ce mace ta gaishe da namiji, amma idan zakuyi koyi da sunnar annabi Muhammad (S.A.W) ne ai shi yake shiga ya gaishe da matanshi a kowace safiya, shi yake zuwa yaji lafiyarsu ya suka tashi, kaga kuma baka kaishi daraja ba da matsayi, sai dai kuma idan zaka nuna min ni matar visa ce ba matar so ba.”
Duk ido suka zuba mata suna kallo har mama da bata ji me tace ba bayan sunan annabin rahama da taji ta ambata, wani murmushi yayi a hankali yace “Nagode da tuni, zan kuma yi k’ok’arin d’abb’ak’a sunnar nan.”
Juyar da kanta tayi tare da mik’ewa daga kan sallayar ta nad’e zata aje taji yace “Ya kika kwana to da kuma..”
Juyowa tayi tace “Lafiya lau.”
Jinjina kai yayi ya mik’e zai fita tace “Nan da awa shida fa jirgi na zai tashi insha Allah.”
Juyowa yayi kamar wanda bakinshi ya sub’uce sai kawai yace “Babu inda zaki je, umarni ne kuma ba shawara ba.”
Har ya juya zai fita da sauri tace “Ban gane babu inda zanje ba? Kuma har da wani cewa wai umarni ne, to a matsayinka nawa zaka bani wannan umarnin?”
Kanta yayo kamar zai daketa da niyyar tsorata ta yana fad’in “Bari na nuna miki a aikace.”
Da gudu ta koma bayan mama tana sakin ihu tana fad’in “Mamieeee kin ganshi fa.”
kallonshi Mama tayi tace “Karka yarda Salahadeen, kaga fice ka bar d’akin nan.”
Hararan Sarah yayi ya nunata da yatsa yace “Zamu had’e ne zaki san wa kika fad’awa haka.”
Daga nan bayan Maman da take ta zuro harshe ta bishi da gwalo tana fad’in “Yelupp, ina da uwa babu mai tab’ani.”
Mama kanta saida ta saka dariya shima fita yayi yana murmushi da girgiza kai, yana fita ta cire hijab d’inta ta koma ta kwanta kafin lokacin tafiyarta yayi dan tasan ya fad’a ne kawai.
Yana fita shima ya koma d’aki ya samu Farha har ta sake kwantawa, zaune yayi yana kallonta yace “Zo ina so zamuyi magana.”
Zaune ta tashi ta kalleshi tace “Magana kuma yanzu yaya Salah?”
Lumshe ido yayi alamar eh, saukowa tayi ta zo kusanshi ta zauna tana fuskantarshi, saida ya nutsu sosai yana kallon fuskarta yace “Farhanatu miye k’addara ne a rayuwa?”
Kallonshi tayi sai kawai taji gabanta ya fad’i, saida ta gama kallonshi tsaf tace “Yaya Salahadeen k’addara a cikin addininmu ita ce cikon imaninmu, tana daga cikin rukunan imani guda shida, idan har zaka yarda da guda biyar amma ka kasa yarda da k’addara hakan zai iya shafar imaninka ba kad’an ba, watak’ila ma dalilin haka kayi shirka kaga kenan ka ruguza da addininka gaba d’aya.”
Jinjina kai yayi alamar gamsuwa yace “K’addara kaso nawa ce?”
Kai tsaye tace “Kaso biyu ce, k’addara mai kyau da kuma marar kyau, Allah yakan jarrabi bayinshi da k’addara marar kyau dan ya gwada imaninsu, idan sukayi hak’uri suka rumgumi k’addararsu sai kaga sun ci riba da kuma nasara, ko da ba’a zahiri suka fito maka ka gani ba zai zama dole dai ka samu sakamako mai kyau in har da iklasi mai kyau ka rumgumi k’addarar nan.”
Jinjina kai ya sake yi yace “Alhamdulillah Farha, daga bayanan da naji daga gareki saina samu k’warin gwiwar fad’a miki ba tare da wani shakku ba, ki sani Farhanatu na ambaci sunan k’addara ne a abinda zan fad’a miki duba da yanda ku mata kuke girmama wannan lamarin zuwa matakin da bai kai can ba, amma inhar kikayi hak’uri kamar yanda kika fad’a to insha Allahu zaki samu sakamakonki mai kyau a gobe kiyama, sannan nima na miki alk’awarin samun duk abinda kike so a gidan duniyar nan daga gareni inhar bai fi k’arfi na ba.”
Ita dai ta zuba masa ido kawai tana kallonshi da sauraronshi, a hankali ya kalleta yace “Jiya da dare Sarah ta shigo garin da wata muhimmiyar magana, kinsan me ta zo dashi?”
Tunda ya ambaci Sarah taji jikinta yayi sanyi hannayenta sunyi nauyi gabanta ya shiga dokawa da k’arfi, kasa motsa bakinta tayi sai kallonshi kawai da take, cikin nutsuwa yace “Ciki ne da ita, tana d’auke da ciki na wasu watanni.”
K’walla ce taji ta cika mata ido kamar zatayi kuka, kallon juna suka shiga yi ko k’yabtawa babu, a hankali ta d’aga labb’anta tace “A..matsayinka…nawa,,,ta fad’a maka?”
Kallonta yayi yace “A matsayina na uban abinda ke cikinta mana.”
Wata zabura tayi ta mik’e tsaye tana jinjina kai tace “Da kyau, lallai yaya Salahadeen yau ka tabbatar min kai namiji ne, yanzu ko kunya baka ji ba ka tsaya gabana ka kalleni ka fad’a min karuwarka na d’auke da cikinka? Da fari nayi shiru na k’yaleku kuyi masha’arku saboda ganin ba ni za’a tarawa zunubin ba, amma yanzu ta zo har gidana ta kawo min maganar banza, lallai yau babu mai bacci a gidan nan.”
Juyawa tayi zata fita ya rik’o hannunta ya dawo da ita baya yana fad’in “Farha kina da hankali kuwa? Bai kamata ki bari kishi ya rufe miki ido ba fa, ni ne ma ke da karuwar?”
A hassale tace “Kai d’in, k’arya nayi ba karuwarka bace? Wallahi ka bani mamaki daga kai har Mama da take biye muku kuna shirya mata wannan tatsuniyar, amma duk ba laifinku bane dan kunga Abba baya raye ne shiyasa, da yana da rai ai ba zaku munafurceshi haka ba bare har Maman ta goyi bayanku a dinga cin zalinaa…”