NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Wata k’ara ta saki tare da fad’awa kan kujerar data tashi a kanta tana dafe da kunci, saida ya d’ora k’afarshi kan kujerar kusa da ita yanda ba zata samu damar tashi tsaye ba yana kallonta cikin wani yanayi da bata tab’a ganinshi ciki ba, nunata yayi da yatsa yace “Ba tsoronki yasa nake k’yaleki ba, bakin mahaifina ne ke min shamaki da caccanza miki kamani, amma akan mahaifiyata wallahi zan iya sab’awa da uban ko waye a garin nan, Farha baki san waye Salahadeen ba, amma ita Sarah data sani duk iskanci da tsiwarta tana shakkata, dan ni iskanci na ba a k’asar haihuwata nayi ba, saida na keta hazo a wata k’asar da ake ji da gaggan shed’anu sannan na darza nawa kalar hatsabibancin, karki d’auka duk zaman da nayi a k’asar waje aiki nake da har na wadataku da abun more rayuwa, dan haka haka kiyaye kafin ki kaini matakin da zan fasa kanki ki mace kuma har lahira.”

D’auke k’afarshi yayi yana kallonta tare da tank’wasa yatsunshi suna bada sautin k’as k’as yace “Sarah na da ciki kuma zata zauna a gidan nan ta haifeshi, idan akwai abinda kika isa kiyi kiyi dan Allah Farha a yau d’in nan ba sai gobe ba.”

Ficewa yayi ba tare daya sake kallonta ba ya nufi d’akinshi dake sama, gyara zamanta tayi tana d’auke hannu daga kuncinta tace “Ni ya mara saboda wata banza? Ba damuwa wallahi zai gani.”

Mik’ewa tayi ta d’auki jakarta da hijab ta saka ta fita daga gidan, saida tayi tafiya mai nisa ta samu mai adaidaita ya d’auketa, gidan k’anwar mahaifiyarta ya kaita, ko da Zulhatu ta ganta tasan ba lafiya ba, amma saida ta bari ta sallami yaranta sun tafi makaranta mai gidanta ma ya fita sannan ta samu ta zauna suna kallon juna tace “Farha me ya faru kika fito da safe haka daga gidanki? Ina fatan dai lafiya ko?”

Girgiza kai tayi ta fashe da kuka tace “Ba lafiya ba aunty, yaya Salahadeen da Mama kawai basa k’aunata yanzu, ni ba zan koma gidansa ba kawai ya sake ni tunda baya so na.”

Da sauri tace “Ke Farha! Hankalinki d’aya kuwa kike fad’in mijinki ya sake ki? Me yayi zafi haka?”

Nuna mata kuncinta tayi tana fad’in “Dubi fa ki gani aunty mari na yayi akan wannan banzar kod’add’iyar baturiyar.”

Da mamaki tsantsa tace “Baturiya kuma? Ba ta tafi ba tun yaushe? Me kuma ya kawo maganarta har ya mareki saboda ita?”

Cikin kuka tace “Aunty wai jiya ta zo da dare ni ko ganinta banyi ba ma, shine yake fad’a min wai ciki gareta kuma nashi ne.”

Sake fashewa tayi da wani kukan hakan yasa Zulha fara rarrashinta tana fad’in “Yi shiru kiyi hak’uri ke daina kuka, dan kina marainiya ai ba gata kika rasa ba, taya zai nemi had’aki da wata banzar baturiya, data tafi ba sakinta yayi kuma kwana nawa auren yayi da zai ce ya mata ciki, ke ni ban yarda da mijin nan naki ba, duk yanda akayi akwai wani abu a tsakaninsu dama rainin hankali ne kawai.”

Cikin shagwab’a tace “Shiyasa nace ba zan koma ba aunty, da shi da mama munafurtata kawai suke suna b’oye min wani abu, inba rainin hankali ba ni ina tare dashi watanmu nawa banyi cikin ba sai ita saboda yafi sonta dama.”

Dafata tayi tace “A’a Farha maganar ba zaki koma ba bata ta so ba, hak’uri zakiyi ki koma gidanki, dan rashinki a gidan yanzu Allah kad’ai yasan me zai faru, amma in suna ganin idonki wani abun ba za ayi shi ba, ke ma kuma zaki ga duk abinda ke faruwa ganin idonki.”

Kallonta tayi tace “Aunty kina so naje naga abinda zai d’aga min hankali ne? Ni gaskiya ba zan iya ba.”

A hankali tace “A’a Farha ba abinda zai faru, can d’in dai shi yafi dacewa da ki zauna, kinga yanzu in na yarda kika zauna anan su kawu da Alhaji duk zasu ga laifina ne, kuma kinga ai mahaifinshi yace ko da rabuwa ta gifta ta tsakaninku bai yarda ki bar gidan nan ba sai dai shine zai fita ya barki, kinga kenan komawarki ta zama dole.”

Turo baki tayi tace “Yanzu aunty ya mareni ya mari banza kenan?”

Da sauri tace “A’a ina fa ya mari banza, ai ki bari zanje gidan da kaina na same shi na mishi magana.”

Sake turo baki tayi tace “Shikenan aunty zan koma amma ba yanzu ba sai anjima.”

Jinjina kai tayi tace “Shikenan, zaki ci d’umamen tuwo na zubo miki? Dan nasan dai baki ci komai ba kika fito.”

Cikin yamutsa fuska tace “Ban ci ba aunty, yanzu nasan su Mamuh sun fara gyara abun karin.”

Mik’ewa tayi tana fad’in “In zubo miki to?”

Girgiza kai tayi tace “Gaskiya aunty ki barshi ba zai shiga ba, haba na d’an saba da lafiyayyen abun kari.”

Hararanta tayi tana fad’in “Ummm! Lallai ma Farha kin min wulak’anci, wato kin saba cin k’wai da shayi da kaji ki kwanta ko.”

Dariya tayi tana rufe fuskarta tace “Haba aunty ba haka bane.”

Nan tayi zamanta kam har kusan k’arfe goma sannan ta shirya komawa gidan, ko da ta shiga ta samu babu kowa a falon, amma hangen k’ofar d’akinshi dake sama a bud’e yasa ta haurawa saman dan ganin me ya tsayar dashi bai fita ba har yanzu.

Awa uku bayan fitar ta Sarah ta tashi daga bacci, wanka tayi ta ciro wata sabuwar riga a yar jakarta tare da baby hijab d’inta, farin hijab ne fa jar riga sun mata kyau sosai kamar balarabiya, mama da kanta ne ta had’a mata abun kari tana ci ta kalli Mama tace “Mamie ina son komawa fa.”

Jim mama tayi dan bata san me zata ce mata ba, sai kawai tace mata “To tunda Salahadeen d’in yana ciki bai fita ki same shi sai ki fad’a masa.”

Jinjina kai tayi alamar to kawai ta ci gaba da cin abincinta, tana idawa ta mik’e ta kalli Mama tace “Mamie muje ki rakani.”

“Ina?” Mama ta fad’a tana kallonta da mamaki, cikin turo baki tace “Wajenshi mana mamie.”

Waro ido tayi tace “D’akin mijin naki zan rakaki Sarah? Ke bana son sakarci fa, to cinyeki zaiyi?”

Kamar zatayi kuka cikin sangarta tace “Mamiee ba mijina bane ba fa, idan na tafi ni kad’ai mugunta zai min.”

Cikin son b’oye dariyarta tace “Ai ko in kina son tafiya to kije ke kad’ai ni babu inda zani.”

Bubbuga k’afafu ta fara yi tana kukan shak’iyanci, da mamaki mama tace “Saratu daina jijjigar nan dan Allah, baki san abinda ke jikinki bane? Ba’a son doguwar kwaramniya.”

Tsayawa tayi tana tattare rigarta cikin shagwab’a tace “To ina ne d’akinshi?”

Nuna mata tayi daga nan cikin d’akin tace “Da kin hau saman bene d’akinshi ne kawai a sama.”

Saida ta nuna mama da yatsa manuniya tace “To Allah Mamie ki sani idan naje ya cuce ni akan d’an cikinshi zan rama.”

Juyawa tayi ta fita ba tare da alamar wasa ba a fuskarta, mama da tuni ta saki baki dan ta d’auka cewa zatayi zata rama akanta, dariya tayi tana girgiza kai tana fad’in “Allah ya k’ara dawwamar da farin ciki a rayuwarki, ina k’aunar yarinyar har zuciyata saboda akwai juriya.”

A b’angaren Sarah kuma tana zuwa ta k’wank’wasa tare da rangad’a sallama, daga ciki taji an amsa cikin wata irin murya data saka gabanta fad’uwa, shiru tayi ta kasa cewa komai haka shima daga b’angarenshi, jin shiru yayi yawa yasa yace “Shigo”

A hankali ta tura k’ofar d’akin ta shiga tana kalle kallen son gano inda mai d’akin yake, kan gado ta hangeshi kwance ruf da ciki babu riga a jikinshi k’afafunshi a sama yana d’an rawa dasu, kanshi akan pillow ya tangale hab’arshi da hannayenshi duka biyun daya kifasu, tsayawa tayi a hankali kamar mai tsoron magana tace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:17 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button