NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Ganin har ya d’auketa zai nufi k’ofa yasa Mama d’aga murya tace “Kai Salahadeen.”

Tsayawa yayi ya juyo duk a kid’ime ya kalli Mama, da sauri ta nuna shi tace “Haka zaka tafi asibitin babu ko riga a jiki?”

Da wani irin sauri ya lumshe ido ya sauke Sarah ya juya da gudu ya nufi d’akinshi, da sauri ta durk’ushe tana fad’in “Hasbunallah wani’imal wakil, la’ilaha illah, hasbunallah wani’imal wakil…”

Jin wani abu mai tauri tauri had’e da kamar ruwa ne ya danno mata da k’arfi ta k’asanta yasa ta tsayawa da addua’r da take ta saki kururuwar data firgita duk wanda ke cikin gidan. Yana tsaka da saka rigar a wuya ya ji wannan siririyar muryar ta daki kunnuwanshi cikin wani yanayi dake nuna mishi tana buk’atar taimakonshi, da sauri ya fito rigar a wuya bai k’arasa sakata ba ya sauko da gudu, Mama ya samu durk’ushe a kusanta rik’e da hannunta tana fad’in “Ki dinga addu’a Sarah kinji, bari ya taho muje asibiti a duba ki.”

Yana zuwa bai tsaya jin ta bakin kowa ba ya samu ya k’arasa zura rigarshi a gaba baya kuma a jirkice ya d’auki Sarah ya fita da ita da gudu gudu, jinin da Mama ta gani a inda Sarah ta durk’usa ne yasa ta sakin salati cikin tashin hankali ta juya ta bishi da gudu tana fad’in “Salahadeen kai, kai tsaya.”

Duk da yaji Mama amma bai tsaya ba dan yanzu haka da yake kallon fuskarta yaga gumin da take fitarwa sai yaji kuka na neman taho mishi, shi kam har ga Allah baya son kowa ya gane rauninshi akan yarinyar har ita kanta, shi kanshi baisan ya akayi ba kuma a yaushe yayi wannan sakacin har haka ta faru ba. Saida suka kai daf da mota kafin ya bud’e Mama ta k’araso tana kallonshi tace “Karka sauketa, jirani yanzu ina zuwa kaji.”

Cikin wata irin murya da baisan yayi magana da ita ba yace “Mama wahala take sha, bai kamata mu b’ata lokaci ba.”

Cikin damuwa tace “Ni nace maka ina zuwa ko.” Juyawa tayi ta koma d’akin da sauri sosai kamar zata fad’i, sake kallon fuskarta yayi izuwa yanzu kam a hankali take lumshe ido ta kuma dantse leb’enta na k’asa sosai alamar dai tana jin zogin, sanda ciwon ya sake murd’o mata da k’arfi sosai ta jawo wuyan rigarshi ta rik’e gam, cikin wannan masifar tashin hankalin ta furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, Sla, mr. mutuwa zanyi, mutuwa zanyi Slahadeen, ba zan iya jurar wannan rad’ad’in ba.”

Da sauri ya durk’usa tare da yin zaune gaba d’aya da ita ya d’orata kan k’afafunta kamar yanda uwa ke tallabe d’anta ta bashi nono, hannayenshi yasa ya shiga shafa fuskarta cikin tashin hankali da yanayi na jigatuwa sai gumi da yake shima kamar shi ke jin zafin ya shiga fad’in “A’a Sarah, ba zaki mutu ba yanzu, babu abinda zai same ki Sarah, zaki tashi kinji ko, zaki tashi Sarah ba zaki mutu ba.”

K’eyarta ya tallabo sosai ya rik’e ya had’a goshinta da nashi haka ma dogayen hancinsu suka manne inda numfashinsu ke gauraya, idonshi a rufe amma ita tana kallon fuskarshi sai hannunta da take ta sake jawo wuyan rigarshi, cikin wata tattausan murya yace “Please Sarah don’t go, i need u in my life, tu es tout pour moi, je ne peut pas vivre sans toi, dan Allah ka da ki tafi ki barni.”

Duk da tana cikin rad’ad’in ciwo sosai wanda ita kad’ai tasan me take ji, amma abinda ya fad’a mata yanzun ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen samar mata da kaso mafi tsoka na sauk’in da taji a daidai lokacin, ita kamta haka ta tsinci kanta da jin wani basaraken dad’i ya mamaye duka illahirin zuciyarta, sakin wuyan rigarshi tayi a hankali ta tallabo k’eyarshi ita ma ta sake manna fuskarsu, wani murmushi mai kama da kuka na wahala ta k’ak’aro mishi, lusmhe ido tayi a hankali ta d’ora bakinta akan labb’enshi, ba sumbata tayi ba sai tsotsawar da ta kusa tafiya da ranshi, yaji sak’on sosai kuma ya karb’eshi da hannu biyu, lumshe ido ya sakeyi shima yayi shiru yana jin yanda take tsutsar bakinshi cikin wani salo mai tafiya da imanin wanda ake wa.

Fitowar Mama ganin abinda ke faruwa sai tayi saurin juyawa ta basu baya gabanta na fad’uwa, a lokacin kuma Sarah ta ja wani numfashi ba tare data saki bakinshi ba, wani iska data furza mishi cikin bakin mai zafin gaske ya sashi bud’a ido, cikin idonta ya sauke nashi idon amma kuma nata idon a tsaitsaye suke sun kafeshi, da sauri ya jaye kanshi yana sake k’ura mata ido, a take wuyanta da idonta suka tafi luuuu sukayi baya idonta kuma suka rufe ruf.

Da wani yanayi ya k’walla kiran “Mamaa, Mammmmaaa.” Da sauri Mama ta juyo tayo kansu dan baisan tana nan tsaye ba, tana k’araso ta sunkuya tace “Lafiya…”

Da sauri yace “Mama bata motsi, bata motsi Mama ki tashe ta, Mama karta mutu dan Allah ki fad’a mata, wallahi idan ta mutu Farha ce ta kasheta ita ma saita mutu…”

Da sauri Mama ta rufe mishi baki tace “Tashi yi sauri mu kaita asibitin.”

Cikin hushi ya mik’e ya bud’a motar zai kwantar da ita yana fad’in “Saida nace muje asibiti Mama amma kika tsayar damu, yanzu gashi zata mutu a banza.”

Shiga Mama tayi ita ma suka rufe tana warware zanin data d’auko dan ta canzawa Sarah, shiga yayi shima yanda ya figi motar yasa Mama kasa wani katab’us, haka mai gadi ya bud’e musu k’ofar suka fita da gudu sosai, taimakon Allah ne ya isar dasu asibitin lafiya wanda Mama kanta ta sadak’ar, clinique Hamdala ce tafi kusa dasu dan haka anan ya tsaya, kasancewar asibitin kud’i ce da gaggawa da kulawa suka karb’eta wata ma’aikaciyar na tambayar katinta, Mama ce tace bata da dan haka tace ta biyota sai su yankar mata.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:17 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               3锔忊儯7锔忊儯

Tun lokacin da suka zo 11 ba tayi ba sai gasu har aka gama sallah azahar babu wanda ya fito yace musu ga halin da marar lafiyar ke ciki, sai dai a fito da takarda a bashi ace ya siyo, daga awannin kam da yake tsaye a wurin nan wata muguwar ragargaza ya wa aljihunshi, sai dai sam tunaninshi ba anan yake ba, yar amana kawai yake dubawa yana fatan ta kasance lafiya, kallo d’aya zaka mishi kasan baya cikin nutsuwarshi, dan ma sanda suka ga babu wani labari Mama ta tilasta mishi komawa gida ya canza kayan jikinshi ya dawo, sanda ya koma ne ma Farha da har yanzu take a tsorace gabanta na fad’uwa ta biyoshi suka taho, amma fa saida taji ina ma bata taho ba, dan a mota daga kallon da yake mata zaka gane kamar zai cinyeta d’anya ne, ba um bare um um amma fa kallon har taji gwara ya mata magana ma.

Suna zaunen nan cirko cirko Dr. d’in ya shiga ofishinshi sai wata ma’aikaciyar ce ta ma Salahadeen izinin shiga, yana shiga ya zauna kan kujerar dake fuskantarshi yana kallonshi kamar wanda aka bawa tsoro, saida ya gama rubutu ya d’ago yana gyara zaman gilashinshi ya kalleshi yace “Abokina kuyi hak’uri fa, munyi k’ok’ari sosai wajen ceto rayuwarta, sai dai mun kasa ceto abinda ke cikinta, yanzu haka tana buk’atar jini.”

Shiru yayi kanshi k’asa da alama ya tafi duniyar tunani, numfasawa yayi ya d’ago kanshi ya kalli likitan yace “Ba komai a duba nawa idan zaiyi a k’ara mata.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button