NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Murmushi ya mishi yace “A’a ba ma jini take buk’ata ba kai tsaye.” Takarda ya mik’a mishi yace “Wannan magani ne da za’a siyo, akwai na k’arin jinin a ciki zasu taimakata insha Allah.”

Kamar cikin hushi ya figi takardar ya fita daga ofishin, yana fitowa bai kula su ba har Mama ma ya fice, saida ta rintse ido dan gabanta saida ya fad’i, zugum zugum sukayi suna jiran tsammani har Mamuh ta shigo asibitin cikin nutsuwa, tana ganinsu ta k’arasa tana aje kwanukan abincin hannunta, cikin kulawa Mama tace “Mamuh ya akayi kika san muna nan?”

Saida ta durk’usa tace “Ai muna gida yaya ya koma har ya taho tare da Farha.”

Kafin Mama tace wani abu tace “Mama ya jikin Sarah?”

Cikin kyab’e fuska tace “To har yanzu dai basu ce komai ba Mamuh, yanzu ma ya fita da takarda nasan ba zai wuce wani abun zai siyo ba.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Wai yaushe ma ta dawo Mama? Jiya dai har muka kwanta bamu ganta ba.”

Girgiza kai tayi tace “Bari kedai, nima ganinta kawai nayi ta dawo da dare.”

Tashi tayi daga durk’uson ta koma kan bancin ta zauna, ana haka Salahadeen ya shigo wucewa kawai yayi suka bishi da kallo, bayan ya kaine ma’aikaciyar tace mishi “Kaine mijinta ko?”

Kallonta yayi kamar bai fahimci yarenta ba sai kuma yace “Eh.”

Da hannu ta nuna mishi k’ofar d’akin tace “Ka shiga tana son ganinka.”

Cikin sanyin jiki da tunanin halin da zai sameta ya shiga, yana tura k’ofar sukayi ido hud’u dan dama shi take jiran shigowarshi, duk da sun mata allurar bacci amma bata samu baccin ba saboda jininta na da k’arfin da adadin awon allurar da suka mata ya mata kad’an, kwance take da ruwan da aka k’ara mata, kallo d’aya zaka mata ka fahimci zabgewar da tayi cikin k’ank’anin lokaci kamar ba ita ba tsabar wahala, tun kafin ya k’arasa ta shiga kiciniyar tashi zaune tana ci gaba da kallonshi, baiyi yunk’urin hanata ba sai ma wata ma’aikaciyar jinyar data shigo, saida ta riga shi k’arasawa kusanta ta taimaka mata tayi zaune, magungunan ta b’alla ta bata wani kuma syrup ne ta bata tasha sannan ta aje gefenta ta fita.

Tsaye yayi gabanta yana kallon hannunta dake d’auke da k’arin ruwan, kallonshi tayi cikin muryar wahala tace “Dan Allah mr. ka ara min wayarka zanyi kira ne, ina so yau na bar garin nan na koma inda nake da ‘yanci da gata.”

Shiru yayi kamar baya tare da rai, ya jima haka kuma bata sake cewa komai ba saida yayi niyya dan kanshi ya ciro wayar a aljihu ya mik’a mata, saida ta saka code na k’asar kafin ta shigar da lambar ta kira, duk da baya kallonta amma hankalinshi a kanta yake kuma yana jin abinda take fad’a, hankalinshi ne yaji ya k’ara tashi sosai sanda yaji cikin fad’a tana fad’in “Mr. Dywane, kayi duk yanda zakayi jirgin nan ya samu izinin tashi da kuma shigowa k’asar nan da nake ka d’aukeni, wannan umarni na ne, ina jiranka nan da awa d’aya.”

Tana gama fad’a ta kashe wayar ta kuma saka wasu lambobin, d’orawa tayi a kunne kafin dak’ik’u aka d’auka, da sauri tace “Yawwa uncle i need u help.”

Daga b’angaren shi ya amsa da “Sarah is that u? Ina kika shiga inata kiranki baya shiga?”

Da sauri tace “Dan Allah uncle ka mana taimakon da jirginmu zai samu izinin tashi ya shigo k’asar Niger nan da awa d’aya, ina so na bar garin nan yanzu kafin a kashe ni.”

Cikin tashin hankalin rashin sanin me ke faruwa yace “Sarah me yake faruwa? Me ya sam…”

Katseshi tayi da fad’in “Babu lokaci uncle, kayi abinda na fad’a maka please.”

Kafin yayi wata magana kud’in suka k’are saboda tsadar kiran dake tsakanin k’asashen, mik’a mishi wayar tayi ba tare data kalleshi ba tana fad’in “Thank u.”

Ko ba komai yaji dad’in godiyar data masa duk da tana halin rashin lafiya, yo shi baisan ta inda zai fara bata hak’uri ko rarrashi ba, tsaye yayi kamar gunki ya kasa katab’us sai tubka yake da warwara har saida yaji ya samu mafitar, juyawa yayi kawai ya fita daga d’akin ta bishi da kallon mamaki, ba ma zai ce mata komai ba? Lallai kawai bata da mahimmanci a garesu gwara ta tafi yafi sauk’i.

Yana zuwa ya kallesu yace “Ku tashi mu tafi gida.”

Da mamaki duk suka kalleshi sai Mama data tashi tsaye tace “Lafiya Salahadeen? Ba dai mutuwa tayi ba?”

Girgiza kai yayi yace “A’a, tana nan da ranta, abinda ke cikinta dai ne ya zube.”

Mama ce tace “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, to amma dan ya zube sai mu tafi mu barta kamar wata mara gata.”

Kallon Mama yayi ba alamar wasa a tattare dashi yace “Ku zaku koma gida, ni kuma zan shirya ne mu tafi tare da ita, an zalinceta Mama kuma ni na jawo hakan saboda wofantar da ita da nayi, amma a halin da take ciki yanzu tana buk’atar wanda zai kula da ita, kin sani kuma bata da uwa ko uba, bata da ‘ya ko k’anwa ko d’an uwa, ni d’in nan ne kad’ai wanda ya rage mata, zan tafi tare da ita nayi jinyar abata saboda tawa ce ita.”

Ko da ya fad’a ya nufi k’ofar fita yasa kai, da kallo suka bishi sai dai tuni Farha ta nemi jirkicewa a wurin, tasan sarai saboda ita ya fad’i haka dan taji zafi, kuma taji zafin sosai fiye da tunaninshi, duk saida suka shiga motar suka barta, har ga Allah k’afafunta ne sukayi nauyi ta rasa me ke mata dad’i, duk da jiranta suke baisa tayi sauri ba shima kuma da yake iskanci yake da niyyar soka mata bai sashi tafiya ya barta ba, saida ta iso ga motar ta bud’a ta shiga bayan ita ma tare da su, suna d’aukar hanya Mama duk da bata san manufarsa ba sai cewa tayi “Salahadeen to ni dai in ma kai ba da gaske kake zaka je ba ni ka kaini na d’auki kayana zan tafi tare da yar amana, gaskiya ba zamu barta a halin da take ciki ba ita kad’ai.”

Murmushi yayi ba tare daya kalli kowa ba yace “Mama in kina so sai muje dake ai, zata ji dad’in kasancewarki kusa da ita.”

Babu wanda ya sake magana har suka isa gida bai ko shigar da motar ciki ba, duk ciki suka shiga inda yafi su sassarfa sosai ya haye sama, bin bayanshi Farha tayi da sauri ita ma dan taji da gaske yake ko kuwa, yana jin an shigo bai juya ba sai cire kayanshi daya shiga yi dan yasan ita ce, saida taga yana canza k’ananan kaya tayi k’arfin halin cewa “Yaya Salahadeen da gaske tafiya zakayi tare da ita?”

Ba wani shauki a cikin muryarshi yace “Um, ko zaki tafi?”

Da sauri tace “Kamar ya? Shikenan saika bita ku tafi?”

Juyowa yayi yana d’aga girarshi sama yace “Oh sorry fa, kinga shirya sai mu tafi tare, bana so na d’auki kwananki na kai wani wurin, ki shirya mu tafi kinji dan Allah.”

Yamutsa fuska tayi da alamar damuwa da takaici, yana gama saka kayan ya bud’a wata drower ya kwashi kud’i ya zuba jakar daya fito da ita, tana kallo ya zauna ya saka takalminshi k’afa ciki ya mik’e, jakar ya d’auka ya sab’a a kafad’a ya zo daf da ita yana kallonta, tallabo k’eyarta yayi ya sumbaci goshinta yace “Ina sonki.”

Sakinta yayi ya rab’ata ya nufi k’ofa, da sauri ta fashe da kuka ta fad’i zaune wurin, wani murmushi yayi yana girgiza kai ya juyo ya dawo kusanta ya sunkuya, kallonta yayi yace “Farha idan kina son zuwa ki zo muje, a gaskiya idan na tafi sai sanda na gamsu yer uwarki taji sauk’i zan dawo, kinga kenan babu ranar dawowata.”

Mik’ewa tayi tsaye tana kallonshi tace “Da gaske zaka tafi dani?”

D’aga kafad’a yayi yace “Zaki iya zuwa, amma dole yanzu sai an fara miki passeport, kinga kenan daga baya sai ki same ni acan, na miki alk’awarin zan kula da komai nan da kwana biyu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button