NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Ana idawa aka sake shafa mata wasu magunguna aka shiga nad’e k’afar da farin bandeji mai kama da simiti, ba tare data d’ago kanta ba ta dinga shashek’ar kuka, yana ji shima cike da tausayinta yake ci gaba da shafata sai lokacin ya bud’e ido yaji bugun zuciyarshi ya daidaitu yana tafiya daidai, kallonshi likitan yayi yana murmushi yace “An gama, zamu kaita d’akin hutu.”

A hankali ya d’ago kanta sai kawai kanta ya tafi luuuu tana shirin zamewa daga hannunshi, da azama sosai ya tallabota ta fad’a hannunshi yana kallon fuskarta, likitan ne yayi dariya yace “Jininta mai k’arfi ne wanda ba kai tsaye maganin da ya ma wani ba zai mata, sai yanzu ne maganin baccin ya karb’eta.”

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi tare da gyara mata kwanciyar ta, ma’aikaciyar jinyar ce ta tura gadon aka fita da ita zuwa d’akin hutun. Yanda take sauke numfashi zai tabbatar maka da tana jin dad’in hutun da take samu tattare da sauk’in dale zuwa ta cikinshi, saida ya gama mata kallon k’urilla sannan ya ciro wayarshi ya kira Mustafa ta WhatsApp, dare sosai a wajensu dan haka yace ya kaiwa Mama wayar, ko da ya tabbatar masa da ga Mama ya mik’a mata wayar, ko gaisawa ba ta bari sunyi ba tace “Ina yar amanata?”

Saida ya saki wani murmushi dan wannan soyayya ta yar amana da mahaifiyarshi na bashi dariya da sha’awa, a hankali kamar baya son magana yace “Mama gata tana bacci a gadon asibiti.”

Da k’arfi tace “Asibiti kuma? Har yanzu jikin nata?”

A hankali yace “Eh Mama, an samu karaya ne a k’afarta, amma yanzu an dubata tana bacci ma.”

Sai kawai Mama ta fashe da kuka har Mustafa dake k’ofar d’akin saida ya shigo ya zuba mata ido, cikin rarrashi yace “Mama, Mama dan Allah ki kwantar da hankalinki, wallahi tana lafiya yanzu ba komai, ki daina kukan mana ke da zaki zo inda take.”

Cikin kuka bilhakk’i tace “Domin Allah Salahadeen wannan zalinci har ina, yarinya daga zuwa ta koma harda karyata, gaskiya ni hankalina bai kwanta da zamanka da ita ba, ni kawai ka dawo min da surukata anan zan kula da abuta.”

Murmushi ya saki sosai wanda ya bayyanar da hak’oranshi ya ma rasa me zai cewa Maman, jin bai ce komai ba yasa ta cewa “Kana jina, ka dawo da ita gabana nan zan kula da ita.”

Cikin sauri yace “Mama, rik’e wayar ki ba Mustafa.”

Mik’awa Mustafa tayi shi kuma yana ganin kira ya sake shigowa na video call saiya d’auka ya sake mik’awa Mama, tana karb’a ta ganshi tarau a majigin wayar saita nemi wuri tayi zaune, kamar mai jin bacci ya kalleta yace “Zaki ga yar amanarki Mama?”

Da sauri ta d’aga kai alamar eh tana fad’in “Eh, tana ina dan Allah?”

A hankali ya taka ya zauna kusa da kan Sarah, gyara wayar yayi yanda ya iya d’aukar kanshi da Sarah dake kwance tana bacci, tana ganinta ta waro ido tace “Kayan menene a jikinta kuma haka kamar na masu datse wuta?”

Gimtse dariyarshi yayi yace “Mama kayan asibiti ne, masu jinya ale sakawa.”

Tab’e baki tayi tace “Amma kuma harda hula?”

Kai kawai ya d’aga mata, kallon fuskar Sarah ta sakeyi data mata wani fayau da ita tayi kyau, a hankali cike da so da k’auna tace “Dan Allah shafa min fuskarta, ji nake kamar na zura hannuna na tab’a fuskarta.”

Kallon Sarah yayi, saida ya sauke numfashi a hankali yasa hannunshi na hagu da baya rik’e da wayar, girarta ya shiga gyara mata kwanciyarta da kyau tare da zagaya duk ilahirin fuskarta, sai ya manta da Mama na kallonshi ma ya shagala da kallon fuskarta da wasa da hannunshi akai.

Muryar Mama ce ta dawo dashi tana fad’in “Kaga da zaka yi k’ok’ari idan ta tashin nan ka had’a mata ruwan zafi tayi wanka, ka samu tuwon masara da miyar kuka da man shanu da d’an yajin daddawa ka bata ta ci, idan aka jima kuma ta samu farfaesun kaji da daddawa a ciki da yaji, wallahi dandanan sai kaga k’arfin jikinta ya dawo ta samu lafiya, ita kanta sai taji wani sabon k’arfi.”

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:18 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 3锔忊儯9锔忊儯

Wata irin bazawarar dariya yayi yace “Mama ina zan samu duk abin nan da kika lissafa yanzu?”

Cikin yatsina fuska tace “Babu ko? Ai kaji irinta garin banza kenan, shiyasa na so ta zauna kusa dani.”

Murmushi yayi yace “Karki damu Mama, zanyi k’ok’ari naga na mata duk abinda ke ma zaki mata insha Allah.”

Kawar da kai tayi alamar kunyar maganarshi, mik’awa Mustafa wayar tayi tana fad’in “Karb’i nan kai saida safe.”

Karb’a yayi yana kallon Salahadeen dake fad’in “Saida safe Mama.”

Cikin zolaya Mustafa yace “Yau fa ka hanani bacci wallahi.”

Hararanshi yayi yace “Kai tafi can sai kace wani mace baka da aiki sai bacci, ka sani ma ina dawowa aure zan maka.”

Wata dariya yayi yace “Haba abokina, aure yanzu d’an yaro dani? Ka bani harna fara k’wari dai ko.”

Tab’e baki yayi yace “Saida safe.”

Kashe wayar yayi tare da mayar da kallonshi kan Sarah da ke ta baccinta, matsawa yayi kusanta sosai ya shafi fuskarta, hanyar fita ya nufa yana danna wayarshi ya kira Richard dan yana so su had’u, ko da ya fad’a masa yana gida ya shiga taxi ta isar dashi madakatar hawa bus, daga nan ma yana sauka wata taxi ya sake hawa ya k’arasa gidan.

Tun daga k’ofar shiga d’akin ya yamutsa fuska saboda tsantseni, kallon d’akin yake tare da tsayawa ya ciro hankc. ya rufe hancinshi, komai a yamutse yake a firgice datti da wari da k’arni, tsakin da yaja ne yasa Richard dake ta cakalar computer da sigari a bakinshi ya d’ago kai, da farin ciki yace “Kai d’an uwa sannu da zuwa, shigo mana.”

Sake mayar da kanshi yayi ga abinda yake, tsaye yayi bai shiga ba kuma bai ce mishi komai ba, jin haka yasa shi d’agowa zaiyi magana sai kuma ya kalleshi da mamaki yace “Me kake nufi? D’akin namu ne kake rufewa hanci?”

Wani lumshe ido yayi tare da cewa “Ina nufin mu fita waje muyi magana, ba zan iya zama cikin d’akin nan wari ya kasheni ba.”

Aje computer hannunshi yayi ya d’auki pillow ya wurga masa yayi saurin kaucewa, tasowa yayi yana dariya dan yasan ba zai zauna a d’akin ba, dama lokacin yana nan shi ne ke gyaran, tunda ya tafi kuma babu mai lissafin ya gyara makwancin, haka suke zama a ciki basu damu ba suma, a k’ofar shiga d’akin ya same shi zaune akan matakala yana ninke hankc. d’in hannunshi ya mayar aljihu. Zaune yayi kusanshi suna mik’awa juna hannu suka yi wata irin gaisawa ta yan duniya, fito da sigarin bakinshi yayi ya mik’awa Salahadeen kamar yanda a baya sukeyi, girgiza mishi kai yayi alamar a’a, da mamaki ya kalleshi yace “Ka daina sha ne?”

Kai ya sake d’aga mishi alamar eh, dukanshi yayi a hannu yana fad’in “Mugu, fad’a min waya canza min kai?”

Kallon titin dake gabansu yayi yana murmushi kawai, sannu a hankali ya shiga tunanin irin gwagwarmayar daya sha sanda ya so rabuwa da sigari ba tare da kowa ya san yana sha ba, duk sanda ya ga wani yana sha sai yaji sha’awarta shima, amma haka zai duk’ufa neman tsarin ubangiji har yaji abun ya lafa masa, idan ransa ya b’ace haka zaiji yana buk’atar yasha, sai dai kullum maganar Sarah na dawo mishi sanda ta tambaye shi me yasa baya sha a gida? Saboda baya so su sani ne? Da k’yar ya samu tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu bai sake sha ba, a daren shakaran jiya kuma data zo mishi da labarin cikin nan, saiya k’ara d’aura niyyar dainawa, sai dai kash Farha…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button