NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Sanda mahaifinta ya kwanta rashin lafiya da lauyenshi da kuma Shakoor su suka zama shaida kan ya mallakawa Samanta duk abinda ya mallaka, har zuwa lokacin bai da wani k’uduri akan dukiyar, bayan mutuwar mahaifinta tsabar son da take masa da kuma ganin tana da cikinshi, sai ita ma ta mayar da jiga jigan kadadorinta da sunanshi, bata so yasan da haka ba shiyasa ma ta rik’e takardun da ba original a hannunta ba, cikin akasi wata rana yana neman wasu takardunshi ya ga wannan takardun, daga lokacin yaji akan me zata barshi yayi ta bauta wa masana’antar Babanta bayan ma ta mallaka mishi komai ko da bayan ranta.

Da tunanin yanda zai dawo da komai hannunshi yake kwana yake tashi, a wannan k’adamin Alhaji Kabeer ya shigo rayuwarshi, a wata tattaunawa da sukayi ya fad’a mishi yana so ya samu kud’i sosai, shi kuma yace yasan inda zai kaishi yayi kud’i. Ba tafiyar mota ko jirgi bace bare yace yasan inda suka bi suka je wurin, shi dai kawai ya same shi a wurin ne wanda hakan na da nasaba da tsafi.

Da zuwan farko sunyi maraba dashi tare da bashi abinda yake so a karon farko, ya fara harkar sosai inda yake bin duk wani umarni da aka bashi, uku daga cikin manyan k’ungiyar ne kawai suka san asalin kan dutsen da suke, amma bayan su babu wanda yasan wurin, sai dai kawai kayi tsafi ka ganka a wurin a kowane dare.

Shekara uku da haihuwar Sarah al’amarinshi suka fara bata tsoro, musamman d’akin daya ware ya hanata ko da zuwa kusa dashi, hakan yasa ta mayar da hankalin kan miye a d’akin na sirri da baya so ta sani, a daren daya zama shine na k’arshe a wurinta, ta farka a bacci bata ganshi ba ta duba duk inda take ganin zai iya kasancewa, ganin bata ganshi sai kawai ta shiga d’akin tayi sa’a kuma a bud’e yake, bata ganshi a ciki ba dan lokacin ya riga daya b’ace, amma abubuwan data gani ne suka tsorata ta dan ya nuna d’akin ana aikata abunda bai dace ba, jan mayafi da bak’i da k’ok’on kai na mutum yasa ta fito a tsorace, rud’ewa tayi kawai taje d’akin Sarah dake bacci ta d’auketa, ta fita daga d’akin zata shiga ascenseur ya fito, da wani sabon tsoron ta kalleshi dan bata ga ta ina ba ya fito, baya ta fara ja hakan yasa shi saurin jawota jikinshi, rumgumeta yayi cikin salon mugunta yace “Ina zaki je?”

Kuka ta fara ba tare data raba jikinsu ba tace “Tafiya zanyi, ka sake ni ina so na tafi, tsoro nake ji, Shakoor ba kai bane.”

Wani murmushi yace yace “Yata fa?”

D’agowa tayi ta kalleshi tace “Da ita zan tafi, ba zan barta hannunka ba.”

“Me yasa?” Ya fad’a yana murmushi, da sauri tace “Saboda ban yarda da kai ba, zaka cutar min da ‘yata.”

Cikin nutsuwa da fitar da kowace kalma yace “Ina sonta Sam, karki raba ni da ita rayuwata ce.”

Girgiza kai tayi alamar a’a, hakan yasa shi cewa “Muje ciki to sai muyi magana.”

Kallonshi tayi tace “Ba zaka cutar dani ba?”

Wani lumshe ido yayi da yake nuna a’a, cikin son tabbatarwa tace “Promise?”

Jinjina kai yayi yace “Promise.”

Gaba ya izata yana binta a baya, a falo suka zauna tana rik’e da Sarah gam, mik’ewa yayi yace “Bari na kawo miki ruwa, naga duk a tsorace kike.”

Da kallo ta bishi har ya shiga d’akin baccinsu, jikinta banda rawa babu abinda yake, tunanin abinda zai faru take, jin shirun kamar zaiyi yawa yasa ta mik’ewa suka tunkari k’ofa. Shakoor da shi kuma ko da ya shiga Kabeer ya fad’awa komai, nan yace bari ya kira mai gidansu kawai a kasheta dan kar ta tona musu asiri, amincewa yayi dan haka ko da suka gama wayar ya fito.

Tana shirin kaiwa k’ofa kawai taji saukar abu a tsakiyar kanta, hakan kuma ya auku tare da tsayawar zuciyarta da kuma gudanar jininta, yana k’arasowa har ta fad’i a wurin k’amk’ame da Sarah a jikinta, yana zuwa Sarah ya b’amb’are a jikinta data farka daga bacci tana kallonta.

Duk binciken likotoci akan gawarta ya nuna kawai wata yar harbawa jini ce ta haddasa mata tsayawar zuciya? Dan haka aka rufe maganar mutuwarta rufewa ta har abada.

         *Ci gaba*

Wayarshi ya d’auka ya kira Salah, ko da ya d’auka a tak’aice yace “Ka same ni office da safe.”

Daga b’angarenshi ya amsa “Ok.”

Ya jima baiyi bacci ba a daren yana tunanin yanda zai fara koyawa kansa rayuwa ba tare da Sarah ba, tun rasuwar mahaifinta da hannunshi ya raini abar shi, baya harkar mata kuma ko a wajen tsafin basa sa shi harka da mata, bai k’ara kallon wata da sunan soyayya ba, tun yana son ‘yar da zuciyarshi har ya fara sonta da gaba d’aya rayuwarshi, ba kawai yana sonta bane dan yana ubanta, yana sonta ne dan ya zama komai nata, uwa uba yan uwa da gaba d’aya duniyarta, baiyi bacci ba kod’an yana tunanin wannan lamari har gari ya waye.

Da safe yana office Kabeer ya zo ya same shi dan jin wani shafaffe da man ne ya dakar mishi yaro? Bayan sun gaisa a mutumce Kabeer yace

“Elhaji Shakoor wai ni kam Sarah tana da samari ne?”

Da mamaki ya kalleshi yace “Princess? Samari kuma? Me zai had’a ta da wannan shirmen? Sanin kanka ne ai ban bata wannan damar ba.”

Kallonshi shima yayi yace “To amman wane irin mutane take mu’amula dasu?”

Cikin k’aguwa ya kalleshi yace “Wai duk tambayoyin na miye? Ka je kan canzan mana.”

Murmushi yayi yace “Shakoor na sanka farin sani, zan iya tambayarka dalilin da yasa kasa aka dakar min yaro na, amma banyi haka ba saboda ina so naji ko zaka fito kai tsaye ka fad’a min gaskiyar.”

Cikin shanyanyun idonshi ya kalleshi yace “Kasan da haka me yasa zaka tsaya kana tambaya ta?”

Tsaye ya mik’e a hassale yace “Ina so nasan dalilin da yasa kasa aka dakar min yaro ne akan matacciyar ‘yarka?”

Shima a k’ufule ya mik’e tsaye yana fad’in “Matacciya? Sarah ce matacciya? Kasan dai ina da hanyoyin da zan bi dan ganin hakan bata faru ba ko?”

Da murmushi ya kalle shi yace “Da kana da su daka jima da bi tun tuni dan gujewa zuwan rana irinta jiya.”

Cike da gadara yace “Shikenan zaka gani, zan sauya wannan tarihin, jinin ‘yata yafi k’arfin shan karnuka irinku wallahi.”

Cikin d’aga murya yace “Karnuka irinku ko karnuka irinmu? Kai daka sha jinin ‘ya’yan wasu fa? ‘Yar ka tafi ta kowa ne?”

A harzuk’e yace “Yes! Yes! Sarah its the best dauther in this world, Sarah its the…its the…”

Bai k’arasa ba saboda wani abu da yaji kamar zai taho mishi mai kama da kuka, saida ya daidai ta nutsuwarsa ya mayar da hawayen sannan ya kalleshi yace “Get out.”

Dafiyar k’eta ya mishi yace “Ka sanni na sanka, mai maintenant je te laisse pour te soullager.”

Ya juya zai fita Salahadeen ya shigo, ido cikin ido suka kalli juna, shi yana mamakin yanda yaron ya shigo ba tare da yaji an nema masa izinin shigowa wurin Shakoor d’in ba, a gwamnatacce ma idan kana son ganinshi saika had’a da siyasa da sa hannun hannu. Inda salahadeen kuma ke nanata kalaman da yaji na k’arshe cewa ” Ka sanni na sanka…

D’auke ido yayi kai tsaye ya zauna kan kujerar dake gaban Shakoor d’in ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya, saida ya ga fitar Kabeer kad’ai ya zauna yana kallon Salahadeen, kallon juna sukayi sosai inda cikin damuwa da amon muryar jimami Shakoor yace “Aiki zan baka, amma akwai buk’atar kayi komai da kulawa.”

Yana jujjuya kujerar da yake kai yana kallonshi da izza yace “Je t’茅coute.”

Saida ya numfasa yace “Kidnapping.”

Saida ya d’an had’e girar sama da k’asa yana kallonshi, ya tab’a mishi kidnapping d’in wani babban lauyer suka sa shi yasa hannu, sannan ya tab’a d’auko d’an wani d’an kasuwa ma suka sa shi yasa hannu kan takardun filinshi, yanzu kuma baisan wa zai d’auko ba, but koma waye zai iya tunda biyanshi zaiyi, a hankali ya saki fuskarshi ya sauke k’afarshi hana kallonshi yace “Waye? Adreshinshi? Photonshi da kuma ranar da kake so?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button