SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Zungurar da Richard ya masa yana fad’in “Fad’a min mana, ko dai princess d’in Abhi ce?”
D’an guntun tsaki yayi ya kalleshi yace “Bar wannan shirmen, magana na zo muyi da kai.”
Jinjina kai yayi yace “Ta samu kenan? Wa zamu shiga account d’inshi mu zaftaro kud’ad’enshi?”
Cike da jin haushi yace “Richard ka saurare ni mana, magana ce mai mahimmanci, ni yanzu duk na daina wannan shirmen ba zan sake aikata abunda babu kyau ba.”
Cikin rashin damuwa yace “Heyy me yayi zafi, me yake damunka ne?”
Kallonshi yayi a tsanake, a take sai yaji haushin kanshi da kanshi, tabbas yayi asarar rayuwarshi da kuma zama tare da Richard ba tare daya anfane shi da komai ba, a matsayinshi na musulmi bai kamata ace ya biyewa munannen halayensu ba, hakan zaisa su bayar da shaida akan musulmi baki d’aya, kamata yayi ace ya zama wakilin kyakyawar shaidar musulmai da musulunci, amma sam baiyi haka ba ya shantake dayawa. Juyar da kanshi yayi cikin rashin son magana yace “Matata nake son yi wa passeport, amma bansan taya zan shigo da ita ba.”
Cike da rashin bawa abun mahimmanci dai yace “Abu mai sauk’i, ka bayar da bayanin zaku zo honey moon ne, ka rigata zuwa ne saboda kai anan kake dama kuma kana da katin shaidar zama a k’asar nan dan ka samu masaukin da zai dace daku, dan dana zaka samu passeport d’in ka da visa ma.”
Kallonshi yayi ya saki murmushi ya mik’e da sauri ya dafa kafad’arshi yace “Da kyau abokina, nagode sosai, Allah ya saka maka da alkairi.”
Yana fad’a ya juya bai jira me zai ce ba ya tafiyarshi, da kallo ya bishi shima kafin ya mik’e ya koma ciki, asibitin ya koma shima bayan ya siyi abu mai mahimmancin da yake ganin zai birgeta, pliwa ce mai kyau wacce akayi pakcajin d’inta fara da kuma kalar yelo yelo, yana shiga d’akin yayi daidai da farkawarta tana k’ok’arin tashi zaune, k’arasawa yayi ya aje pliwar a gefen gadon kusa da inda magungunanta suke, matsawa yayi kusanta ya sunkuya ya zura hannu ta k’asanta d’aya kuma a bayanta, da sauri ta tureshi tana fad’in “Me kake yi haka malam? Ina zaka kaini?”
Ko kallonta baiyi ba sai gyara mata zaman da yayi ya mik’e tsaye, juyawa yayi ya zauna kan doguwar kujerar dake d’an nesa da gadon.
Kumbura fuska tayi tana turo baki tana so ta juya ta harareshi sai dai tana ji a jikinta ita yake kallo, suna haka suka ji an k’wank’wasa k’ofar d’akin tare da bud’awa aka shigo, duk zubawa k’ofar ido sukayi dan ganin me shihowa, tana ganin Kabeer ta saki murmushi tana fad’in “Uncle.”
Da sauri ya tako yana sake rik’e k’atuwar pliwar hannunshi, tunda ya ganshi yaji ranshi ya b’ace sosai, shi ya sani ba mutumin kirki bane shima daga abinda ya sani a game dashi da mahaifin nata da kuma abubuwan da suka faru, idan ya had’asu ya auna a mizani zai baka tabbacin lallai shima kamar waccen ne, sannan daga bayanan da Richard ya bashi kwanan baya cewa ana bibiyarta a mekka ya sa mishi kokonto akanshi, a hankali ya mik’e ya zo kusan Sarah ya tsaya yana kallonshi.
Aje pliwar yayi a wata yar drower tare da kallon Sarah ya d’an sunkuyo da niyyar rumgumota jikinshi, ita kanta harta bud’e hannayenta ta d’ago zata karb’i tayin rumgumar. Amma sai ji yayi an tokareshi da hannun da baisan ko nawa bane, kallon hannun yayi daya tokare mishi k’irji haka, ita ma a lokacin ta kalli hannun daya bi ta gabanta ya gifta, Salahadeen ne ya togace shi daga shirin rumgume mishi mata, kallon Sarah yayi fuskarshi a matuk’ar had’e sosai yace “Daga yau na haramta miki had’a jikinki da kowane mutum ko da wanda ya haifeki ne.”
D’auke hannunshi yayi daga k’irjin Kabeer ya kalli k’wayar idonshi yace “Bare kuma kowane jaki da doki, ban yarda ba, idan kuma baki ji ba to zaki jawa wanda baisan hawa ba bare sauka matsalar da zata sa ya rasa wani sassa nashi.”
Duk ido suka zuba mishi, sosai yaji zafin abinda matashin ya fad’a, hak’ik’a yana jin labarinshi a wurin Shakoor kafin ya mutu, yasan ta’adinshi da iskancinshi, to amma me yasa zai mishi bayan yasan waye shi? Kuma ko bai sani ba matsayinshi na wanda Sarah ke kira uncle ai zai girmama shi.
Kalaman Sarah ne suka dawo dashi daga duniyar mamakin dake neman shek’eshi tana fad’in “Are u mad? Shi fa uncle d’ina ne, akan me zaka fad’a mana magana haka?”
Ko kallonta baiyi ba sai ma juyawa da yayi ya koma ya zauna inda yake, cikin jin haushi ta kalli Kabeer tace “Uncle wai me yasa zai dinga min haka? Ni fa babu wani had’i tsakanina dashi, haka ka…”
Dafa kafad’arta yayi cikin danne abinda yake ji yace “Princess, karki damu mana, shi fa mijinki ne yana da ikon hanaki ko saka ki, sannan bana so kiyi rigima a halin da kike ciki yanzu saboda wannan k’aramin prince d’in.”
Ya k’arashe maganar yana nuna cikinta da yatsa, kunya taji ta rufe fuskarta sai kuma ta bud’a fuskar ta nuna Salahadeen dake zaune ya sharesu tace “To uncle ka fad’a masa ya bar nan wurin kafin na kashe shi da hannu ko kuma bak’in cikinshi ya kashe ni, ya koma k’asarsu ya bar ni nan ida wanda zasu kula dani.”
Murmushi yayi yace “Karki damu kinji zai koma, yanzu fad’a min ya k’afar taki?”
Cikin shagwab’a ta turo baki tace “Da sauk’i uncle, amma ka samu Dr. nan ka rok’a min alfarmarsu su barni na koma gida.”
Jinjina kai yayi yace “Shikenan zan fad’a musu naji idan hakan zai yiwu.”
Kallonta yayi yace “Akwai wani abu da kike buk’ata ne?”
Girgiza kai tayi tace “A’a.” Jinjina kai yayi yace “Shikenan zan tafi, amma zan sake dawowa naga jikinki.”
Godiya ta sake masa har ya fita tana kallo Salahadeen ya bi bayanshi, suna fita k’ofar d’akin ko da ya rufe k’ofar ya rik’o hannunshi, tsayawa yayi cak ya juyo yana kallonshi, cikin gadara yace “Miye haka? Tsaranka ne ni? Kasan ko ni waye?”
Tab’e baki yayi yace “Ban sani ba, amma nasan kai kasan waye ni, abu nake son tambayarka? Sannan ina so na maka wani gargad’i akan Sarah.”
Sakin hannunshi yayi ya zuba hannayenshi aljihu yana kallonshi sosai yace “Ya akayi kasan ni mijinta?”
Wani murmushin rainin hankali yayi ya gyara tsayawarshi yace “Ubanta ne ya fad’a min, baya komai ba tare da shawarata ba.”
Ba tare daya d’auke idonshi daga kanshi ba yace “Idan shine ya fad’a maka aurenmu, samun cikinta fa? Ya akayi ka sani?”
Saida yaji gabanshi ya tsinke ya fad’i, sam baiyi tunanin maganar daya fad’a zata iya dawo mishi ta haka ba, gashi kuma yanda ya zuba masa ido alamu ne na shi yake jira ya bashi amsa, wani murmushi yayi mai kama da kuka yace “Ita kamar uba take d’aukata, tana fad’a min duk abinda ya shafeta.”
Ajiyar zuciya ya sauke yace “Magana ta gaskiya bana son sake ganinka kusa da ita, idan zai yiwu kayi nesa da ita daga yanzu zuwa lokacin da zan d’auketa mu bar nan, dan gaskiya ban yarda da kai ba.”
Wata dariya ya bushe da ita yana kallonshi yace “Wai nayi nesa da Sarah kake cewa? To ubanta Shakoor ya dawo nan bai isa ya min shamaki tsakanina da ita ba bare kai.”
Wani murmushin gefen labb’a yayi yace “Haka nima, ko da ubanta yana raye baida wani iko akanta, ni nine mai fad’a aji a kanta, na kuma isa nasa ko ba’a so, wannan kashedi nayi maka a matsayinna na Salahadeen, idan kuma kasa na dawo Salah to ba zaka ji da dad’i ba.”
Maysowa yayi kusanshi sosai suna kallon juna yace “Naga alama so kake kaja dani, amma zan nuna maka ni na haifeka a duniyanci, mu zuba ni da kai muga wa zaiyi nasara.”