SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Karb’a tayi cikin wani mugun sanyin jiki saboda tuna mata da akayi wajen mijin da zata je har da wacce ake ganin kishiyarta ce ma, aje wayar tayi kan gado sanda Mama ta fita ta wani fuska ta shige ban d’akin.
Sai dare ya dawo lokacin har ta fara bacci bacci saboda zaman shiru ya mata yawa, taji motsin shigowar amma sai tayi gum bata motsa ba, kallon fuskarta yayi ganin bacci take saiya matsa kusa da ita, gyara mata zanin rufar yayi har wuyanta ya d’an shafi kanta, cike da k’arfin hali ya sunkuya sosai yana dafe da kanta da niyyar sumbatar goshinta. Cikin zabura ta ja baya tana bud’a idonta akan fuskarshi a tsorace, inuwa da jinini mutum da taji ne yasa ta farkawa, kallon idonta yayi shima sai kawai yaji ba zai yarda ya zo a banza ba, idan kuma ya basar zatayi tunanin wani abu na daban, ba tare data daina kallonshi ba tace “Mr. me kake shiri..?” Bai bari ta k’arasa ba ya fizgo kanta ya had’a bakinta da nashi ya sumbata, sakinta yayi ya mik’e ya nufi kujerarshi, da ido kawai ta bishi tana mamakin lamarin mutumen, in yayi wani abu saita shiga tunanin me yake nufi? In kuma yayi wani abun saita ga dama haka ya dace a samu a tsakaninsu ai. Kwance taga yayi kan kujerar tare da warware zanin rufar dake kan kujerar ya rufe ido kamar mai shirin yin baccin da gaske.
Ita ma gyara kwanciyarta tayi ta rufe ido, amma saita samu numfashinta ma baya fita yanda ya kamata, sam bata tare da nutsuwarta bare ta samu bacci ya d’auketa, jikinta har wani gumi gumi yake fitarwa, so take ta bud’a ido ta kalleshi amma tana tsoron karsu had’a ido, duk da dai bata jin alamun ana kallonta. Sake lik’e idonta tayi gam tana karanto addua’r bacci ta hanyar motsa labb’anta kawai, haka dai tana d’an tunane tunane har baccin yayi gaba da ita ba tare data sani ba.
Ta jima da yin nisa a baccinta sosai kuma shi ma ya fahimci haka, tasowa yayi daga kan kujerar ya shiga ban d’aki yayo alwala, yana fitowa ya gama iya dubansa bai samu wani abun da zai iya shinfid’awa ba a matsayin sallaya, kayanta da aka ninke mata aka saka a cikin yar drower wurin ya bud’a ya d’auko hijab d’inta, shima kuma k’arami ne baida tsayin da zai ishe shi, daidaita shi yayi ya ketashi da k’arfin tsiya hakan uasa hijab d’in yin tsayi duk da babu fad’i, haka ya shinfid’a ya kabbara sallah.
Da sassafe ya tsaya kanta da niyyar ya tasheta, tsaye yayi yana kallon yanda ta wani saka hannu bibbiyu duk ta dafe mararta da yake a saman zanin rufar ne ta d’ora, tab’e baki yayi ya daddab’ata, bud’a ido tayi ta sauke a kanshi ta sake lumshe ido, daddab’ata ya sake yi tace “Umm.”
Cikin fad’a yace “Ki tashi malama kin wani rumgume mara kamar kin rumgume yaro.”
Da sauri ta tashi duk ta zaro ido tace “Ba komai fa, lafiya lau.”
Yatsina fuska yayi da mamakin yanda ta zabura ta kuma tsorata lokaci d’aya, duk sai yaji wani abu na son darsuwa a ranshi amma saiya share kawai yace “Hajia tashi kiyi sallah.”
Kallonshi tace “Asuba tayi? Wayyo Allah na sallah.”
Wajen saurin yasa ta mantawa da ciwon k’afarta kawai ta dirko daga kan gadon, saida ta dire k’afar ne taji ciwon, da sauri ta dafe gadon tana fad’in “Wayyo k’afata.”
Da wani irin sauri ya zagayo inda take ya durk’usa cike da nuna damuwa ya kalli k’afar yace “Da zafi ne? Sannu bari na taimaka miki.”
Sam saita nemi ciwon ta rasa ta koma kallonshi da mamakin yanda ya wani nuna damuwa sosai a kanta, d’agowa yayi ba tare daya kula da kallonta ba ya kamata sosai ya nufi ban d’akin da ita. Da taimakonshi ta samu tayi alwala har ta zo kabbara sallah, ganin hijab d’inta ne a k’asa a yage ta d’aga kai ta kalleshi tace “Mr. wannan menene?”
Kallonta yayi a hek’e yace “Baki gane shi bane ko me?”
Cikin rashin kunya tace “Ban gane ba kam, ko zaka iya fad’a min na fahimta?”
Harara ya daddala mata ya kawar da kanshi, gyara tsayuwa tayi tace “To kasan ka yaga min hijab ne kuma ka tashe ni nayi sallah? To ka ciro rigarka ka bani saina rufe kaina.”
Tasowa yayi daga kujerar ya zo gabanta ya tsaya, sosai ya matse mata wuri yanda ta kasa d’aga kanta ta kalleshi, tana gani ya shiga b’alle botiran rigarshi har saida ya gama, cire rigar yayi inda fara k’al d’in singlet d’inshi ta bayyana, yab’a mata rigar yayi a fuska ta rufeta, lumshe ido tayi sanda k’amshin turaren rexona ya sake surarawa ya shiga hancinta, hannu tasa a hankali ta janyo rigar ta fito da fuskarta, yanda ya k’ura mata ido ita ma sai ta shiga kallonshi da tunanin da bata san ma me take hasashe a game dashi ba a lokacin.
Jefa mishi rigar tayi a jiki ita tana fad’in “Idan naje gida zanyi a halin larura.”
Juyawa tayi zata nufi gadonta ya rik’e hannunta, juyowa tayi tana kallonshi shima kuma haka, cikin jinjina kai tace “Miye?”
Saida ya d’aga mata gira d’aya yace “A makarantar taki an sanar dake miye miji? Ya kuma ya kamata mata ta zama a gurin mijinta?”
Saida ta zame hannunta daga nashi tace “Me yasa kake tambayata?”
Shafa tarin sumarshi yayi ba tare daya kalleta ba yace “Akwai masaukin bak’i a gidanki?”
Girgiza kai tayi ta k’arasa takawa ta zauna kan gadon, yana kallonta har ta gyara ta jingina bayanta a pillow, ba tare data kalleshi ba tace “Akwai wajen zaman sama da mutum hamsin ma idan kana so, amma wa zaka sauke?”
Juyawa yayi ya koma kan kujera shima yana fad’in “Ni da kuma…matata.”
Saida taji gabanta ya gurfana ya fad’i, gabanta ta kafe da ido tana kallo inda ta shiga maimaita kalmar matata, da sauri ta kori zancen ta kalleshi tace “Zan iya sauke ku a matsayin bak’ina, sai dai ina da sharad’i akan haka.”
Kallonta yayi kamar zaiyi magana kuma dai yayi shiru, ko ta d’auka baida masaukin ne shi? Yana da gidan da shima ya mallaka anan sanda yake zaune, bai waiwaye shi bane saboda ya rabu da duk abinda ya samu da waccen dukiyar baya, kuma a yanzu ma ba dan baida kud’in kama musu inda zasu zauna ba, nufinshi na son Farha ta ga wacece Sarah yasa yake son su zauna tare, idan kuma ba gidanta ba abun ba zai bayar da cittar da yake buk’ata ba. Kallon data masa ne yasa shi mata alama da ido irin ina jinki d’in nan, ba tare da damuwa ba tace “Ku tabbatar ba zaku dame ni ba, sannan zaku tsaya a matsayinku.”
Wani murmushi ne ya sub’uce masa bai shirya ba, kallonta yayi yana murmushi yace “Ita ko kuma dukanmu?”
Cikin d’aga kafad’a da tab’e baki tace “Dukanku mana, gidanka ne kai d’in?”
Yanzu kam dariya yayi har ta fito da hak’oranshi yace “Da kai da kaya fa duk mallakar wuya ne, matata kam zata iya yarda da sharad’inki amma banda ni.”
A take tace “Saboda me? Da kai aka gina gidan?”
Girgiza kai yayi kawai ya gyara zamanshi ya lusmhe ido bai ce komai ba, yatsina fuska tayi ta harareshi da tab’e baki tana rawa da kai alamar shegantaka take mishi dan taga idonshi rufe.
Kafin ta ci komai aka sake zuwa dan duba aikin da akayi a k’afar, bayan dubawa a n’aura da d’aukar hoton k’afar ya tabbatar aikin yayi jiran warkewa kawai za ayi, nan suka sallameta kamar yanda ta buk’ata tare da gargad’in karta yarda ta taka k’afar sai bayan sati biyu, sannan kwana uku su dawo a sake dubata, godiya suka musu inda Salahadeen ya biya cajin da suka musu. Doguwar rigarta ta mayar inda ta d’auki hijab d’inta tayi dubara ta lakayashi ta rufe kanta zuwa wuyanta kamar yanda yake, malamar asibitin ta jawo keken da za’a turata yace kawai ta barshi, saida ya kalleta yace “Kin gama kwalliyar?”