SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Kallonshi tayi da mamakin wai kwalliya? To shi ya tab’a ganinta da kwalliya ma wacce ake kira kwalliya ne? Tana shirin tab’e baki kawai taji yayi cak da ita ya d’aga sama ya rumgume a jikinshi ya d’auki hanya, cikin tsoro da fari tayi saurin zagaya hannunta ta wuyanshi ta rik’e gam, lift suka shiga inda tafiyar ta rage musu tsayi kenan. Ikon Allah kuma ya k’ura mata ido kamar dai tak yake jira tace ya had’a kanta da garun wurin, duk sai taji tsoro ya kamata kawai ta k’i had’a ido dashi, saida taji alamar sun tsaya zata bud’e taji wani sanyi sanyi duk ta k’agu ya sauketa.
Taxi suka samu inda tayi doguwar tafiya dasu, tunda ta ga ba hanyar gidan bace ta fara tambayar ina zai kaita? Bai kulata ba har saida ya umarci mai taxin daya tsaya, ko da ya samu wuri ya paka ya fito yana bashi kud’in shi, bud’e inda take zaune yayi yana shirin tallabota ta dakatar dashi da cewa “Zan fito malam.”
Ruro baki tayi ta fara k’ok’arin zuro k’afa tana fad’in “Sai kace wata gurguwa kayita d’aukata kamar ka haifeni.”
Ganin sai jan k’afar take tana so ta k’arasa fitowa ta rufe k’ofar yasa shi hassala ya fizgota ya sab’a a kafad’a ya rufe taxi, a ranshi yana ayyana lallai in bata yi sannu ba zai b’arar da ita ta yanda ba ciki ba yanzu sai dai ta rasa hankalinta.
Motar dake pake a gefe bak’a wulik ya bud’e ya turata ciki, da sauri ta tashi zaune kafin tayi wani yunk’uri harya mayar da k’ofar ya rufe, zagayawa yayi gidan gaba ya shiga aka ja motar, wata ajiyar zuciya ta sauke cikin zubo da hawaye tace “Mr., dan Allah in ma kasheni zakayi ko siyar dani ka min wata alfarma mana?”
Cikin sake had’e rai ba tare daya juyo ba yace “Fad’in muradinki na k’arshe.”
Saida ta sake matso hawaye sosai ta had’e yawu tace “Ka barni har na haife…”
Shiru tayi tasa hannu tana share hawayenta, juyowa yayi tare da Richard dake tuk’a motar suka kalleta, a hankali yace “Ina jinki, me kike son fad’a ne?”
Girgiza kai tayi alamar ba komai, da alamar tambaya a fuskarshi yace “Kin tabbata?”
D’aga kai tayi tana fad’in “Ba komai, na rantse maka.”
Jinjina kai yayi ya kalli Richard da ido ya mishi wani zaurencen daya sa Richard tsayawa ya fito a motar shi ya koma mazaunin matuk’i, ciro wata tablet yayi ya shiga jagulawa cikin k’warewa, har lokacin kuma bata daina share hawaye ba har saida taji Richard yace “Na tura maka a wayarka, zaka samu sak’on yanzu.”
A k’alla sunyi awa d’aya a hanya kafin suka isa wani k’aramin tsuburi, ko da akwai wasu gidajen hutawar to dai ba anan kusa da gidan da suka tsaya ba, banda ruwa babu abinda kake gani sai bishiyoyin dake bayan ginin gidan, shi kanshi gidan da wani irin katako ne mai inganci da k’arko akayi shi sai kuma gilashi da kake hanyen rabin komai na ciki daga wajen, sai filin rairai kuma a duk inda babu ruwan.
Richard juyawa yayi ya koma shi kuma yana d’auke da ita ya taka matakalar wacce ita ma ta katako ce, saida yayi dubarar saka makulli ya bud’e suka shiga, zaunar da ita yayi kan kujera ya juya kamar zai fita ya kunna wutar data gauraye wurin.
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:18 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LABARI*
SAMIRA HAROUNA
*SADAUKARWA GA*
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
4锔忊儯1锔忊儯
A take ta k’ara bud’a idonta tana kallon d’akin, mamaki ne sosai da kuma abun birgewa ta gani, ko ina hotunanta ne a kafe tun daga yarintarta har zuwa yanzu girmanta, wasu hotunan tare da Abhi d’inta wasu kuma ma tare da mahaifiyarta tun bata da wayo. Kamar wata yar k’auye haka ta saki baki da hanci tana juyawa ta ko ina inda hawaye suka shiga mata zarya ba tare data sani ba tsabar kewar iyayenta da taji a lokacin, dafa kujerar tayi ta mik’e tsaye tana tokare da k’afar bata yarda ta taka ta ta shiga janta tana k’ara zagaya d’akin tana kallon hotunan.
Ganin hankalinta ya tafi can shi kuma dama yana zuwa nan d’in saiya samu damar ciro wayarshi ya duba sak’on, wani murmushin gefen labb’a yayi ya jinjina kai ya juya ya kalleta yace “Zan gano komai, zan gano abinda kika so fad’a d’azun.”
Mayar da wayar yayi a aljihu ya shiga takawa a hankali ya matsa kusanta, jin motsinshi yasa ta juyowa da sauri, suna had’a ido tace “Ina ne nan? Me yasa ka kawo ni nan?”
Kallonta yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya rab’ata ya shige ciki, tana ci gaba da kalle kallenta tana juyowa kawai suka had’a ido, saida gabanta ya fad’i a taken nan, tuni tsoro ya shiga zuciyarta saboda yanayin kallon da yake mata. Da k’yar ta shiga kiciniyar dawo da nutsuwarta, wuk’ar hannunshi ya d’ago yana d’an bubbugata a d’aya hannunshi yana kuma kallonta kallon da babu alamar wasa a ciki, wata zabura tayi har ta nemi fad’uwa tayi nasarar dafe wata yar kwabot d’in dake bayanta harta ture wani hoto ya fad’i ya fashe, gefe tayi dan gudun karta taka kwalbar a tsorace tana ci gaba da kallonshi, cikin nutsuwa ya shiga bin gabanta a hankali yana mata wannan mugun kallon. Gwajam taji ta fad’a kan kujera dan dama k’afar janta ne kawai take, ganin yana nufota a tsorace ta shiga fad’in “Dan Allah mr. karka kashe ni, ka fad’a min abinda kake so nayi alk’awarin zan baka, na rok’eka karka cutar dani dan Allah.”
Saida ya zo kusanta ya durk’usa gabanta ya d’ora wuk’ar kan cinyarta ya dafe hannayenshi akan kujerar ya sakata tsakiya, jingina tayi a bayan kujerar tana kallonshi, ido cikin ido yace “Me zaki iya fad’a min game da maganar zubewar cikinki?”
Zaro ido tayi a firgice cikin tashin hankali ta shiga fad’in “Bbbn…bbba..komai.”
Sunkuyar da kanshi yayi cikin gadara yace “Kinga wuk’ar nan?”
D’aga kafad’a tayi alamar eh, jinjina kai yayi yace “To ba barazana zan miki da ita ba, huda mak’oshinki zanyi da ita kika sake min k’arya.”
Da sauri ta rik’e hannunshi da duka hannayenta biyun sanda yayi niyyar d’aukar wuk’a, cikin rarrashi ta shiga cewa “Zan fad’a maka, zan fad’a zan fad’a, karka cutar dani wallahi zan fad’a maka gaskiya.”
Kallonta yayi yace “Ina jinki.” Saida ta had’e yawu tana kallonshi duk cikin firgici tace “K’arya na maka, ka yafe min karka min komai, nayi tunanin ba zaka barni na dawo nan ba indai ina da cikin nan, kuma naga matarka zata kasheni da abinda yake cikina, a dalilinta ne na kusa mutuwa, shiyasa na tsorata nace likitan su fad’a muku cikina ya zube amma gaskiya sun ce yana nan bai zube ba.”
Sakin hannunshi tayi tana wani kukan tausayi tace “Ka yafe min.”
D’aukar wuk’ar yayi ya aje gefe, mik’ewa yayi cak ya d’auketa ya shiga da ita wani d’akin bacci, ajeta yayi yace “Kiyi sallah.”
Tana ganin fitarshi sai kawai ta fashe da kuka ta fad’a kan gadon, duk komai taji ya jagule mata ta rasa me ke mata dad’i ma, ta jima tana kukan tausayin kanta kafin ta bud’a wradrob d’in data gani, abun farin ciki kam kaya ta samu wanda da gani daidai awon da take sakawa ne alama dan ita aka aje, sai dai ba kayan da zasuyi sallah bane, da k’yar ta samu abinda ta rufe kanta dan lokaci nata wuce mata tayi sallah, daga nan zaune tayi duk azkhar d’inta na safe.