SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Shogowa kawai yayi d’auke da farantin abinci ya aje, kusanta ya tsaya ya kamata ya zaunar da ita kan gadon, saida ya mik’ar da k’afafunta sannan ya d’auko abincin ya aje gabanta, zaune yayi gabanta ya shiga gutsiro komai yana saka mata a baki, bata mishi musu ba sai karb’a, dan yanzu kam tsoronshi take ji sosai burinta yanda zata rabu dashi ne. Sam babu mai kallon idon wani har saida ya saka mata wata loma tare da fad’in “Wannan wajen hutawar Abhinki ya so baki kyautarshi ne a matsayin kyautarki k’arin shekararki, amma Allah bai nufa ba har ya rasu.”
Cikin shashek’a kuka tace “Ya akayi kasan da wurin nan kai? Abhina yana min bazata ne wajen bani kyautar k’arin shekarata, kana so ka ce kai ya fad’a maka kenan tun ni bai fad’a min ba?”
Fuskarta ya kalla yace “Saboda ni na samo wurin, ni ya bawa alhakin kula da wurin, sannan bai min shamaki da shiga ko ina a gidan nan ba.”
Hannu tasa ta sake goge hawaye tace “Ina kewar iyayena sosai, ina son ganin kakani na, ina son wani a kusa dani da zan fad’awa abinda ke damuna, please ka kira min kakata.”
Cikin lura da duk hawayen dake saukowa a idonta ya ga hawayen da suka d’iga cikin kofin lemun dake kusanta sosai, d’aukar kofin yayi ya kafa kai ya shanye tas sannan ya aje yana kallonta, har zai d’auki farantin abincin sai kuma yace “Kin k’oshi ne?”
Tsayawa tayi da kukanta tana kallonshi da mamakin jin yanda bai damu da matsalarta ba, ganin ba tace komai ba yasa shi mik’ewa ya d’auke farantin ya juya ya fita Pillown dake bayanta ta jawo ta k’amk’ame tana wani kukan marar sauti.
…Ba wai daidai gwargwado bane k’ololuwar kulawa ce yake bata, har mamaki take idan tayi nufin wani abu da kanta sai taga ya taimaka mata tayi, matsalarta dashi kawai basa wata maganar arzik’i, daga d’aure mata fuska sai harara ko ya mata magana cikin gatse, ita kuma dama tunda suka zo gidan sai mutuwar iyayenta ta dawo mata sabuwa fil, dan haka yanzu ta daina walwala ko farin ciki sai dai tayi shiru, yar maganar dake shiga tsakaninsu k’alilan ce.
Ta wani b’angare kuma yanzu haka Farha na kan hanyarta ta zuwa, da taimakon Kasim da kuma Mustafa suka mata komai bayan an mata passeport visarta ma ta fito saboda ganin darzar amarci ne zata tafi, taji ta kamar zatayi rashin lafiya saboda kad’aici da kuma keta hazo, sa’arta d’aya wata babbar mace data samu a jirgin ita ma zatayi tafiya, ita ce ta d’an zama suna magana har jirginsu ya sauka inda zai tsaya.
Da safe zasu tafi asibiti kamar yanda aka ce su koma bayan kwana uku, tana cin break yana tsaye yana danna waya ba tare daya kalleta ba yace “Zaki iya min wani taimako?”
A tak’aice ta kalleshi ita ma tace “Uhum!”
Sai lokacin ya kalleta yace “Farha ta zo, zaki iya magana da drivernki su d’aukota tunda yanzu asibiti zamu je?”
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tara mishi hannu tayi tace “Naga wayarka.”
Mik’a mata yayi ta d’anyi danne danne ta kara a kunne, kallonshi tayi kafin a d’auka tace “A kaita can gidan nan? Ko nan?”
Ba tare daya kalleta ba yace “A kaita can, mu ma daga asibiti can muka nufa.”
Ba tace komai ba sai magana da yaji tana yi a wayar, ba wani jimawa ta kashe kiran ta mik’a mishi ya karb’a, yunk’urawa tayi zata tashi yayi saurin soka wayarshi aljihu ya zo ya kamata, bata wani cire rai da cewa zai d’auketa ba dan kusan haka yafi yi yanzun, hakane kuwa ta faru cak ya d’auketa suka fita, mota ya sakata a gidan gaba kafin suka d’auki hanya.
Ta d’an jima tsaye tana kalle kalle ta rasa inda zatayi sai lambar daya turo mata take ta k’ok’arin kira, ta sake danna lambar ta aika kira wata zuk’ek’iyar mota ta tsaya gabanta fara fat da ita, irin motar nan da ake kira limozine, bata kula ba sai k’ok’arin sauraren turancin da ake mata a wayar take, daga gidan gaba matuk’in ya fito ya zagayo inda take, cikin rusunawa ya d’an sunkuya yana fad’in “Barka madame, zamu iya tafiya.”
Jakarta taga ya kimkima zai saka a boot, da sauri ta rik’e tana fad’in “Malam waye kai? Ina zaka kai min jakata?”
Duk da bai fahimci komai a zancenta ba ya dai gane bata yarda dashi ba, gyara tsayuwa yayi yace “Madame Sarah ce ta turo ni na d’aukeki, tace ke k’awarta ce da zata zo.”
Ita ma bata gane komai ba sai sunan Sarah da taji ya fad’a, dama french ne yayi zata iya gane wani abun, sakar mishi jakar tayi tana binshi da harara tana tab’e baki, saida ya saka jakar a baya ya dawo ya bud’e mata k’ofar yana jiran ta shiga, kallonshi tayi ta kalli cikin motar sai kace wani d’aki luf luf da ita, cikin wani haushi haushi bak’in ciki bak’in ciki ta shiga da sauri ya mayar ya rufe, da sauri ya zagaya ya shiga ya fara jan motar cikin nutsuwa har suka haura titi.
Gaba d’aya mantawa tayi da b’acin ran da take ji na k’in zuwan Salahadeen, kallon cikin motar take sosai duk ji take kamar a wani d’aki ne take gicire kan gado, saida ta gama kallon komai kafin ta mayar da kallonta ga titi ta shiga kallon gari da gararin garin, ita dai bata ga komai ba banda dogayen gina gine da jajayen fata abubuwan mamaki al’ajabi da kuma dariya da haushi. Wata tattausar tsayawa da taji motar tayi ne yasa ta kallon gabanta, wata k’atuwar k’ofa ce bak’a ta k’arfe mai raga raga wacce kake iya hangen cikin gidan, bata ga waya bud’e ba bayan wani katin shaida data ga driver ya nuna a daidai wani d’an k’aramin akwati mai d’auke da lambobi, sai kawai taga k’ofar ta bud’e sanda a majigin ya d’an hasko wani rubutu da bata iya ganin me aka rubuta ba, shigewa yayi hakan yasa dole ta sake juyawa dan tana so taga mai kula da k’ofar, amma sai taga ta mayar da kanta ta rufe hakan na tabbatar mata da k’ofar auto. ce.
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:19 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LABARI*
SAMIRA HAROUNA
*SADAUKARWA GA*
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
4锔忊儯2锔忊儯
Tsayawar motar a daidai k’ofar shiga tabkeken falon ya dace da shigowar wata motar a cikin gidan, driver ne ya bud’e mata ta fito tana kallon k’ofar shiga da mutane masu kama da ma’aikatan ke fitowa, duk tsaye sukayi suka jeru suka had’e hannayensu suna kallon duka motocin suka ta inda zata fito. Wata tsohuwa ce ta fito cikin riga da wando ta tsaya ita ma, duk kallonsu take kamar yanda suma suke kallonta babu wanda yace wani abu.
Salahadeen ne ya fito a d’aya motar daworsu kenan daga asibiti, rufewa yayi ya zagaya ya bud’e, rik’e hannayenta yayi ta fito ya mayar da k’ofar ya rufe, a hankali suka shiga takowa har suka matso kusan mutanen, tana kallonsu ta ga kakarta, tsaye tayi tana kallonta da mamakin kasancewarta anan, wasu hawayen farin ciki ne taji sun cika idonta, zame hannayenta tayi daga hannunshi ta shiga jan k’afarta da sauri, ita ma tana ganin yar jikar tata wacce mahaifinta ya rabasu da ita ta saki murmushin jin dad’in ganinta, da sauri ta taho hannayenta bud’e suka rumgume juna, kuka Sarah ta saka ita kuma tana daddab’ata tana fad’in “Come on beby, stop craying, i am here now.”