NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Sake k’amk’ameta Sarah tayi tace “Ya akayi kika zo nan my granny?”

A hankali ta d’agata daga jikinta tana kallon Salahadeen daya matsa kusan Farha yana magana da ita, nuna mata shi tayi da baki tace “Yaron kirki ne, da fari sawa yayi aka satoni daga gidana, saida na zo nan ya fad’a min komai a game dake.”

Kallonshi tayi tana dariyar abinda Kaka ta fad’a tana mamakin yanda ya k’ware wajen sace mutane, daya fad’a maka abinda ke faruwa ko zai faru ya taho da kai cikin dad’in rai ya gwammace ya d’aukoka kawai ka d’auka saceka yayi.

Kallonta tayi taja d’an k’aramin tsaki irin na damuwa tana sake rik’e hannayenta tace “Sorry my baby, kin rasa komai ta wata fuskar, amma kina da komai ta wata fuskar.”

Rumgumo fuskarta Sarah tayi da hannayenta ta sumbaci kumatunta tace “Ki yafe min granny, na manta dake bana zuwa inda kike.”

Shafa kumatunta tayi tace “Babu komai my baby, muje ciki ki huta na shirya miki abincin da kika fi so, sannan naji ya lafiyar wannan k’aramin prince d’in.”

Zaro ido tayi da dariya cike da jin kunya tace “Granny! Who told u that?”

Dariya tayi ta kamata a hankali suka nufi k’ofar shiga tana sake nuna mata Salahadeen, kallonshi tayi sai taji ranta bai mata dad’i ba ganin ya wani tsaya gaban Farha sai magana yake mata k’asa k’asa ita kuma tana wani kumbura baki. Ma’aikatan da su Sandra ne suka shiga gaisheta dan dayawansu sabbi ne basu santa ba bata san su ba, ba tare data kalli Farha ba ta kalli Sandra ta nuna mata Farha tace “Ku sauketa a d’akin daya dace, ki ware mata ma’aikaciya guda da zata kula da duk wata sabgarta.”

Cikin girmamawa tace “Angama princess.” Ta fad’a tana kallon wata ma’aikaciyar, ciki duk suka shige inda kaka ta shiga bawa jikarta kulawa, saida ta ci ta k’oshi harta fara mata kukan shagwab’a sannan ta rakata d’akinta dan tayi wanka, bayanta ta tsaya ta cire mata zip d’in riga ta zageta ta sauka k’asa, da sauri ta juyo gaba tana rufe da k’irjinta da hannu tana fad’in “Granny, ba fa yarinya bace ni yanzu, ki barni zanyi da kaina.”

Gwaleta tayi da fad’in “Kinsan da ko uwarki yarinya ce a wurina bare ke?”

Cikin turo baki tace “I know.”

Towel d’in ta d’auka ta d’aura mata a k’irji ta rakata ta shiga ban d’aki, sosai ta nutsu tayi wanka ta jima a ciki kafin ta fito, Kaka da kanta ta shafeta da lotion d’inta ta bata riga da wando masu taushi sosai marar nauyi ta saka, tana zaune bakin gadon Kaka na tsaye tana tsefe mata kai tana gyara mata shi da mayuka, anan take sake tambayar duk abinda Salahadeen ya fad’a mata, ita kuma mamaki tayi yanda ya zaunar da Kakar ya fad’a mata komai, me yasa ya fad’a mata har aurensu da samun cikinta? Me yasa ita kad’ai ce baya zama yayi doguwar magana da ita ta fahimta?

Kaka ce ta katse mata tunani da fad’in “My baby me yasa kika yarda kika sauke matarsa anan gidan? Me yasa kika yarda kika auri mutumin dake da mata? Akan me zaki yarda ki raba mijinki tare da wata?”

Hangenta tayi ta madubi tace “Granny! Meya matsalata dashi to? Ba komai tsakaninmu sai auren bogi da jahun cikin daya shiga jikina nashi, ina haife masa abinda ke cikina kowa zai kama gabansa ne.”

Lek’o fuskarta tayi da mamaki ta kalleta tace “Kina lafiya kuwa baby? Yaron daya fad’a min ido da ido cewa shi fa ba zai rabu dake ba, har ya nemi izinina na son komawa dake k’asarshi, a hakan kike tunanin ku rabu cikin sauk’i?”

Jaye kanta tayi ta juyo da mamaki tana kallonta tace “Granny shi ya fad’a miki haka?”

Cike da tabbaci tace “Eh mana baby.”

Girgiza kai tayi ta sake juyawa tana fad’in “Yaudara ce kawai granny, yana so na koma k’asarsa ne, ni kuma ba zan tab’a komawa ba, mutumin da banda muzurai da hantara babu abinda yake min.”

Tana gama d’aure mata gashin da k’aramin ribom ta zauna gefen gadon tana kallonta tace “So, teld me about u? Me yake tafiya a rayuwarki ta b’oye?”

Ajiyar zuciya ta sauke ta taso daga kujerar ta haura kan gadon, hakan yasa Kaka juyawa inda take tana kallonta, d’ora kanta tayi saman k’afar kakar, a hankali ta shiga shafa kanta wanda yasa Sarah lumshe ido tace “Kaka ina kewarsu sosai, ina ma suna nan a raye! Da sun kasance kusa dani sun kula dani, ina so naji d’umin mahaifiya a kusa dani granny, ina son jin kalaman Abhi sanda yake furta min kalmar princess, wannan kalmar tafi dad’in ji daga bakinshi fiye da kowa.”

Ajiyar zuciya ta sauke ta bud’a ido wasu siraren hawaye suka sauko mata kan kumatu, sake gyara kanta tayi tace “Yau ga princess d’in Abhi da ciki a jikinta, sai dai Abhi baya nan bare ya ga jikanshi da ido ya mishi gata ninkin baninkin wanda ya min.”

Tsayawa tayi da shafa kanta tace “Baby na fahimci abinda kike ji, kiyi hak’uri kinji, hak’ik’a ina sonki kamar yanda nake son Samantha dana haifa, ke jikata ce k’waya d’aya k’wal da nake da ita.”

A hankali tace “Na sani Kaka, kina sona sosai, Abhina ne kawai ya nesanta ni daku, bansan me yasa ba?”

Shafa kanta tayi tana murmushi tace “Abhinki ya nesantaki damu ne saboda baya son kiyi muguwar shak’uwa damu wacce zata iya sawa wata rana ki bijire masa kuma kiyi nesa dashi, soyayyar da Abhinki ke masa tasa ya manta da cewa macece ke zaki iya yin aure, kowane motsi naki inda a nesa dashi kike to akan idonshi kike yin shi, kusan nace miki yana da masu kirga miki saukar numfashinki duk saboda mugun tsaron da yake baki.”

Cikin mamaki ba tare data d’ago ba tace “Amma granny me yasa Abhi yake min duk wannan tsaron?”

Lek’a fuskarta tayi tace “Wannan ne kuma ban sani ba, amma dai a zahiri ya nuna son da yake miki ne.”

Jawo hannun Kakar tayi ta rumgume a tsakiyar k’irjinta tana fad’in “Dan Allah granny ki zauna anan, kinga baki da kowa yanzu acan banda masu miki aiki, ki zauna muyi zamanmu anan, kinji?”

Shiru kaka tayi kafin tace “Ba zan iya zama anan ba baby, amma na miki alk’awarin idan na koma nan da kwana biyu zan sake dawowa na ci gaba da kula dake har ki haihu lafiya.”

Cikin shagwab’a tace “Me yasa granny? Ba kya son zama tare dani ne? To ni zan biki can mu tafi tare.”

Dariya tayi tace “Ba haka bane, amma idan zaki je can zanfi kowa jin dad’i.”

Dariya tayi ita ma suka zubawa k’ofa ido da aka k’wank’wasa, Kaka ce tace “Yes come in.”

Bud’ewa akayi aka shigo, Salahadeen a gaba sai Farha a baya wacce ta gama mishi mitar bai je d’aukarta ba, ya fad’a mata asibiti suka je sannan ta koma tambayar ina ne nan ya kawota? A take ya fad’a mata gidan Sarah ne, cikin jin haushi da mamaki tace “Gidan Sarah kuma? To me yasa ka kawo ni nan? Dama a gidanta kale zaune duk zaman nan da kayi a baya?”

Cike da k’aguwa yace “A’a ba haka bane, ina da nawa muhallin, wannan kuma nata ne inda take son tayi jinya, ni kuma jinyarta na zo yi banda hurumin hanata abinda take so.”

Juyawa tayi tace “A gaskiya ni ba zan iya zama anan ba? Ka kaini gidanka kawai ko kuma na koma.”

Zaune yayi bakin gadon yana cire takalminshi k’afa ciki yace “Wuce, idan kin koma ki gaishe min dasu k’warai.”

Kallonshi tayi da mamaki amma sam bai kula ba, k’aramin tsaki tayi ta juya inda jakarta take ta d’auko, bud’awa tayi ta d’auko dalleliyar wayar Sarah ta mik’a mishi tana fad’in “Wayarta ce inji Mama tace a kawo mata.”

Kallonta yayi cike da taushe abinda ke zungurarsa yace “Aikena ne kike kenan na kai mata?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button