NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Janye hannun nata tayi da wayar tace “A’a, yi hak’uri.”

Harara ya wurga mata yace “Ki samu kiyi wanka sai mje na rakaki ki kai mata, sannan ki mata godiya na masaukin data baki a gidanta.”

Wani yatsina fuska tayi sai dai bata ce komai ba ta aje wayar ta juya, har zata shiga k’ofar data tabbatar ta ban d’aki ce aka k’wank’wasa k’ofar, k’arasawa tayi ta bud’e taga wannan baturiyar ce data musu jagora zuwa d’akin nan, cikin ladabi a harshenta tace “Madame an gama shirya miki break, zaki sauko ne ko kuma kina buk’atar a kawo miki nan ne?”

Jim ta d’anyi cikin rashin jin dad’in kasa fahimtar zancenta, kafin tayi wani yunk’uri daga inda yake zaune yace “Ki barshi acan zata sauka k’asa.”

Sunkuyar da kai tayi tare da rusunawa ta juya ta tafi, rufe k’ofar tayi ta wuce ban d’aki tana jin takaici yanda zata fara fahimtar yarensu.

Tayi wanka ta shirya cikin riga da siket d’inta masu kyau na leshi wanda suka karb’i jikinta, tare suka sauka dashi k’asa inda ta dinga kallon kusurwar da zata sadasu da wajen cin abincin, komai na wurin kallonshi take duk da kuwa k’ok’arinta na son ganin ta d’auke idonta ta basar, wasu mahaukatan kujeru data gani had’i da carpet da canter table d’in data gani a falon sai taji kamar tayi wuf ta koma dasu ta aza su falon gidanta, d’aukar idonsu kawai ya ishi ya tabbatar maka zasuyi dad’i da laushi wajen zama, tsarin abun ya birgeta sosai babu k’arya, ga wata bangagejiyar cobot ta glass wacce ke jere da kwalaben lemuka iri iri masu tsadar tsiya, duk da k’amshin bana turaren wuta bane amma dai sanyayyen k’amshin ya kashe mata duk jikinta. Sam bata lura da sun iso wajen ba saida taji tayi karo da mutum, da sauri ta kalli gabanta sai ta ga Salahadeen ne daya tsaya da nufin nuna mata wajen zaman.

Mayar da kallonta tayi ga wajen daya nuna mata da nufin kallon kujerar, amma sai taji ta zarme da kallon wani ramfatsetsen teburin glass dank’arere d’auke da wasy watsa watsa plate na tangaren dana silba d’auke da… Ba zata kirashi da abinci ba dan wani abun bata san ma miye ba ko a ido bare a suna, banda albasa da ganyen salade da kuma tumatur da gasassen kaza data gani a gudanta an mata kwalliya bata san komai ba. Wasu wutace dake kunne masu bada haske kalar ja wani d’umi d’umi ne ke fita a wurin wanda ke ratsa fatar jiki har kaji kamar ka tabbata a wurin, wani matsakaicin carpet ne shinfid’e a kasan dinning d’in, wannan ma’aikaciyar ce ta matso tana ja mata kujera, saida ta sauke ajiyar zuciya ta kalleta ta matsa ta zauna, kallon gabanta tayi inda ma’aikaciyar ta tambayeta me zata ci? Salahadeen ne ya fad’a mata abinda sam Farha ma bata ji me ya faru ba, hankalinta ya tafi kan bangon dake gefenta da taga yana wani k’yalk’yali kamar da walk’iya a cikinshi kamar kuma wani abu ne aka shafeshi dashi mai kwalliya.

Da sauri ta juya inda taji motsin mai aikin, fridge ce ko drower ba glas ita ma bata sani ba, bata tabbatar da fridge ce ba saida taga kayan cikinta sanda aka bud’a, mak’il take da kayan sha kawai kala kala, d’aukowa tayi ta bud’e wata tartsetsiyar kwalba mai kyau ta d’auki kofin tangaren ta tsiyaya mata lemun mai kauri da kalar ja sosai, tana aje musu tace “Da wani abunda kuke buk’ata?” Salahadeen ne yace “No u can go.”

Juyawa tayi ta fita, kallon Farha yayi dake kallon abincin gabanta, murmushi yayi a b’oye tare da nuna mata plate d’in yace “Bismillah, zaki iya ci ko na samo miki wani abu?”

Cikin sanyin jiki ta girgiza kai alamar a’a, cokalin ta d’auka mai yatsu ta d’an tsakuro salade d’in, data kai baki da k’yar ta taune shi ta had’e dan baida maraba da wanda ba’a saka komai ba, to dama tumatur da albasar yanka ne aka musu mai fad’i kuma ba’a yamutsa shi ba haka kawai, wani abun data gani ta sakankance da cewa zaifi dad’i, tsakura tayi shima a hankali ta sake Bismillah ta kai bakinta, tana taunawa ta tsaya tana kallon Salahadeen saboda zak’i taji a maimakon gishirin da take tunanin abun na da shi, aje cokalin tayi cikin b’acin rai tace “Yaya ni gaskiya ba zan iya cin abun nan ba, haba komai wani iri a baki ba dad’i.”

Kallonta yayi yace “Ga nama nan ki ci mana, idan kina son jin d’and’ano sosai ga robar gishiri sai ki k’ara.” Ya fad’a yana nuna mata yan robobin dake rufe da huda guda uku a samansu, kallonshi ta sake yi tace “Allah ya kiyaye in ci yankan kafirai, sun yanka naman ba Bismillah zan ci, ba zan iya ba gaskiya kawai ka nemo min wani abun, tun a jirgi haka suka dinga bani wani shegen abu kamar wake da shegun ruwa yan kad’an.”

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta da murmushi yace “Ashe Sarah k’ok’ari tayi data iya cin abinda bata tab’a ci ba lokaci d’aya, yanzu kin fahimci wani abu game da haka ko kuma har yanzu kan naki a toshe yake?”

Turo baki tayi gaba ta kawar da kanta ba tace k’ala ba, mik’ewa yayi yace “Muje ki kai mata wayarta sai mu fita.”

Mik’ewa tayi suka nufi babban falon, shi ma bai cika zuwa gidan ba idan ba muhimmin aiki zai yiwa mahaifinta ba, dan haka bai san kusurwar inda zai ga d’akinta ba saida ya tambayi wata ma’aikaciya dake tafe da n’aurar wanke carpet duk falon ya cika da k’arar n’aurar, ita ce ta nuna mishi inda zaiyi kafin suka wuce shine fa yanzu suka shigo a tare.

Ganinsu baisa ta tashi daga k’afafun Kakarta ba sai ido data kallesu lokaci d’aya ta d’auke idonta, kakar ce ta nuna musu wata lallausar sofa dake gefensu tana fad’in “Ku zauna mana.”

Zaunawa sukayi sai Farha dake bin d’akin da kallon cikin dubara, wasu hotunan zane data gani ta d’an tab’e baki tana ayyanawa a ranta ko miye anfanin mak’alasu a d’akin (milyoyin kud’i kenan), a hankali ta maido kallonta kansu sanda Kaka tace “Yarinya ya hanya? Ina fatan dai kin ci abinci?”

Salahadeen da baya so su fahimci bata jin yaren yayi saurin sakin murmushi yace “Eh Kaka ta ci.”

Kallon Sarah yayi yace “Princess ya k’afar taki?”

Mamakin yanda ya mata magana yanzun yasa ta saurin d’aga ido ta kalleshi, suna had’a ido ta sunkuyar da nata tana fad’in “Da sauk’i.”

Jinjina kai yayi yace “Anjima zamu fita ki fara taka k’afar.”

Farha ya kalla yace “Muje ko?”

Mik’ewa tayi hakan yasa shi mik’ewa shima, tare suka nufi inda su Sarah suke ta mik’o mata wayarta tana fad’in “Mama tace na kawo miki wayarki.”

Mik’ewa tayi zaune ta mata murmushi tasa hannu ta karb’a tace “Thank u.”

Tashin da tayi ne ya fallasa shara-shara rigarta wacce ko bras bata saka daga ciki ba, a take Farha ta hangi gabanta wanda duk da kasancewar mace kuma wacce ta fita su masu girma saida taga sun birgeta, tsaye suke cirr inda daga k’asa suke da fad’i kuma jajir dasu, abun birgewa ma yanda sukayi wani pumpum dasu. D’auke kanta tayi daga kallonta ta kalli gefenta da yake tsaye, tuni ya hangi abinda ta gani ita ma wanda yake mallakinshi ne, saida gabanshi ya fad’i yaji jikinshi yayi sanyi sosai, sab’anin abinda Farha taji na birgeta shi harda sha’awar tab’asu yaji, yaji yana so ya rumgumesu da tafukan hannayenshi ya saka su a bakinshi ya d’umamasu da yawun bakinshi.

Wasu yawu ya had’iya ya lumshe ido ya bud’e a kanta data koma k’afar kaka ta fita shirginsu kuma, a hankali cikin french daya tabbatar Farha zata gane yace “Ki cire rigar nan mana, ko kina so sai kowa ya gama kallon abinda baida hurumi akai ne?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button