NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Tashi tayi zaune tana ci gaba da kallonshi tace “Sorry? What do u mean?”

Gwiwar k’afarshi d’aya ya durk’usar a gabanta inda ta mik’e k’afarta mai ciwo, a hankali ya shiga shafa bandejin k’afar yana kallon k’afar yana fad’in “Ki rufa min asiri Sarah Abhi, ki taimake ni ki ceci rayuwata ki canza rigar nan, ina kishinki sosai ya kamata ki fahimci haka.”

Cikin dubara ya had’a ido da ita ya wurga mata wani kallon gargad’i, saida taji gabanta ya fad’i tayi saurin d’auke idonta, Kaka ce ta dafa kafad’arta tace “Kiyi abinda mijinki yace baby, bari na d’auko miki ki canza.”

Matsawa Farha tayi baya tana kallon yanda ya durk’usa k’asa yana shafa k’afarta, wata rigar Kaka ta d’auko ta kawo mata mai kauri, karb’a tayi tana kallonshi yana mik’ewa tsaye, da kallo ta bishi har suka fita ta cire rigar ta saka wacce, kumburo baki tayi ta kalli Kaka dake mata dariya.

Gyara kwanciyarta ta d’auki wayarta ta duba iya abinda zata duba, a jerin kiraye kiraye taga lambar Sajida wacce ko suna bata saka ba ta dai aika kirane ta datse tun kafin tayi k’ara lokacin hankalinta na kan tafiyar nan, suna ta saka hakan yasa ta samu lambar a jerin masu WhatsApp, shiga lambar tayi ta tura gajeran sak’on cikakkiyar sallama daga k’asa ta rubuta sunanta da sunan mahaifinta ta tura. Har ta fita a lambar sai kuma ta lura da akwai hoto a profil d’in, shiga tayi dan dubawa kawai sai taga wani abun al’ajabi.

Maza uku ne tsaye sai mata biyu zaune akan kujera tare da wani kyakyawan dattijo da suka saka tsakiya, dattijon da alama mahaifinsu ne dan duk kamarshi ta fito a fuskokin yaran ban da d’aya wacce kuma kamar ita ce k’arama a ciki wacce ke da duhun fuska, amma daga Sajidar har sauran mazan duk sai taga kamarsu sosai a fuskarshi. Ba wai kamar da suke dashi bane ya tafi da tunaninta sai yanda dattijon ke da matuk’ar kama da Abhinta, Abhinta? Eh sak Abhinta ne wannan mutumin, gashi babu abinda ya raba su dashi, kyawu jar fatar k’asumbarsu da murmushin dake kan fuskarshi ma sanda ya rumgumo yan matan a jikinshi, dafe goshi tayi ta sake zoomin hoton ta matso kusan Kaka tace “Granny look, kamar Abhi na ko?”

Kallo tayi da kyau sai kuma ta kalleta tace “Yeah, wanene shi?”

Girgiza kai tayi tana kallon fuskarshi tana jin kamar akwai wani abu tsakaninta dashi, ciza yatsunta tayi tace “I dont know, but wani abu zai faru granny.”

Lusmhe ido tayi ta d’aga hannunta d’aya tace “Allah kasa abinda nake tunani ne zai faru.”

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:19 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                  4锔忊儯3锔忊儯

Saida ya fara sama mata sandwich ta ci kafin ya d’anyi yawo da ita suka dawo gida, a lokacin rana tayi sosai alwala sukayi ita ta kabbara sallah a gida shi kuma ya tafi masallacin dake bayan gida nesa da nan. Waben Sarah ma sanda tayi alwala ta kabbara sallah kallonta Kakar ta shiga yi da mamakin me take yi haka? har ta kammala bata daina kallonta ba, tana idarwa ta juyo ta kalleta tayi murmushi tace “Granny ya da kallona haka kamar baki gane ni ba.”

Da mamaki tace “Baby me kikayi haka? Meye wannan kuma?”

Murmushi ta sake yi ta tashi daga kan carpet d’in, kusanta ta zauna ta kalleta sosai tace ‘Granny sallah nayi, na gana da mahallici na ne ubangijin sammai da k’assai, sarkin daya busa mana numfashi kuma rayukanmu suke hannunshi, ubangijin daya tsara mana yanda zamu rayu bayan ya halluci mu, ubangijin daya mana ni’imomi dayawa daga ciki harda iskan da muke shak’a, Allahn daya hallice mu kawai dan mu bauta masa.”

Wani kallo ta bita dashi mai fassara yanda al’amarin ya girgizata tace “Baby wannan ubangijin naki duk shi ke da wannan kirarin haka?”

Wata yar dariya tayi da bata shirya mata ba tace “Granny, banda ilimin da zan iya kirari wa ubangijina, saidai muna kamaltawa ne kawai abisa wasu siffofinshi daya siffanta kanshi dasu da kuma sunayensa da suka zo mana a cikin littafi da kuma sunna, kirani na masa a tak’aice yanda zaki fahimta, sannan na fad’a miki aiyukansa a fakaice, sannan na fad’a miki ni’imomin daya mana wanda ba dan tausayi da rahamarsa a garemu ba da tuni ya kifar da duniyar saboda zunubanmu, amma ubangijina mai tausayi ne da jink’anmu kamar yanda yasha kiran kansa da sunan nan a cikin littafi mai tsarki.”

Had’e fuska tayi hakan ya bayyanar da tamuk’ewar fatarta tace “Baby sai naji duk kalamanki sun canza kamar bake ba, kina lafiya kuwa? A ina kika koyi maganganu irin wannan?”

Wata dariyar ta sake yi ta kamo hannunta tace “Granny kad’an daga mu’ujizar Alqur’ani kenan, idan ka fara fahimtarshi cikin sauk’i tunaninka ke washewa, sannan rayuwarka tayi haske tamkar mutumin k’auyen dake rayuwa shi kad’ai a tsakiyar dajin da babu ko hasken farin wata amma ya dawo babban birnin da ake ji dashi wajen k’awatuwa, sannan ya yalwata zuciyarka ka zama mafi kyawan d’abi’u, bugu da k’ari ya warware duk wani k’ullin dake kan harshenka, dad’in-dad’awa ya k’ara maka fasaha da zalak’ar harshe ta yanda makarancinshi da jahilinshin basa zama d’aya ko wajen zancen daya shafi duniya.”

Wani yanayi ne da bata san lokacin daya risketa ba tace “Abun mamaki baby, wannan wane irin addini ne haka?”

Saida ta lak’aci kumatunta tace “Addina shine addinin mahaifina kuma addinin wanda kike mishi kallon mijina ne, addini na shine addinin da Allah yace lallai addini a gurin Allaj shine addinin islama, sannan addinin da duk wanda ya mutu akanshi ake kyautata masa samun ceton ubangijinshi Allah, annabawan Allah da ma bayin Allah, dan a wannan ranar aboki ma kan ceci abokinshi, addinin da nake kai granny shine addinin da fiyayyen hallita kuma masoyi d’an gatan Allah yayi wafati a kai, addinin musulunci kenan.”

Jinjina kai tayi cike da wani sanyi da jikinta yayi tace “Tabbas mahaifinki ya tab’a fad’a mana shi musulmi ne kafin aurensu da Sam, amma ban tab’a jin irin kalaman nan daga bakinshi ba.”

Murmushi tayi ta mik’e tsaye tana fad’in “Muje muyi lunch, a waje nake son cin abinci ma yau granny.”

Mik’ewa tayi suna rik’e da hannun juna tana takawa a hankali suka fita, a falo ta samu d’aya daga cikin ma’aikatan zata wuce, Sarah ce tace “Ki fad’awa Sandra a waje zamuyi lunch.”

Saida ta sunkuya tace “Ok mme.” Sannu sannu suka ci gaba da takawa har suka fita, ciwon k’afarta da kuma tafiyar dake tsakaninsu da wajen zaman yasa su shiga wata yar mota mai rumfa a sama wacce dama aikinta kenan tak’aitawa wanda baisan doguwar tafiyar dale cikin gidan, suna isa suka samu kujeru suka zauna, dama kuma wajen zaman mutum hud’u ne a wurin, amma an k’awatashi sosai da da shinfid’a da kayan kwalliya, wayarta ta d’auka ta shiga dannawa, cikin sa’a kam ta samu Sajda en ligne ta amsa sak’on sallamarta har tana tambayarta tana ina ya yanzu? Kuma yaushe zata dawo makaranta? Suna cikin tattaunawa ma’aikatan suka shiga aje abinci da abun sha, cikin ma’aikatan ta kalli d’aya tace “Ina bak’ina? Suna nan ne?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button