NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Maida mata tayi da “Ki turo min lambar Abbanki zanyi magana dashi.”

Da “Ok.” Ta amsa mata tare da turo mata lambar, mik’ewar da Farha tayi ce tasa ta d’aga kai ta kalleta, da kallo ta bita ta tab’e baki har saida ta b’acewa ganinta sannan ta aje wayarta gefe tana kallon kowace kusurwa ta gidan. D’aki ta koma ta cire mayafinta ta zauna kan gadon, sake duba d’akin take da kyau, inhar gaskiya zata fad’a to fa d’akin nan kawai da aka sauketa ma babbar daula ce, tabbas a mahaifarta ne zata iya d’aga hanci da felek’e a game da ginin kece rainin da Salahadeen yayi, ta d’auka gidan nan mak’ura ce wanda daga shi sai kid’an tashi, amma daga k’ofar gidan nan data gani ta fara raina kanta, ta gane lallai a garin nasu ma dan bata shiga wasu wabajen ne data gane k’arya tunaninta ke fad’a mata, yanzu gashi ta kawo kanta gidan da ka rantse rabin unguwace aka gine, dan ko filin wajen da suka zauna yanzu cin abinci zai kai rabin nasu gidan, bare kuma sauran wajajen ba ma za’a had’a ba. Kuma a haka fa shine taji yace gidan Sarah, gidanta ne yanzu nan ita kad’ai?

Ajiyar zuciya ta sauke saboda tuna yar rayuwar da tayi tare dasu, wacce ta tashi a gidan nan amma tayi rayuwar wannan gidan? Ita ce har da kwana a k’auye wanda ko ita data fi kusa dasu ba kwanan dad’i tayi ba bare kuma ita? Ita ce har ta iya cin shinkafa ta ci tuwo? Wacce ke kewaye da hadimai ta ko ina ita ce acan take kai ruwan wanka da kanta? Ita ce ta tab’a sawa daka da hannu ta mata wulak’anci ta cizgata son ranta? Lallai tayi namijin k’ok’arin hak’uri, a gaskiya fa da ita ce ba zata iya ba ko kad’an. Gashi gaba d’aya ma Salahadeen d’in sai wani abu ta ga yana ma Sarah da bata gane mishi ba, kawai ita gida ma taji tana so ta koma ba zata iya ba.

Da yamma tana falo zaune tana kallon tashar labarai da wayar tana ta jiran ganin Abban Sajida en ligne dan suyi magana, Sandra ce ta shigo tare da wata mace bak’ar fata, gaisawa sukayi inda Sandra ta d’ora da “Kiyi hak’uri ma’am na jima ko? Wallahi da k’yar aka dace da irin ma’aikaciyar da kika ce kina so, dan saida aka tura ni hotel.”

Murmushi ta mata tace “Ba damu Sandra tunda dai an dace.”

Kallon matar tayi tace “Ya sunanki?”

Da ladabi ta amsa mata da “Linda Kippazo.”

Jinjina.kai tayi tace “Linda kin iya girkin abincin hausa?”

D’aga kai tayi alamar eh da fad’in “Eh madame, nayi aiki a a wurare da dama kuma ni yar africa ce, ina jin hausa ma sosai.”

Nan ma jinjina kai tayi tace “Ina da bak’uwa ne ta musamman kuma bata iya cin abincinmu, ina so ku shiga kicin tare da Sandra ki duba duk abubuwan dake akwai wanda zaki iya buk’ata, wanda kuka babu sai ki fad’a mata zata nemo miki.”

Duka jinjina mata kai sukayi suka nufi kitchen d’in, Salahadeen ne ya shigo ganinta zaune yasa shi yin sallama, har zai nufi d’akin tana mamakin yanda ko magana bai mata kamar wani gidanshi tace “Ji mana.”

Tsayawa yayi yana kallonta, a hankali tace “Akwai mai aiki da nasa aka kawo min, kayi magana da matarka zata iya umartarta kan duk abinda zata ci, sannan zata iya yin magana da ita dan tana jin hausa ita ma.”

Takowa yayi a hankali har ya tsaya kusanta, duk’awa yayi yana kallon k’afarta yace “Ya k’afarki? Tana ciwo ne?”

Girgiza masa kai kawai tayi tana shak’ar kamshin turarenshi da taji ya mata dad’i a hanci yau, mik’ewa yayi tsaye har zai wuce tace “Karb’i.”

Tsayawa yayi ya juyo yana kallonta, wani kwali ne a hannunta mai kyau wanda akayi pakejinshi mai fad’i da kuma d’an tudu, saida yasa hannu ya karb’a yace “Na miye?”

Saida ta d’auke idonta daga kanshi tace “Ka kaiwa bak’uwata, ta fitar da zakuyi ce dinner, gudumuwata ce gareta a matsayinta na bak’uwa ta.”

Tab’e baki yayi yace “Sai naji kince ta fitar da zamuyi? Ke fa? Ko baki ji me na fad’a miki bane? Duka iyalina nake buk’ata a wurin.”

D’ago kai tayi ta kalleshi a matuk’ar tsaurare tace “Ka daina tunanin ni iyalinka ce, me yasa kake son mayar da wasa gaskiya ne? Sla bamu dace da kai ba.”

Aje kwalin yayi gefenta ya sunkuyo yana dafe hannayen kujerar da take zaune, saida yayi kamar zai fad’a mata ya dafe hannayenshi yana kallon idonta, ita kam kawar da kai tayi dan kamar zai sumbaceta sun matse sosai, cikin wata murya yace “Maimaita na ji.”

Da k’yar ta d’an juyo da kanta ta kalleshi tace “Me zan maimaita?”

Cike da kallon shauk’i yace “Sunana.”

A hankali tace “To d’an matsa baya.:

Lumsshe ido yayi ya girgiza kai alamar a’a, marairaicewa tayi ta sunkuyar da kanta tace “Sla…hadeen.”

Wani kallo ya mata ya sake cewa “Maimaita na sake ji?”

A marairaice tace “Why? I am tired.”

Wani kallo ya mata wanda yasa ta saurin cewa “Slahadeen.”

A hankali ya sake cewa “Sake maim…” Bai kai k’arshe ba suka ji motsi a bayansu, cike da son basarwa kawai ya k’arasa had’e bakinshi da nata dan ko ma wanene ya d’auka abinda ya tarar kenan…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:19 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 4锔忊儯4锔忊儯

Cikin ma’aikatan ne wata ta shigo dan sanar da ita zuwan Kabeer dake son ganinta, muryarta cikin firgici tana fad’in “Sorry ma’am.”

A hankali ya raba bakinsu yana kallon fuskarta yanda ta lumshe ido tana karb’ar bak’on yanayin, fad’awa yayi kan kujerar yana wani shak’iyin murmushi yace wa mai aikin “Ke.”

Juyowa tayi har tana shirin bud’e k’ofar jiki na mata b’ari saboda ta tsorata ganin Hajiarsu da wani wanda dai labarin ya fara gauraye gidan wai mijinta ne, duk da bai da yanayi na talauci kama daga fatar jikinshi sumar kanshi zuwa suturar jikinshi duk sun nuna shima mai kud’i ne, amma dai tunda basu ga nashi izzar da ikon ba kam su dai har yanzu Hajiarsu ce a sama, kanta a k’asa ta matso tana jiran taji me zai ce mata, saida ya jawo Sarah jikinshi wacce ke kallonshi da mamaki yace “Ki kawo min abu mai sanyi na sha.”

Da kai ta mishi alamar to ta wuce wajen da kayan sha suke, har ta d’auko ta kawo masa Sarah bata daina kallonshi ba, karb’a yayi ya shiga kurb’a hankali kwance, jin idonta akanshi ne yasa ya kalleta, yatsu biyu yasa ya rufe mata baki data bud’e tana kallonshi, sake wangale bakin tayi zatayi magana kawai yayi saurin kifa mata kofin a baki wanda hakan yasa lemun ciki zubo mata a wuya har zuwa k’irji ya gangara cikin rigarta, bin lemun daya zuba yayi da kallo, juyawa yayi ya aje kofin yasa hannu ya jawo k’ugunta ta baya ya sake matsota kusanshi sosai. Soka kanshi yayi k’asan wuyanta kamar a mafarki taji yana lashe inda lemun ya zuba, da sauri ta zabura kamar zata tashi tsaye amma kuma rik’e yake da k’ugunta ya zagayo hannunshi ta cikinta, ta d’auka zai tsaya amma sai taji kam ya d’anyi k’asa da rigarta ya zura harshenshi tsakiyar mamanta, k’arfi tasa sosai ta ture shi daga kanta tana gyara rigarta ta juya mishi baya tana sauke numfashi kamar wacce tayi tseren gudu.

Kallon k’eyarta yayi ya mik’e yana tab’e baki ya taka matakalar da zai haye ya nufi d’akinsu yaji an bud’e k’ofar, wannan ma’aikaciyar ce tana bayan Kabeer daya shigo yana fad’in “Kinsan wanene no da zaki hana ni shigowa ganin ‘yata? Kiyi hankali kafin nasa a koreki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button