NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Wani murmushin takaici yayi ya kalli idonshi yace “Salahadeen kana birgeni sosai, babu abinda ke kayar maka da gaba, amma wannan aikin sai kayi da gaske.”

Wani iska ya furzar yace “Bana da lokacin b’atawa, ina so na koma gida na gobe ko jibi.”

D’agowa yayi daga kujerar ya tangale hannayensa yana kallon tsakiyar idonsa yace “Gobe nake so ka sato min ita.”

Wasu mukallai dake gabanshi ya turo mishi yace “Wannan makullin motar da zaka tafi da ita ne sanda zaka d’aukota, wannan kuma makullin gidan da zaka kaita ne gidana dake beach.”

Wani photo ya d’auko sai dai bai bashi ba ya ci gaba da cewa “Da misalin k’arfe 10:30 zata fito daga office zuwa caf茅t茅ria dake cikin r茅naux motor’s, babu tsayayyen abinda take zuwa yi, sai dai zata iya ci ko shan duk abinda taji ya birgeta, bata fita da waya ko jakarta ta hannu, minti goma take yi a wurin ta koma office, a wajen komawa bata lift take komawa ba, a k’afarta take tafiya saboda kiyaye lafiyarta, a duk wata kusurwa da zata shiga daga nan zuwa office d’inta akwai s茅curity cam茅ra a wuri d’aya ne kawai babu, wajen parking d’in motoci.”

D’ora hannayenshi yayi kan teble d’in yana kallonshi yace “A liftar ma akwai cctv cam茅ra?”

Ba tare daya d’auke idonshi daga kan shi ba yace “Babu.”

“Bien.” Ya fad’a yana komawa jinginar ya ci gaba da cewa “Daga lift d’in zan d’auketa zuwa wajen motar, photonta?”

Tura mishi photon yayi yasa hannu ya d’auka ya juya ya kafe da ido, da sauri ya saki photon ya kalleshi tsabar firgici, ba dan yana namiji ba daya saba da kwaramniya da sai yace jikinshi ma ya fara rawa rawa na son sanin dalilin da yasa uban ke son sace ‘yarsa. Da sauti ya turo masa photon yana fad’in “Sarah ce fa? Ko baka gani ba?”

Kallonshi yayi da kyau yace “Na sani, ita nake so ka d’auko min.”

Mamaki ne ya hana shi magana sai kallonshi da yake, ganin kallon yayi yawa yasa shi cewa “Salahadeen, karka bawa kanka wahala wajen tunanin lamarin nan, just do it.”

Ajiyar zuciya ya sauke yana ci gaba da kallonshi shi dai, d’an murmushi ya masa yace “Karka damu, ba cutar da ita zanyi ba, ina da dalilina na yin haka.”

Wata ajiyar zuciyar ya sake saukewa cikin sanyin jiki yace “Ok.”

Tablet d’in dake gabanshi ya shiga daddanawa, kallonshi yayi yace “Zaka samu alerte d’inka yanzu.”

Mik’ewa yayi tare da d’aukar makullan ya fita da tunanin me ke faruwa ko yake shirin faruwa?

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 03:58 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa ta Orange money(ba chap chap ba yan uwa, orange money dan karka tura ta chap chap amma zaku iya tura kati) akan wannan lambar 91-71-28-22 ko kuma wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               6锔忊儯

Cikin gajiya da zaman ta kalli k’eyarshi tace “Mr. har yanzu bamu isa sauka inda zamu je bane?”

Saida ya juyo ya kalleta jin tace wai mr., juyawa yayi ya kalli abokinshi yace “A ina motarka zata tsaya?”

Ba tare daya kalleshi ba yace “Sai marad’awa insha Allahu.”

Kallonta yayi yace “Kinji ko?”

Mayar da hankalinshi yayi kan titi hakan yasa ita kuma ta shiga jijjiga kujerar da yake zaune tana fad’in “Ka tsayar da motar nan na sauka mr., kai mak’aryaci ne satoni ne kayi, ka tsaya zan sauka anan dan Allah karka kashe ni, kasan Abhi yana da kud’i ko nawa ne zai baka idan ka fad’a masa, idan kuma siyar dani zakayi ka fad’i nawa kake buk’ata, amma ka mayar dani gida na gaji da zaman nan bana son wurin nan ko kad’an.”

Kallonshi Kasim yayi a harshen hausa yace “Kaji wai siyar da ita za kayi? To wa zai siyi wannan kod’add’ar anan?”

Da sauri Salahadeen ya kalleshi ita ma ya juya ya kalleta da tunanin taji abinda ya fad’a tunda tana kama hausa, amma sai yaga bata damu ba sai ma kallonshi da take tana fad’in “Mr., ka mayar dani wajen Abhi.”

Banza sukayi da ita suna ta hirarsu, haushi ne yasa ta bud’a gaba d’aya muryarta ta rintse ido ta dalla wata razananniyar ihu, da k’arfi Kasim ya taka birki shi kuma ya rufe kunnuwa tare da juyowa dan ganin me ta gani, ba komai kawai iya hege ne na nata, cikin tsawa yace “Ke ya isa haka.”

Gum tayi da bakinta saboda tsawar daya mata, cike da masifa yace “Na sato ki nayi me dake? An fad’a miki ina siyar da mutane ne? To idan kika sake min irin ihun nan saina murd’e miki wuya.”

Ya gama fad’an zai juya kawai ta fashe da kuka tana fad’in “Ni ka mayar dani wajen Abhi to, kuma Abhi bai tab’a yi min tsawa ba, kai kuma mugu ne dodo.”

Tsaki ya mata tare da juyawa ya zago sigari ya kunna, yana jin yana jin sautin kukanta har k’asan zuciyarsa saboda yanda take yinshi da gaskiyarta, tun suna jin kukan a k’ok’on kansu, har suka fara jin shi a hankali kamar tana musu susar kunne, har k’arshe suka ji shashek’a kawai take saukewa, ko da ya juyo ya ga bacci ne ya d’auketa daga zaune wajen kukan.

Fuskarta ya tsurawa ido yana kallo, babu kwalliya a fuskar duk ta goge wajen kuka da wahalar hanya, mayar da kallonshi yayi kan Kasim yana fad’in “Mata sha’aninsu sai su.”

Kallonshi Kasim yayi yace “To wai me yasa ka taho da ita ne?”

Ba tare daya kalleshi ba yace “Kai labari ne mai tsawo, zan fad’a maka idan muka zauna.”

Jinjina kai yayi yace “Ina fatan dai ba auren zobe kayi ba? Alhalin kasan kana da Farhana anan, tana nan tana jiranka.”

Kallonshi yayi yace “Aure da wannan? Talauci.”

Kallonshi yayi jin yace talauci yace “Ban gane talauci ba?”

Girgiza kai yayi dan mutum ne shi da bai cika magana ba, kallonshi ya sake yi yace “Amma dai ka dawo kenan ko? Ko zaka koma ne?”

Kallonshi yayi ya girgiza masa kai alamar a’a, saida har ya cire rai da zaiyi magana ya ji yace “Na zo cin amarci ne.”

Dariya Kasim yayi yace “Gaskiya ya kamata, tunda yanzu Farhana ta girma ta mallaki hankalin kanta, shekara sha hud’u ta k’ara uku kaga sun zama sha bakwai fa kenan.”

Wani matashin murmushi ya saki yace “Da Abba yaji tawa da sai yanzu ne za ayi aurenmu, amma son da yake mata da tausayinta na kasancewarta marainiya yasa shi gaggawar aurar damu kafin na bar k’asar nan, da fari ina ganin kamar an takura ni ne, amma kaga yanzu sakayau nake ji na.”

Murmushi Kasim yayi yace “Dole ne mana tunda ka zo more rayuwa da ita.”

Kallonshi yayi yace “Ba abinda nake nufi kenan ba.”

Haka suka ci da fafarar hanya ba ji ba gani sai tsayawa abinda ba’a rasa ba, har dare ya tsala musu sosai a hanya, data farka ma wani kuka ta sake saka musu tana kwaroroton ya kaita wajen Abhi, saida suka shiga garin kai tsaye ya kaisu k’ofar gidansu Salahadeen ya aje shi kuma ya wuce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button