NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Yana ficewa taji wani bak’in haushi ya taso mata, tsaki ta sake yi tana cillawa kayan harara, tunanin yanda zatayi dasu ta shiga yi amma sai taji an k’wank’wasa k’ofar d’akin.Sandra ce da Linda suka shigo, saida suka k’arasa kusanta da murmushi Sandra tace mata “Barka da hutawa.”

Fahimta da tayi gaisheta ne tayi yasa ta amsawa da kai da kuma ido alamar yawwa d’in nan, Linda ce ita ma cikin hausa tace “Barka da hutawa madame.”

Kallonta Farha tayi tare da jin wani dad’i na ta samu wacce zata iya yin magana da ita dan ta gaji da kume bakinta, amma saita basar ta amsa mata da kai ita ma, wani d’an tab’e baki Sandra tayi tana fad’a a ranta cewa “Wannan ba dai jiji da kai ba, kuma yanzu haka ba kowa bace, amma har tana neman tafi yar masu gida, har yanzu banji muryarta ba ko kuwa ma dai kurma ce?”

Sake tab’e bakin tayi ta kalli Linda da taji ta mata wata hausar tace “Wannan ita ce wacce zaki ma aiki daga yanzu har lokacin da zata tafi, zaki iya tambayarta idan akwai abinda take buk’ata bayan wannan?”

Jinjina kai tayi ta kalli Farha cikin kakkauran muryarta tace “Madame ni sunana Linda, an d’aukoni ne na dinga girka miki abinci kawai, idan kina buk’atar wani abu ki fad’a min saina fad’a mata?”

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi ta kalli Sandra ta kuma kalli Linda, a hankali cikin fitar da kowace kalma tace “Ban buk’atar komai.”

Kallon Sandra tayi ta fad’a mata abinda tace, hakan yasa ta juyawa ta fita daga d’akin, kallonta Linda tayi tace “Madame akan aikina nake, me kike buk’ata na fad’a miki?”

Gyara zama tayi ta hanyar d’ora k’afa d’aya kan d’aya tana kallonta tace “Kin iya dafa macaronie da farar miya?”

D’aga kai tayi alamar eh, cike da gamsuwa tace “To ki dafa min, amma bana so kiyi anfanin da sashin kowace dabba anan, dan basa Bismillah wajen yankan.”

Cikin kwatanta mata da hannu tace “Madame idan kina buk’atar naman musulmi ai akwai alimentation d’in data musulmi ce, kuma suna yanka namansu da bismillah sai a siyo miki.”

Girgiza kai tayi tace “Duk yaudara ce malama, abinda inji ne ke yankawa taya zasu tsaya wata bismillah, kawai kiyi yanda nace miki.”

Jinjina kai tayi tace “To madame ko na karb’i kud’i a hannun mrs Joseph saina siyo miki ki yanka da kanki?”

Wani kallo Farha ta mata tace “Wai an fad’a miki bana cin nama a gidana ne da zaki takura min sai na ci naman anan? Kije kiyi abinda na saki kawai malama.”

Da sauri ta juya tana fad’in “To to madame, yi hak’uri.”

Da harara ta bita tana juya baki, mik’ewa tayi ta shiga ban d’aki ta d’auro alwala dan taga lokacin yayi a wayarta kasancewar ba’a jin kiran sallah anan.

Har saida ta ida sallah da azkhar d’inta tana tunanin idan lokaci yayi ta mayar da isha’i Linda ta dawo, da sallama ta shigo d’akin ta tsaya bayanta tana fad’in “Madame an gama abinkinki yana dinning.”

Mik’ewa tayi tana kallonta har ta nad’e sallayarta ta mayar ta aje, juyawa tayi ta kalli madubi ta gyara fuskarta ta cire hijab d’in, bata d’auki mayafi ba kawai ta kalleta tace “Mu tafi.”

Gaba ta shige Linda na binta a baya tana fad’in “Sak’o daga madame Sarah tace a fad’a miki idan kin gama abincinki ki sameta a saloon room.”

Ko juyowa ba tayi ba ta wuce kawai, amma me zai faru saita manta hanyar da suka bi da Salahadeen da safe, sam rasa inda zata nufa tayi saboda girma da kusurwar gidan, tsayawa tayi ta juyo ta kalli Linda tace “Ki wuce mana kin tsaya kina bina a baya.”

Da sauri Linda ta shiga gaba tana ji a ranta ba fa lallai su kwashe lafiya da matar nan ba, ita kam inda ma Hajia babbar ce to da tana iya hak’uri ta shanye, amma k’awarta kam bata da zuciyar d’aukar irin wannan wulak’ancin. Saida suka isa ta ja kujera ta zauna Linda ta had’a mata komai, babu nama a ciki amma k’amshi sosai yake tashi a wurin, waken gwangwanin (Mac茅doine) da aka saka ya k’awata yar farar miyar tayi kyau da gani, ga wani dan ganyen pasili (persil) da aka watsa a ciki, ta bud’a fridge zata d’auko mata abi da zai dace da cin makar ta nuna mata kwalin wata madara tace “D’auko wannan.”

Kallonta tayi ta kalli hannunta inda ta nuna, d’auko madarar tayi ta kawo ta tsiyaya mata a kofi ta aje, cikin ladabi tace “Zan iya tafiya madame? Ko na jira ki kammala saina rakaki saloon room d’in?”

Ba tare data kalleta ba tace “Ki jira ni mu tafi, bansan wajen ba.”

Jinjina kai tayi alamar to ta k’ara matsawa gefe, tana kai lomar farko bakinta ta tsaya da taunawa ta kalleta, ita ma kuma ita take kallo da fatan kar tayi k’orafi, dan wasu mahaukatan kud’i ne aka ce za’a biyanta daga yanzu zuwa sanda matar zata tafi, kud’in da a shekara uku da tayi tana aiki a hotel d’in nan bata same su ba. Da k’yar ta taune abincin ta had’e baki na rawa na masifa tace “Menene haka? Ya zaki bani abinci kamar mai hawan jini haka babu d’and’ano ko na sisin kwabo?”

Da sauri ta matso tana fad’in “Yi hak’uri madame ki gafarce ni, wallahi na saba ne kasancewar anan su basu damu da d’and’anon ba, amma ga gishiri nan zaki iya k’arawa.”

Ta fad’a tana mik’a mata robar, harara ta dalla mata tace “Zuba min to.”

Da sauri ta zazzaga mata ta kalleta tace “Jaraba kiji yanzu.”

Sake kai loma tayi tana taunawa da k’yar, fizgar robar gishirin tayi dama farko dan bata san yanda zatayi anfani dashi bane yasa tace ta zuba mata, k’ara zazzagawa tayi kafin ta sake ci, gira ta d’aga sama tare da yatsina baki irin ba laifi d’in nan, dan abincin yayi dad’i rashin arom ne matsalar.

Saida ta gama ta d’auki madara ta sha taji salap babu zak’i sai wani shegen k’amshi da gard’i tana wucewa ta mak’oshi lafiya lafiya, d’auke kai tayi ta kalleta tace “Haka madarar take salap shine kika bani?”

Da ladabi tace “Sorry madame, sai fa kin saba da jin irin wannan go没t d’in a bakinki, dan su nan suna kiyaye lafiyarsu sosai ta hanyar nisantar wannan d’and’anon da tumatirin gwangwani da zak’i, ba kowane lokaci ne zaki samu abincin da d’and’anon da kike so ba.”

Tsaki tayi ta kalli wasu robobin dake wurin irin na goshirin, nuna mata tayi tace “Akwai sugar a cikin nan?”

Da sauri ta d’auko ta mik’a mata, tana kallo ta zazzaga a cikin kofin madarar ta d’auki colaki ta motsa sannan tasha, kallon Linda tayi tace “Zak’in ma ai dad’i gare shi.”

Wani kallon mahaukaciya ta mata a ranta tace “Idan kuma ya kamaki zaki gane baki da wayo ba.”

Saida ta gama suka mik’e Linda na gaba tana binta a baya, tab lallai gidan nan sai a kashe mutum babu mai ji bare gani, gaba d’aya wata kusurwarce ta daban wacce bata tab’a sani ba, lallai saita ware lokaci tace a nuna mata gidan nan ciki da waje, wani d’aki ne Linda ta bud’a suka shiga suna kallon d’akin.

Yanda kasan dai saloon ce ka je haka wurin yake, drower har biyu ke akwai mangaza mangaza masu d’auke da mayuka na kai kowane iri dana relaxer na dandruf, haka mayuka na gyaran k’afa da ruwan wanke k’afar kala kala dana tafukan hannu, kayan aiki kuma babu kalar da babu kama daga na gyaran kan zuwa k’afa da hannu jiki da ma ido, abu d’aya da babu sosai shine kujerar zama, kujera uku ne da madubi uku alama wurin gyaran mutum uku ne za’a iya yi ma lokaci d’aya. Sai wata sofa mai kyau a gefe daga farkon shigowa, amma hatta da frdge akwai yar matsakaiciya cike da kayan sha da ci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button