SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Sarah suka samu zaune da ma’aikata guda biyu, d’aya na mata stimmin gashi d’aya kuma na wanke mata k’afafu, jin shigowarsu yasa Sarah juyowa tana d’auke kokombre dake saman idonta tana murmushi tace “Yawwa shigo, ki zauna dan Allah zasu gyara miki kai ne.”
Tana fad’a ta juya tana mayar da kokombre a idonta, jiki a sanyaye ta k’arasa inda wata mai aikin dake zaune ta mik’e tana nuna mata, zaunawa tayi ta cire mata d’an kwalinta, hangen gashin Sarah take tana mamakin yanzu can miye ake mata? Duk da ba laifi tsayin gashinta ya sauka har ga wuya, amma kitso ne akan dole aka shiga since shi ana cikin yi kuma wacce data gama gyara ma Sarah k’afafu ta canza komai na aikin ta fara gogewa Farha na ta har da abun lallen dake k’afafun saida aka goge shi tas.
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:20 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LABARI*
SAMIRA HAROUNA
*SADAUKARWA GA*
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
4锔忊儯5锔忊儯
Wayar Sarah ce tayi k’ara hakan yasa mai gyaran kan dake ta tsantsara mata wani fitinannen coiffure ta d’auka ta d’ora mata a hannu, saida ta bud’a ido taga lambace babu suna, kamar ba zata d’auka ba sai kuma ta d’auka ta d’ora a kunne, daga b’angarenshi yace “Fatan dai ba zaku b’ata lokaci ba wajen shiryawa? Nan da minti biyar zan shigo gidan.”
Cikin sauta murya sosai tace “Um um, sai ka zo.”
Bai amsa da komai ba kawai ya kashe wayar, aje wa tayi tana girgiza kai kawai, shiri yayi nisa sosai ana ta gyarasu da tsefesu gwanin birgewa, cikin masu aikin ne wata ta kalli Farha tace “Madame ina kayanki da zaki saka?”
Kallonta tayi sai Linda ce tace “Kayan da zaki saka take tambaya?”
“Suna d’aki.” Tace, Sarah ce daga can zaune tace “Linda ki d’auko mata su nan saita canza.”
Da ladabi ta amsa ta fita, mai aikin kuma ta kalli Farha tace “Kina buk’atar kiyi wanka ne?”
Shiru ta mata dan haka Sarah daga can a hausa tace “Ga ban d’aki nan ki shiga kiyi wanka saiki fito.”
Waigawa ta shiga yi da son ganin ban d’akin, bata ga komai ba sai mai aikin ce data fahimta ta matsa kusan drowern mayukan nan ta turata sai ga k’ofa ta bayyana, bud’e mata tayi hakan yasa ta tashi, hular wanka ta d’auka ta saka mata dan kar gyara ya lalace, da sauri tayi tsaye tana k’amewa wuri d’aya, kallon k’afafunta tayi saboda wani irin laushi da taushi da taji sunyi tare da wani tudu kamar an k’ara cika mata tsoka a k’afar, sai taga sun mata wani kyau kamar ta had’iye k’afafunta ita kanta, lura da duk abinda ke faruwa yasa Sarah sakin murmushi a ranta tana fad’in “Zuwa yanzu nasan kin fara fahimtar yanda kike tarban bak’inki da yanda ni nake tarban nawa.”
Mai aikin ce tayi sauri ta jawo mata takalmin dake k’ofar ban d’akin ta aje mata gabanta, sakawa tayi sannan ta shige tana ji kamar karta taka k’afafun.
Wata siririyar meke up aka watsa mata akan matsakaiciyar fuskarta wacce ta dace da ita, pantin akaihu aka mata amma da kalar farin ruwan vernie d’in wanda ba zaka ce an saka ba sai kaga suna k’yalli, gashin an gyara sai k’amshi da kyalli yake, amma sai aka mishi wani irin dunk’uli a baya kamar gammo aka tattare shi baya ya mata acuci, kayanta suka mik’o mata ta tashi ta saka a lokacin Farha ta fito. Suna had’a ido tayi saurin d’auke nata idon, har k’asan zuciyarta ta yarda tayi kyau sosai, shirin da tayi shiri ne na manyan yara shiri da wani lokacin take ganin jaruman bollywood Hollywood da sauransu suna yi idan ana wani taro na karramawa ko bada kyauta, a take taji har zuciyarta ta yarda babbar yarinya ce mai fantamawa kuma tafi k’arfinta, sai yanzu ta yarda da abinda ya fad’a mata cewa ba dan yanayin rayuwa ba da ganin Sarah ma zai mata wuya, bak’ar riga ce da gani kasan musamman aka zanata saboda ita saboda yanda ta bi komai nata ta fito dashi, abun birgewa ga rigar shine har tana d’an jan k’asa sannan dogayen hannu ne gareta har sun wuce gwiwar hannu, ga sark’a da yan kunnai masu tsadar gaske, amma sai Sarah ta kawo wani k’aramin hijan wanda yafi kama da hula ta saka saboda rufe abinda addini yace a rufe, daga gashinta zuwa wuyanta ne ya rufe ya kuma fito da shap d’in kan nata da wuya, zargama zargaman takalmi bak’ak’e ta saka sai jakarta ta hannu data rik’e.
Kallon kanta tayi a madubi, ita kanta tasan tayi kyau kuma tsarin da tayi duk da za aga kamar k’auyenci tayi amma a wurinta yanzu shine wayewar. Farha ma zaune tayi aka ci gaba da gyara ta tsaf har aka bata kayanta ta saka ita ma, abun mamaki tana saka rigar sai taga ashe sak irinta sarah ce kala ne kawai ba d’aya ba, kuma sai gashi kalar ta fito da hasken fatarta kamar yanda bak’i ya fito da Sarah, takalmin ta saka ita ma amma jin tayi wani zak’ek’e alamar ta k’ara tsawo saita fara tambayar kanta zata iya kuwa? Kamar yanda ta saka hijab d’inta haka ita ma ta saka nata kalar rigarta, sunyi kyau sosai inda ba dan banbancin fata da fuska ba saika rantse yan biyu ne, kallon Linda Sarah tayi ta mik’a mata katin cirar kud’i tace “Ki sallamesu.”
Karb’a tayi da girmamawa suka fita tare suna mata sai anjima da girmamawa, kallon Farha tayi dake ta hangen kanta a madubin ta kasa juyawa saboda gudun fad’uwa, ba wai bata saka takalmi mai tsini bane, wannan ne dai yayi tsawo sosai ba zata iya ba, hannu Sarah ta mik’a mata tana fad’in “Zo zauna, ba zan iya tashi ba saboda k’afata, yanzu zai zo ai sai mu tafi.”
Kallonta tayi ta kalli hannun nata, har zata share hannun amma tana takawa sai taji ta b’angwale zata fad’i, da saurin tsiya ta damk’o hannun Sarah ta rik’e gam, saida ta tako ta zauna kan sofar sannan ta fara sassauta rik’on data ma hannunta, saida ta kalli hannun da sai yanzu ne taji wani bala’in taushi ga hannu kamar na jariri sabuwar haihuwa.
Tana sakin hannun Sarah ta d’auki wayarta, daidaita tayi irin zata d’aukesu selfie tace “Kallo nan.”
Kallon wayar tayi kam tare da d’an sakin fuskarta daga had’ewar data mata, murmushi Sarah tayi ta d’aukesu, masha Allah sunyi kyau a hoton kam, a take tayi posting hoton a WhatsApp d’inta da cewa me and my rival.
K’wank’wasa k’ofa akayi Sarah ta bayar da izinin shigowa, mai aikin ce tace “Ma’am, yallab’ai yana jiranku a waje.”
Saida ta kalli Farha tace “Ki fad’a masa mun shirya, amma ni wa zai fita dani?”
Sunkuyawa tayi tace “Ok ma’am.” Fita tayi inda ta kalli Farha tace “Mijinki yana jiranki a waje.”
Kallonta tayi sai kuma ta mik’e tsaye tana d’an rik’e rigarta a hannayenta, da kallo ta bita tana rik’e dariyarta saboda yanda take takawa zaka san a tsorace take, tana fita a bakin k’ofar ta samu labceciyar motar na jiransu, fitowa yayi daga bayan motar yana gyara zaman rigarshi cot, k’ara gwale idonta tayi ta bud’a bakinta. A gaskiya ya birgeta sosai saboda ya had’u, bak’ak’en suit ne sai farar riga k’ar da ita babu nikctied, bak’ak’en takalmi sai d’aukar ido suke, saida ya tsaya gabanta ya d’an k’yasta mata hannu tayi saurin kallonshi, d’aga mata gira yayi yace “Ya dai?”
Ajiyar zuciya ta sauke ta girgiza kai tace “A gaskiya kyau, ashe dama haka kayan nan ke maka kyau? A gaskiya yau ka fito a bature sak.”