NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Sama da k’asa ya kalleta, shafa gefen fuskarta yayi yace “Wa ya baki shawarar rufe min kayana? A gaskiya ko ma wanene yana da matuk’ar sani akaina, ya gane ni d’in mai kishin iyalinsa ne.”

Tab’e baki tayi ta juyar da kanta, murmushin k’eta ya mata dan yasan bata ji dad’i ba, ajiyar zuciya ya sauke yace “Kinyi kyau sosai, ina zuwa.”

Wayarshi ya ciro ya sake matsawa kusanta ya kalleta yace “Yi murmushi.”

Saida ta d’an kwanta a k’irjinshi tana dafe dashi ta saki murmushi, d’aukarsu selfie yayi tare da nuna mata yace “Kin gani ko? Zan nunawa Mama ta gani.”

Murmushi tayi tace “Ka fini kyau fa.”

Murmushi kawai yayi yace “Shiga ciki ina zuwa.”

Da kallo ta bishi har ya shige d’akin data fito, shiga motar tayi ta zauna tana kallon k’ofar da jiran fitowarsu. Yana shiga suka k’ure juna da ido kowa da abinda yake sak’awa a ranshi, maganar gaskiya ya mata kyau sosai, tsintar kanta tayi da yin murmushi har ya k’araso inda take, durk’usawa yayi kusan k’afarta data mik’e mai ciwo, a hankali ya kamo k’afar yana kallon fuskarta, a gaskiya ta birge shi daya ga kayan jikinsu basu nuna tsiraici ko wani sashe na jikinsu ba, gashi tayi wani kyau har wani haske take tana d’aukar ido.

Cire takalman yayi a k’afar ta yana kallo can k’asan mak’oshi yace “Menene wannan?”

Ba tare data d’auke ido daga kanshi ba tace “Takalmi mana.”

Kallon idonta yayi yace “Kina fama da k’afar kuma kika saka shi?”

D’aga kafad’a tayi alamar ya zanyi to? Kama tafin k’afar yayi inda babu bandejin yana k’ok’arin saka mata takalmin, wani taushi daya ji a k’afar yasa shi shafata yana kallon k’afar, saka mata yayi ya mik’e tsaye ya tara mata hannu alamar ta taso, saida ta kalli fuskarshi ta kalli hannun a hankali ta d’ora hannunta akan nashi, mik’ewa tayi tsaye hakan ya bashi damar k’are mata kallo na tsanake, d’auke kanshi yayi yana tab’e baki yace “U look beautiful.”

Ita ma d’auke kanta tayi tana had’e fuska tace “Thank u.”

Sake rik’e hannunta yayi sosai ya fara takawa ita kuma tana binshi a hankali cikin dubara, saida suka kai k’ofa zasu fita ya saki wani murmushi tare da sumbatar hannunta yana sale jadadda mata “Kinyi kyau fa sosai, kamar wata zara a cikin taurari.”

Dariya abun ya bata ne yasa ta tintsirewa da dariya tana fad’in “Allah?” Jinjina mata kai yayi shima yana dariyar, b’angaren da Farha ke zaune tana ganin yanda suke nishad’i suka tsaya, kallonta yayi yace “Matsa min.”

Saida ta wurga masa harara sama da k’asa kafin ta matsa tana d’auke kanta daga kallonsu, shiga yayi ya zauna sannan ya kamo hannun Sarah ta shigo suka saka shi tsakiya, rufe motar tayi kafin driver yaja su.

A tare ya kamo hannayensu ya rik’e da hannayenshi duka biyu, murza hannayen ya shiga yi hankali kwance, kallon dukansu yayi yace ” Farhanatu, Saratu.”

Duka kallonshi sukayi amma babu wanda ta amsa mishi, cikin sanyayyen murya yace “Ko zaku iya yi min wata alfarma dan Allah?”

Babu wacce ta d’auke idonta daga kanshi, sai dai jin Farha ba tace komai ba sai ita tayi wani murmushi tana d’ora d’aya hannunta kan hannunshi dake rik’e da nata tace “Ohh baby, ai mu naka ne mallakinka, zamu iya yi maka komai indai za kayi farin ciki, ka fad’a mana a shirye muke insha Allah.”

Kallonta yayi yana mai jin dad’in abinda ta fad’a ko da ba daga zuciyarta ya fito ba, kallon Farha yayi sannan ya kalli hannayensu daya rik’e tamau yace “Ina so ku min alk’awarin zama lafiya da junanku, ku had’a kanku hakan shine samun nutsuwata da farin ciki na da ma yalwatar arzik’ina, amma rashin had’a kanku shi zai gurb’ata tunanina da nutsuwata.”

Wani kallo Farha ta mishi saboda mamaki har bakinta ya sub’uce tace “Wai kana nufin ba zaka saketa ba kenan? Wai me yasa ba zaka fito fili ka fad’a min abinda kake nufi da ita ba?”

Jim yayi amma bai ce komai ba haka kuma bai kalli kowa ba, Sarah kam tuni ta juyar da kanta tana dariya dan ita abun nashi ma dariya yake bata, jin ba tace komai ba yasa shi kallonta yace “Ke me kika ce?”

Da sauri ta kalleshi kamar wacce ta dawo daga wani tunani, ajiyar zuciya ta sauke ta shiga sakin wani murmushi tana d’aga mishi gira sama, shima girar ya d’aga mata hakan yasa ta zame hannunta daga nashi, kallon Farha tayi cike da son cikata tace “Amm Farha ko? Sorry! Anan mu ba haka muke saki ba, kafin ya sake ni dole saina yarda sannan mu gurfana gaban alk’ali tare da lauyoyinmu, idan dukanmu mun amince ne zamu saka hannu sannan alk’ali ya raba auren, a yanzu kuma da nake d’auke da cikinshi shima wani babban case.”

Saida ta gatsine mata fuska tace “Dan haka ina ga zai fi kyau mu bar maganar sakin nan, dan zan iya haife wannan cikin na kuma d’aukar wani bamu gama shari’ar nan ba.”

Cikin masifa ta d’ago daga kujerar kamar zata zunbule k’asa tace “Me kike nufi kenan? Kina so kice ba zaki rabu dashi ba ko me? Amma ai kinsan taimaka miki ne yayi ko? Dan haka ko kina so ko baki so dole kisa hannu wallahi ku rabu.”

Ajiyar zuciya ta sauke tana gyara zamanta tare da d’ora hannunta kan kafad’arshi, d’aya hannun kuma mab’allan wuyan rigarshi ta shiga wasa dasu tana fad’in “Kiyi hak’uri Fara..am Farha, maza anan suna wuya da tsada sosai, samun kamar mijinki ba abu bane mai sauk’i da har zanyi nasarar samunshi kuma na wofantar dashi haka kawai, kuma ai yana da damar auro biyu ma bayan mu.”

D’auke hannayenta tayi ta mayar da kanta ga hanya tana kallon ababen hawa, tana ji tana masifa wani zancen ta gane wani kuma a banza ta fad’a, shi ma kuma yana ji amma saiya mayar da ita kamar mai busa masa sarewa, dan tuni Sarah ta tafi da gaba d’aya kuzarinshi da kalamanta da kuma kusancin da suka samu, babu wanda ya sake kulata har ta gaji ta dinga jan tsaki da k’wafa har suka tsaya bakin had’add’er hotel d’in mai sunan miracle hotel, mai gadin wurin ne ya matso da girmamawa ya bud’e k’ofar da Sarah ke zaune, fito tayi cikin k’asaita da kama jiki, ta d’aya b’angaren Farha ta fita Salahadeen ma ya fita ta can, jiransu tayi suka zagayo inda suka shiga takawa a tare suka nufi ciki bayan mai gadin ya bud’e musu k’ofar yana musu maraba da zuwa, driver kuma wajen parking motoci ya nufa.

Wurin zaman mutum uku ne aka gyara musu shi suka zauna, duk da taso bawa idonta hakk’insu wajen zagewa ta kalli abun kallo, amma da yake ranta a b’ace yake duk haushi take ji saita share kawai ta danne kanta tana ta hararen Sarah, ma’aikacin wurin ne ya kawo musu ruwa tare da aje musu littafin dake d’auke da kalolin abinci, Sarah na d’auka ta mik’awa Farha ta fizga da k’arfi ta aje, tab’e baki tayi a ranta tana fad’in “Matsalarki ce idan kika kunyata mijinki.” Sai Salahadeen daya shiga duba na hannunshi, saida ya gama ya mik’a mishi ya kalli Farha yace “Me kika zab’a?”

Cikin jin haushi tace “Ban son komai, gida nake son komawa kawai.”

Banza yayi da ita ya kalli Sarah dake danna wayarta yace “Ke fa?”

A harshen turanci tace “Abinda zaka ci, amma ka tabbatar babu dangin k’wai ko nama a ciki, ba zan iya ci ba.”

Kallon mai aikin yayi ya fad’a mishi abun buk’atarsu ya juya yana mai rubutawa, gaba d’aya ta mayar da hankalinta kan wayarta tana magana da Sajida wacce dukansu suke ji a jikinsu zasu iya zama yan uwa, yanzu haka magana suke akan hoton data d’ora akan statu d’inta na ita da Farha take tambayar da gaske tana da aure har da kishiya? Tabbatar mata tayi tare da tsaigunta mata yanda akayi auren nata ya kasance, yanzu haka ma ta fad’a mata abinda ya faru a mota shine ta maido mata da dogon msg kamar haka “Idan zan iya baki shawara yer uwa ki kama kanki, ba wai kishiyarki ba har shi d’in ya kamata ya koyi hankali, ki daina sakar mishi fuska har yana ganin hak’oranki, dan a yanda na fahimci labarinku akwai wulak’anci a cikin al’amarinshi, akan me zai dinga fifitata a kanki? Dan kawai aurenku ya zo a haka? Kawai ki d’aure masa fuska ki nuna masa ke rabuwar kile so kamar yanda ita ma take so, sai dai kuma in kina son shi to zaki iya hak’uri ki shanye komai.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button