NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Hanyar fita da yayi tasa ta mik’e zata shiga ban d’aki dan yin alwala tayi sallah isha’i data kubce musu, amma sai gani tayi ya kashe wutar d’akin ya dawo da baya kuma, girgiza kai kawai tayi ta shiga ban d’akin, da kallo ya bita yana ganin shigarta ya kwab’e rigarshi ya haye kan gadon, wani kakkauran blanket yaja ya rufa, a take ya lumshe ido saboda wata ni’ima da yaji, laushin katifa dana zanin dake samanta dana rufar, tattausan piluluwa dake wurin ga wani d’umi na musamman da shinfid’ar ke fitarwa, sanyin ac d’akin yana busawa a hankali yana shiga ta cikin zanin yana bayar da wata ma’ana mai dad’in gaske, sai yaji yana hamdalah ga ubangiji daya sa suna cikin masu jin dad’in rayuwa tare da fatan samun gida managarci a k’arshen ma. Ya kuma sake tausayawa yar amanar Mama da har ta iya bacci a tsohon gidansu, kai ba ma tsohon gidan ba har sabon gidan nashi da yake ganin aljannar duniya ne sai yaji idan aka kwatantashi da shinfid’ar Sarah ma kad’ai sai suji kunya. Sannan k’amshi, k’amshin jikinta ne a duka shinfid’ar, pillow kuma k’amshin man kanta kawai yake fitarwa, hakan ya haddasa mishi lumshe ido lokaci d’aya yaji wani basaraken bacci na son d’aukarsa ma, to amma da yake akwai nufin da ya shigo dashi d’akin saiya murje ido yana jiran fitowarta kawai.

Ta d’an jima kafin ta fito da k’aramin towel a hannu tana tsare ruwan jikinta, tun fitowarta ta hangi tudu saman gadon ta kuma tabbatar shine, amma saita share tayi kamar bata gani ba, wajen kayanta ta bud’a ta d’auki wando mai tsayi sosai wanda ya saketa ta saka, doguwar riga ta d’ora a sama sannan ta saka beby hijab d’inta a ranta tana tunanin fita da safe taje siyo wasu abubuwan buk’atarta. Yana kallo ta kabbara sallah bayan ta kalli gabas, da ido ya dinga bin duk wani motsinta har ta d’auki kusan minti ashirin kafin ta idar, bata tashi daga nan ba saida tayi azkhar d’inta gaba d’aya sannan ta zura hannu kan gadon ta d’auki wayarta, app d’in Qoran compl猫te dake ciki ta shiga, a daidai inda ta tsaya ta tashi kamar yanda bayan ko wace sallah ta farilla take karanta hizib biyu, wanda hakan ke bata damar sabke Alqur’ani a kowane wata sau d’aya, bata d’aga murya sosai ba kuma bata yi k’asa da ita ba, a inda yake dai kuma a yanayin da yake bacci ne kawai ya nemi d’aukeshi saboda yanda k’ira’arta ke shiga kunnuwanshi tamkar susan kunne qke mishi tare da shafa kanshi dan yayi bacci, sam k’ira’ar bata da banbacin data haihuwar larabawa da suka tashi cikin karatun dare da rana, sai gashi shi dake jiran ta gama ta zo ya b’arje gumi sai kawai bacci ya tafi da shi bai san lokacin ba.

Tana idarwa ta fita a app d’in saita shiga jadawalin jerin kira, lambar mahaifin Sajida data turo mata ta sake jarraba kira, dan tasan yanzu ba ba dare bane a wurinsu, saida wayar tayi kamar ba za tayi k’ara ba sai kuma taji ta d’auki kururuwa, da sauri ta gyara zamanta gabanta na dokawa da sauri sauri ta kasa kunne sosai tana sauraren a d’auka.

Ana d’auka daga can b’angaren aka fara da “Assalama alaikum.”

Wata ajiyar zuciya ta sauke da sauri ta da sakin murmushin daya sa hawaye fitowa a kurmin idonta ta rintse ido, sak kalar muryar Abhi ce, Abhinta dama yana da yan uwa? Amma dai bari ta tabbatar, muryarshi taji yana sake fad’in “Hello salama alaikum.”

Da sauri ta bud’a ido tace “Wa’alaikum salam.”

Jin muryar mace kuma daga yanda ta amsa salamar yasa yaji harshenta ba bahaushiya bace kamar yanda yaga code d’in lambar data kirashi bai ma san ainahin na ina bane sai yace “Zan iya sanin dawa nake magana?”

Cikin nutsuwa da saisaita numfashinta da rub’abb’ar hausarta tace “Sunana Saratu Shakoor Aghali, ni k’awar Sajida ce gareta na samu lambar.”

Daga inda yake zaune ya mik’e yana kallon bangon makeken ofishinshi, cikin b’arin murya yace “Saratu kika ce? Ke wacece?”

Ita ma tsaye ta mik’e ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta tace “Ni ba kowa bace, dama naga kana kama da Abhina ne sosai, shine nace ta bani lambarku, idan babu damuwa ka min lamunin kiranka mahaifina.”

Cikin girgiza kai yace “Saratu? Saratu Shakoor? Saratu waye mahaifinki?”

Cikin danne kukan dake taho mata tace “Ban san komai ba a game dashi, baya fad’a min komai game da tarihinsa, abinda na sani kawai shine shi d’an garin Agadez ne, sannan yana ce min ki manta da maganar dangina, ba zasu tab’a sonki ba saboda sun guje ni.”

Girgiza kai yayi daga inda yake yace “Zaki iya turo min hotonshi na gani? Saratu sunanki sunan mahaifiyata ne, sunan mahaifiyarmu ne ni da d’an uwana mai sunan Shakoor, dan Allah ki turo min na gani.”

Da sauri tana juyawa daga wajen madubin tace “Ba damuwa uncle, yanzu zan turo maka.”

Kashe kiran tayi ta kalli bangon dake rufe ruf da labule farare masu kyau, juyawa tayi ta kalli inda Salahadeen ke kwance hankali kwance yake baccinshi, da sauri ta yaye labulen hakan ya bayyanar da wani k’aton hoto, ba zata wuce shekara d’aya ba inda take k’irjin Abhi a cikin abun goyo na gaban nan, sai mahaifiyarta a gefe yana rumgume da ita suna bakin ruwa, dukansu cikin annashuwa suke da farin ciki, d’aukar hoton tayi a wayarta ta shiga lambarshi kasancewar yana WhatsApp da ita ta tura mishi.

Yana jin shigowar sak’on jiki na b’ari ya danna ya shiga bud’ewa, k’ura ido yayi har hoton ya bud’e, kad’an ya hana wayar sub’uce mishi yayi saurin tarota yana fad’in “Shine, shine, wallahi d’an uwana ne Shakoor, dama suna raye shi da iyalinsa?”

Da sauri ya dannawa Sarah kira ta WhatsApp d’in na murya, d’auka tayi cike da wani yanayi yace “Wallahi shine, shine Ummi na kina ina yanzu?”

Sai kawai Sarah ta fashe da kuka har yana jin sautin, zaune tayi bakin gadon tana k’ok’arin danne kukanta tana fad’in “Uncle ashe dama akwai ranar da zanyi magana da dangina? Abhi yana fad’in min ba zaku tab’a so na ba, uncle ka fad’a min inda kuke ni zan zo na same ku.”

Cike da rashin jin dad’i yace “Ba haka bane Ummi na, sab’anin da muka samu da mahaifinki ba zamu bari ya shafeki ba, dama mu fad’anmu dashi shine na auren baturiya wacce ba musulma ba alhalin a dangi akwai yara bila adadin da zai iya aura, sai kuma bunk’asar dukiyarshi cikin k’ank’anin lokaci da abun ya zarta tunanin mai hange, amma tunda yayi nisa damu kowa ya shiga damuwa da zulumi, yanzu haka takwararki wacce kika ci sunanta daga gidanta nake, saida ta sake min k’orafin mun kore mata yaro ya gudu ya bar gari hankalinmu ya kwanta.”

Daidaita nutsuwarshi yayi da sauke numfashi da kyau kafin yace “Dan Allah Ummi na ki dawo, ki zo Hajia ta ganki ko zata ji dad’i, sannan ki fad’a masa shima dukanmu muna kewarsa ya dawo gida, ku zo tare da mamanta ki ma kinji?”

Da k’yar ta toshe bakinta tace mishi “To Abhi, zan sake kiranka.” Da sauri ta kashe wayar ta jefa kan gado ta fashe da kuka, ganin Salahadeen ya d’an motsa yasa ta tashi da gudu ta manta da ciwon k’afarta ta shige ban d’aki ta kulle. Kuka tayi sosai na bara bara har shashek’ar kukanta ta tashe shi, ban d’akin ya nufa inda yake jin kukan ya shiga bubbugawa. Yayi tambayar duniya me aka mata amma kanjil bata ce mishi ba bare ta amsa, cike da damuwa da son jin kamar zaiyi kuka shima ya sulale jikin k’ofar ban d’akin yayi zaune ya had’a kai da gwiwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button