NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Tsaki tayi tace “Aikin banza, wannan daular har abun birgace? Waya sani ma kud’in ko na shan jinin mutane ne tunda har ke kanki baki tsira ba saida uban naki ya so yankaki saboda suuuu.”

Marin da Sarah ta kifa mata yasa ta jan suuuu d’in, bata yi tsammanin jin haka ba, bata d’auka tana da wannan k’arfin halin ba duba da acan gida bata da wani katab’us, dafe kunci tayi tana kallon Sarah data nunata da yatsa tace “Nasan doka da kuma ‘yancina, zan hak’ura ki ci zarafina a garinku a gidanku, amma a garina kuma a k’asata abune da ba zai yiwu ba, ki iya bakinki akan mahaifana inba haka ba zaki tsinci kanki a gidan yarin da ko rana bata isa wajen.”

Juyawa tayi zata shiga motar Farha ta yunk’uro a hassale ta d’aga hannu da niyyar dukan Sarah, a tare kamar had’in baki cikin salo da k’warewa masu tsaronta suka zaro bindigoginsu, basuyi wata-wata ba wajen nuna Farha da bakin bindigar a kanta suna zare mata ido da mata gargad’in karta motsa.

Salahadeen na ganin haka ya kalli Farha ya ga ta k’ame wuri d’aya da hannu a sama kawai ya sakar mata murmushi, girgiza kai yayi kawai ya soka wayarshi aljihu ya ciro makullin motar dake hannunshi ya nufi inda motar take, tana kallonshi da ido ya shiga ya tayar ya bar gidan. Sarah data juya ta kalleta ita ma tsayawa tayi cike da alfahari tace “A cikin second d’aya zan iya sawa a rufe min babinki, k’aramar kalma daga bakina kawai suke jira su aiwatar da nufina akanki, amma ba zanyi haka ba saboda bak’uwata ce ke.”

Kallonsu tayi a harshen turanci tace “Ku rabu da ita muje.”

Tana kallo suma motarsu ta marama tashi motar baya, cije leb’en k’asa tayi cikin haushi kamar zata fashe ta juya ta koma ciki.

Tana cikin tafiya hankali kwance ta shiga app d’in ta WhatsApp, kafin ta ankara kiran ya shigo na sabon Abhinta, d’agawa tayi a take ya bayyana gareta tare da wata tsohuwa a gefe wacce ta tabbatar kakarta ce dan ga kamarsu nan sai dai kawai fuskar tsufa, suma tarau ta bayyana garesu inda lokaci d’aya suka gane a mota take, da murmushi akan fuskokinsu cikin son fizgar hausar da k’yar Sarah tace ” Heyy tsohuwa, kai wannan ita ce takwarata ko Abhi?”

Dariya ya saka ya kalli Hajia data had’e fuska tace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:20 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 4锔忊儯7锔忊儯

“Haka zamu fara yi dake tun yanzu?”

Dariya tayi sosai tace “I am sorry k’awata.”

Kallon fuskarta kaka tayi da kyau saita fashe da kuka tana share ido tace “‘Yar nan ina kuka shige? Yaushe zaku zo na ganku? Ina Shakoor yake da mamanki?”

Ajiyar Sarah ta sauke tana k’ok’arin k’ak’aro murmushi tace “Ki daina kuka mana karki saka ni kuka nima bayan nayi kwalliya a fuskata.”

Dariya Hajia tayi tana fad’in “Ja’ira kawai, kenan kinsan ni kakarki ce?”

Dariya tayi tace “Na sani mana, Sajida ta fad’a min kalar rigimarki, shiyasa zan zo miki a shirye.”

Dariya Hajia tayi ita da Abdel tana fad’in “Da wannan gurguwar hausar taki sai mutum yayi da gaske yake ganewa? Ai ba zaki iya ja dani ba.”

Girgiza mata kai tayi tace “Zan iya mana k’awata, ai ina koyon hausar kuma ina ganewa sosai.”

Abdel ne yace “Yanzu dai ku tsaya da rigimar nan, ki fad’a mana yaushe zaki zo?”

Yanda zata fad’a mishi da hausa ne ya mata wuya sai kawai tace “Ku dube ni kowane lokaci Abhi, nima yanzu banga abinda zai sake zaunar dani garin nan ba bayan na sameku.”

Gyara zama yayi yace “To in hakane me zai hana ku taho tare da Saji, tunda ita ma ta kusa dawowa hutu.”

Jim ta d’anyi saboda tunawa da malamin makarantarsu yace zai nemeta kuma har yanzu shiru, tana fatanta dai ba korarta zasuyi ba, kallonshi tayi tace “Karka damu Abhi, zanyi magana da malaman makarantar na samu hutu tare da ita, ni sabuwa ce a makarantar ban jima ba bare na fara samun hutu, idan na samu zanyi magana daku.”

Mayar da idonta tayi akan Hajia tace “K’awata, me zaki tanadar min kafin na zo?”

Hararan wasa ta mata tana fad’in “Shak’iyiya, ba an fad’a min kinyi aure ba, to idan kinzo zan miki gyaran jikin da zai gigita tunaninki da mijin naki, dan nasan ku baku damu da wannan ba ko?”

Zaro ido tayi da mamaki tana dariya cikin jin kunya tace “Waya fad’a muku? Sajida ce ko? Kinga K’awata karki d’auki abinda ta fad’a da mahimmanci, idan na zo zamuyi hira dake sosai.”

Wata harara ta sake mata tace “Iyee! Ni zaki ninkewa ta baibai ko? Ko kin d’auka bansan har da d’an k’umshinki bane a jikinki.”

Dafe kai tayi tana waro ido tace “Oh my God, haka dama Sajida ta min…” Rasa abinda zata ce tai sai Abdel ne yace “Silili ba, ai babu abinda bata fad’a mana ba.”

Girgiza kai tayi tare da d’aga kai ta kalli inda motar ta tsaya, kallonsu tayi tana murmushi tace “Abhi zan shiga mall shopping, zamu sake magana insha Allah.”

D’aga mata hannu Hajia tayi da cewa “Idan kinje gida ki had’ani da mahaifinki kinji.”

Da darita tace “Shikenan.” Murfin k’ofar ta kama tana fad’in “Me zan siyo miki idan na shiga ciki?”

Kallonta tayi tace “Ki siyo min irin kayan nan na jikinki.”

Jinjina kai tayi tana murmushi tace “Karki damu zan siyo miki wanda suka fi nawa girma.”

Dak’uwa ta mata tana fad’in “Kema kina zuwa nan zan saki hangandi sai kin cike duk ramar nan da wannan dogon wuyan, insha Allahu sai kinyi kumari kin kusa kamo ni.”

Dariya ta sake yi kawai sukayi sallama tana mai zura k’afafunta waje sanda mai tsaron ya bud’e mota k’ofar, fita tayi tana mai daurewa sosai akan ciwonta, ba wani sauri take sosai a tafiyarta ba a hankali ta shiga, lift ta hau ta k’arasa saman wajen samun kayan da take buk’ata. Ta jima a wurin tana siyan kayayakin kafin ta fito tare da rakiyar ma’aikatan wurin suna d’auke da jakunkunan kayan, har bayan mota suka saka mata kafin suka tayar da motar suka d’auki hanyar komawa gida.

Biyu daga cikin ma’aikata mata ne suka d’auko kayan suka shigo dasu ciki, ganin Kaka a falo zaune yasa ta kallesu tace “Ku shiga da kayan ciki.”

Kusan kaka ta k’arasa ta zauna tana fad’in “Granny ke kad’ai?”

Saida suka sumbaci juna kafin tace “Har kin dawo?” Cikin sauke numfashi tana cire takalminta tace “Na dawo granny.”

Kallon k’afarta tayi tana duba bandage d’in da aka mata, d’ora k’afar tayi kan cinyarta tana d’an mamatsawa ta kalli Kaka tace “Granny na samu yan uwan Abhi fa, munyi magana dasu d’azu har kakata ma na gani.”

Da farin ciki tace “Da gaske? Amma zaki je ki gansu ko?”

Jinjina kai tayi tana murmushi tace “Zan je granny, amma sai nayi magana da malamin makarantarmu sannan.”

Jinjina kai tayi ita ma tace “Nima na sa a ciro min ticket d’in jirgin da zai tashi da asuba, ko da kin tafi can idan kin dawo ki same ni gida, ina so ki zauna kusa dani saboda kula dake.”

Wani murmushi kawai tayi tana jinjina kai alamar gamsuwa, wayarta ta d’auko ta shiga dannawa kakar tace “Baby akwai probl猫me fa?”

Cikin kulawa ta kalleta tace “Na me fa granny?”

Cikin nutsuwa tace “Bak’uwar can taki d’azu ta fito da kaya tace wai zata tafi, to ni dai ba fahimtarta nake ba, haka dai Linda ta fad’a mana me take nufi, amma nasa ta bata hak’uri ta koma ganin ke ba kya nan kuma shi mijin naku baya nan, kinga bai kamata mu barta ta fita ba.” Girgiza kai tayi kawai tana yatsina fuska ba tace komai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button