NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Salahadeen daya gaji da jiranta shigowa yayi danya duba ko ta manta da abinda ya fad’a ne? Yana shigowa idonshi falon suka fara sauka ya ga ikon Rabb, zaune akan kujera suna dariya sai girgiza kai Sarah keyi tana fad’in bata so bata so, to me kuma ya faru? Waya musu sihiri haka da har suka d’inke a take? Kanshi ne ya d’aure kawai ya juya ya fita, a motar ma zaune yake yana ta son gano me ya faru dasu? Fita yayi yana tunanin ba zai dawo gidan ba gaba d’aya dan idan sun shirya kansu ne to zasu nemi ina d’an gudaliyarsu ya shiga? Idan kuma ba sulhun gaske bane ba zasu damu dashi ba. Wani murmushi ne yaji ya taho mishi dan har ya fara hango kanshi Sarah ta fito cikin birnin k’asar Tha茂lande tare da masu tsaronta suna tayata nemanshi (Ohhh, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak’i?).

A hannun Sarah ta samu lambar Mustafa dake WhatsApp suka kirashi, sai yace baya gida amma yanzu zai koma sai ya basu Maman, zaman jiranshi sukayi naawa d’aya kafin ya had’asu da Mama a hoto mai motsi, cikin farin cikin ganinta da kuma ganinsu tare duk sunyi ruf da ciki akan gadon Sarah suna kallon Mama tace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:20 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 4锔忊儯8锔忊儯

“Yar amanata, ke ce da kanki tare da Farha?”

Dariya sukayi suka kalli juna Farha tayi saurin cewa “Mama ina wuni?”

Zaro ido tayi tace “Wunin lafiya Farha? Ku wajenku yamma ce?”

“Eh Mama, ina su Iffatu?”

Turo baki Sarah tayi tana fad’in “Mamie ni zan fara magana dake fa amma kinga tana neman hana ni.”

Baya Farha taja tana fad’in “Na bari to ku gaisa.” Gyara kwanciya Sarah tayi suka shiga gaisawa da Mama, sun jima suna hira har Sarah tace “Karki damu Mamie ina nan tafe zan sake ganinki.”

Cike da zumud’i Mama tace “Da gaske yar amanata? Yaushe zaki zo? Ko tare zaku taho?”

Jinjina kai tayi tace “Watak’ila mu taho tare dasu watak’ila kuma na rigasu tahowa, saboda ina cikin farin ciki ina son ganin dangin Abhina.”

Da sauri Mama tace “Kin same su ne?” D’aga kai tayi tace “Na same su Mamie, na ga yer uwata da yayan Abhina da kuma mahaifiyar Abhina, suna Agadez ne su da zama.”

Sosai ta mata murna suka ci gaba da hira kafin Farha ta matso suka sake gaisawa da Mama ta tambayi su Iffa Mama tace suna islamiyya, da haka sukayi sallama da cewa sai sun sake magana.

Suna gama wayar Farha ta kalleta tace “Ki kira mana shi muji ina ya shige haka tunda yace yana jira na.”

Tashi tayi daga ruf da cikin tana kallonta ta bata wayar tace “Ki saka lambar saiki kira.”

Karb’a tayi ta shiga rattab’a lambar ta danna mishi kira, abun mamaki turanci aka shiga yi mata, mik’awa Sarah wayar tayi tana saurara ta kalleta tace “Yayi nisa da service, to ina ya shiga haka?”

Tab’e baki tayi da d’aga kafad’a alamar bata sani ba, sharewa tayi ita ma ta sauka daga gadon tana fad’in “Zan fita wajen Granny tana shirye shiryen tafiya ne da asuba.”

Saukowa tayi tana fad’in “Bari muje tare.” Tare suka fita har d’akin da Kaka take.


Ta idar da sallah magriba wayarta ta shiga ruri, mik’ewa tayi ta aje Alqur’anin data karb’a a wurin Farha ta d’auki wayar, uncle Kabeer shine sunan data ambata, take maganganunshi suka dawo mata a kai, duk sai taji jikinta yayi sanyi ta tsani uncle d’in, da k’yar ta d’aga wayar ta d’ora a kunne tana fad’in “Assalama alaikum.”

Bai iya amsa mata ba dan ya sab’ama tsarinsu sai cewa da yayi “Pricess me yake faruwa? Yanzu a gabanki mijinki zai ci mutumcina kuma kina kallo? Amma kinsan da mahaifinki ne ni ba zai min haka ba ko?”

Cike da k’osawa ta zauna bakin gadon tana dafe goshinta tace “Sorry uncle, nima yafi k’arfina, kayi hak’uri.”

A gankali yace “Shikenan naji, yanzu ya za ayi ina son ganinki na tabbatar da kafiyarki?”

Wani wal wal tayi da ido irin shiiit d’in nan kafin tace “Uncle karka damu dani naji sauk’i ai, dan yanzu haka ma ina shirin barin k’asar nan ne.”

Da d’an k’arfi yace “Barin k’asar nan kuma? I zuwa ina to?”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Zanje Agadez ne, na gano dangin Abhi zan je na gansu, watak’ila kuma na koma can kenan.”

“Amma yaushe zaki tafi Sarah.” Ya tambaya cike da kulawa, cile da jin haushi tace “Ba yanzu ba uncle, ina so granny ne ta tafi da asuba saina saka lokaci nima.”

Dan kar ya sake mata wata tambaya tayi saurin cewa “Yawwa uncle zan tafi suna jirana, bye! Za muyi magana.”

Tana fad’a ta kashe wayar ta aje kan gado ta cire hijab d’in ta fita falo, Farha ta samu ita kad’ai a falon kamar a dame take, zaune tayi tana fad’in “Whats-upp baby?”

Kallonta tayi cike da damuwa tace “Har yanzu bana samunshi a waya, gashi har dare ya fara yi bai dawo ba, hankalina ya kasa kwanciya wallahi.”

Gyara zamanta tayi tana fad’in “Haba kema, amma dai kinsan ke ce bak’uwa a garin nan ba shi ba ko? Namiji ne kuma a garin nan yayi karatu, ina tabbatar miki zuwa yanzu yana can tare da abokai wani wurin shak’atawar suna holewarsu.”

Zaro ido Farha tayi tace “Wurin shakatawa? Da ‘yan mata kuma?”

D’aga kafad’a tayi tace “Ban sani ba gaskiya.”

Babu wacce ta sake cewa komai sai Farha data ci gaba da kiran lambarshi amma bata samu, matuk’a a dame take yanda a zahiri ya bayyana maka. Sai dai Sarah ma a k’asan zuciyarta tunanin ina ya shiga takeyi? Ko dai ya tafiyarshi shi kad’ai ne ya bar matarsa nan? To idan kuma yana nan ya canza wurin zamane fa? Jiya ta d’aga mishi murya yau kuma ta mari matarshi, ta yiwu shiyasa ya bar mata gidan, d’an tab’e baki kawai tayi taja k’aramin tsaki a b’oye.

Mai aiki ce ta sanar dasu an gama abinci, sun isa kan dinning d’in kawai Sarah ta ture abincinta tace na Farha take son ci, ya mata dad’i sosai haka ta ci kamar zata cire yatsu, tana idarwa taji wani masifaffen bacci ya lullub’eta, kallon Kaka tayi da Farha tace “Zan je nayi sallah na kwanta bacci nake ji sosai.”

Murmushi Kaka tayi tace “Je ki kwanta baby, ai kinji dad’i da baki had’u da ciki mai laulayi ba.”

Murmushi kawai tayi ta wuce ba tare da taji komai daga Farha ba, tana shiga d’aki da k’yar tayi alwala bacci na rufe mata ido sosai, dole ta gajarta sallah tana idawa ido na son rufewa ta samu da k’yar ta karanci shafi biyu, bata iya hawa kan gadon ba daga nan bacci ya d’auke ko hijab d’in bata cire ba wanda ta siyosu d’azu.


Sun idar da waya da Kabeer ya mik’e tsaye inda yake yana fad’in “Tafiya kuma? Me yake damun yarinyar nan ne? Ina ba zai yiwu ba wallahi! Ba zan bari ta bar k’asar nan ba.”

Safa da marwa ya shiga yana tunanin yanda zai dakatar da ita daga tafiyar, inhar ta sake yin nesa dashi ba lallai ya samu damar ganin duk wani motsinta ba, amma anan tana cikin kulawarshi ne da saka idonshi, ya jima yana tunanin hanyar da zai tsaya da ita, kamar an tsikare shi kuma saiya tsaya waje d’aya, wani murmushi ya saki yana jinjina kai alamar ya samu mafita yace “Na samu mafitar.”

Da sauri ya shiga d’akin baccinshi ya wuce zuwa d’akin da babu mai iya ganinshi, wata k’warya ya shiga yin wasu tsabace tsabacenshi, yana idarwa ya mayar da k’waryar muhallinta ya juya gabanshi yana shek’a wata dariya ta mugunta da k’arfi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button