NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Jujjuyawa ta shiga yi tana k’arewa unguwar kallo, duhu babu haske sosai banda hasken farin wata, nuna mata k’ofar yayi yace “Muje ciki.”

Kallonshi tayi tace “Abhi na.”

Kallon raini ya mata yace “Muje yana ciki.”

Saida ta ga ya wuce sannan ta bishi a baya tana d’an gugurd’ewa da takalminta saboda rashin kyawun hanyar, makulli yasa ya bud’e k’ofar suka shiga, babu soro ko wata bishiya data ma gidan inuwa, filin gida ne sai d’akuna guda hud’u, d’aya ban d’aki ce sai d’aya d’akin k’ananshi maza su biyu, sai d’aya kuma mahaifiyarshi tare da k’annanshi mata, sai d’aya na amaryarshi wacce yanzu take tare da k’annanshi suna tayata kwana.

D’akin na tsakiya ya nufa ya shiga k’wank’wasawa a hankali, daga ciki aka tambaya da “Waye?”

Murya k’asa k’asa yace “Mama ni ne, Salahadeen ne.”

Da sauri aka fara bud’e k’ofar ana fad’in “Salahadeen? Tafiyar daren ce kayi da bana so ko?”

Zubawa k’ofar ido sukayi har matar ta bud’e, riga ce muna-fata a jikinta da kallabinta akai, kauce mishi tayi a hanya tana fad’in “Shigo ciki.”

Sam bata lura da ita ba saida ta ga ya kalli wajen yace “Shigo.”

Saida gabanta ya fad’i ganin Sarah, tambayar farko data wa kanta ita ce wacece? Kamar za tayi kuka tace “Ba zan shiga ba, ni kawai ka d’auke ni daga wurin nan, ban yarda da kai ba mr.”

Matsowa yayi kusanta ya kamo hannunta da k’arfi suka shiga ciki, ikon Allah ta tsaya kallo sanda ya saki hannunta yana hararenta, cikin tsiwa da d’aga murya tace “Mr. i dont need this place, i hate u and i hate this place, take me home i wont see my Dad.”

Tsawa ya mata ta hanyar fad’in “Shet up.”

Kallon daya mata yasa ta yin shiru tana kallonshi, kallon mahaifiyarshi yayi yace “Mama na same ku lafiya?”

Bata bari ta bashi amsa ba tace “Hey mr., kayi magana yanda zan gane, karka yarda kayi ciniki na ina tsaye anan, da ganin matar nan mai siyar da mutane ce tana kaisu Africa tana bautar dasu.”

Kallonta yayi kamar ya kifeta da mari, to anan d’in ina ne take? K’wafa yayi ya sake kallon mama zaiyi magana, sai gani sukayi ta cire botiran rigarta ta sama ta jefa kan lafiyayyar shinfid’ar katifar dake k’asa tana fad’in “Bana son wurin nan, ka d’auke ni anan kafin na mutu dan zafi.”

Cikin d’aga murya ya kalleta yace “Ke ki min shiru na gaisa da uwata mana.”

Turo baki tayi gaba ta kalleshi ta kalli mama data kasa d’auke idonta kan yarinyar, bata ga wata kama da zata yarda mahaifiyarsa bace, fatarsu ma ba d’aya ba ita tana da duhu shi kuma gashi fari dashi, juya baki tayi tace “Wannan ba mahaifiyarka bace, mai siyar da yaran mutane ce, ka zo ne ka siyar dani ita kuma ta tsallakar dani africa.”

Har zai mata tsawa sai kuma ya ga ba wannan take buk’ata ba, yarinyar data girma cikin kulawa da rarrashi, watak’ila ma bata san me tsawar ke nufi ba, saida yayi kalar tausayi ya nuna mata shinfid’a yace “Je can ki kwanta, safiya nayi zaki bud’a ido ki ga Abhinki, wannan mahaifiyata ce ba mai siyar da mutane ba.”

Ganin ta kafeshi da ido bata da niyyar tafiya yasa yace “Please, in dai kina son ganin Abhinki.”

Da alamar tambaya ta kalleshi tace “Are u sure.”

Da ido kawai ya mata alamar eh, wucewa tayi ta tsaya kan shinfid’ar ta juyo ta kalleshi tace “Mr. anan ne zan kwanta?”

Juya mata baya yayi ya fuszar da iskan k’osawa, bai kalleta ba yace “Ba fa anan zaki zauna ba, zuwa safiya zaki bar nan.”

Saida ya ga ta kwanta kan katifar tana ta latsa matela tana ta jujjuyawa kamar ta kwanta kan tabarma, kallon Mama yayi yace “Muje ciki mama.”

Shigewa tayi uwar d’akin mamaki kamar zai kasheta, tsaye ya same ta rik’e da baki tana tunanin wannan ikon Allah, tana ganinshi ta had’e rai tayi kicinkicin a tsawace tace “Wacece wannan Salah? Wace fitsararriyar yarinya ce ka kawo min? Daga k’asar wajen ka taho min da ita nan?”

D’an sunkuyawa yayi yace “Mama dan Allah zauna sai muyi magana.”

Jinjina kai tayi ta koma ta zauna kan gadon k’arfenta mai runfa ruf ya ji shinfid’a lafiyayya, k’asa ya zauna ya gyara zama ya shirya zancen da hankalinta zai d’auka wanda kuma ba zatayi fushi ba ya fad’a mata, wani abun gaskiya ne wani kam ya kasa fad’arsa a gaskiya saiwa ya d’an lullub’eta ya fad’a. Kuka Amina ta saka tana share hawaye da bakin kallabinta mai sulb’i tana fad’in “Wannan duniya, wannan duniya ina zaki damu? Uba? ‘Yarsa ta cikinsa yake so ya kashe saboda abin duniya, kai amma wannan akwai rik’akk’en d’an ta’adda.”

Kallonshi tayi tace “To amma dai musulma ce ko?”

Kallonta yayi shima yace “Eh to sama sama dai.”

Da mamaki tace “Sama sama kamar ya?”

“Eh mana Mama, tunda mahaifiyarta ba musulma bace mahaifinta ne musulmi, ni dai a zamana dasu banga tana wani abu daya nuna tana rik’e da addinin mahaifinta ba gaskiya.”

Numfasawa tayi tace “To yanzu ya zakayi da ita anan?”

Cikin ladabi yace “Mama kawai zata d’an kwana anan ne zuwa safe mun san abinyi.”

Jinjina kai tayi tace “Toh shikenan, yanzu kai ina zaka kwanta? Su Iffatu suna can tare da Farah d’in.”

Saida ya juya yace “Ba komai mama, tunda an kusa sallah asuba ma zanyi alwala na tashi masallaci kawai.”

“To shikenan.” Ta fad’a tana kallo har ya fice.

Shakoor hankalinshi in yayi dubu ya tashi, ya kira wayarshi har ya gaji da jin cewa kashe take, ya kira wayar Sarah tana k’ara ba’a d’aga ba, office d’in ya kira secr茅taire d’inta ta tabbatar masa data fita caf茅t茅ria amma bata dawo ba, nan ya taho campagnin hankali ba kwance ba da tunanin abinda ke shirin faruwa.

Abun kamar da wasa sai kuwa lokaci yaja babu labarin Sarah, a caf茅t茅ria an tabbatar ta zo kuma ta tafi, amma komawarta ne babu wanda ya gani, ganin abun zaifi k’arfin d’aukar zuciyarshi sai kawai ya shigar da police a al’amarin, duk yanda ake taka tsantsan da b’oyewa sai gashi an rasa daga ina labarin ya fita har aka fara haska hoton Sarah a matsayin yar billionnaire an nemeta an rasa.

Bai gushe ba yana gwada kiran wayar Salahadeen har dare ya tsala, bai tab’a tunanin wai zai yaudare shi ba, yafi tunanin sun samu matsala ne kan hanyarsu ta zuwa wajen hutawarshi dake bakin ruwa, a sab’ule cikin damuwa ya halarci k’ungiya.

Shugaban ne yace “Shakoor yau ne alk’awarinmu da kai? Ina yarinyar take?”

Shiru yayi kamar baiji shi ba sai rarraba ido daya fara, jin shirun yayi yawa yasa shi d’aga kai ya kalli shugaban, cikin rawar murya yace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 03:58 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa ta Orange money(ba chap chap ba yan uwa, orange money dan karka tura ta chap chap amma zaku iya tura kati) akan wannan lambar 91-71-28-22 ko kuma wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button